Page 14&15✍🏻

En başından başla
                                    

             "Lafiya ƙalau Ayman."

           "Yaya ina tsarabata?"
   
          Miƙa masa laida ya yi yace, "Gata."
   
           "Na gode sosai Yayan mu."
   
       Shigo suka yi shima ya biyo bayansu, yana cewa, "Umma kinga tsarabata da Yaya ya bani min."
   
    "Inyye! Na tayaka murna."
   
    "Fatan dai ka yi masa godiya?"
   
    "Eh! Na yi masa."
   
    "Anya! Ka yi masa kuwa"
   
    "Allah na yi masa, Yaya ai dai na yi maka haka ko?"
   
       "Eh! Ka yi min."
   
    "Kin ji ko Umma? Na yi masa."
   
      "Na yarda yanzu."
   
    Dariya suka yiwa Ayman ganin yadda ya canja lokaci ɗaya, zama suka yi take tambayarsa ya Hajiya yake, ya shaida mata tana lafiya ƙalau da sakon godiya da  gaisuwa da ta ba da, ta ji daɗi sosai har sai da farin cikin ya bayyana.
   
    Kamar daga sama suka ji Aymana na cewa, "Umma ina Yaya zai je?"
   
    "Tambayesa kiji Aymana tun da gashi nan a kusa dake."
   
    Juyawa ta yi ta kalle sa tace, "Yaya ina zaka ka bar mu?"
   
     "Aymanata karatu zan tafi yi."
   
      "A ina Yaya?"
   
       "Wajen."
  
      "Waje kamar ya Yaya?"

     "Ƙasar wajen nake nufi."
   
    "Amma Yaya me yasa ba zaka zauna ka yi nan ba?"
   
          "Aymanata can sai yafi yi min sauƙi, inna zauna a nan zan ɗauki dogon lokacin kafin na cika burina."

       "Yaya menene burinka?"

        "Na zama litita."

    Zato ido tayi tace, "Amma dai ba zaka ringa yi mana allura ba ko?"
   
     "Hhhh!" Dariya ya yi sosai dan tambayarta ta bashi dariya yace, "Eh! Ba zan ringa yi muku ba."
   
    "To..! Yaushe zaka tafi?"
   
    "Juma'a ta sama insha Allah."
   
    "To..! Yaya wace ƙasa zaka tafi?"
   
     "Indiya Insha Allah."
   
      "Kuma Yaya...."
   
    Dakarar da ita yayi yace, "Dan Allah Aymana kiyi haƙuri da wannan tambayo yin naki, bari Daddy ya dawo sai ki tambayesa shi yasa komai ni ban sani ba."
   
    Dariya sosai Umma ke musu, sanin halin Aymana da tayi da ƴar banzar tambayar da bata da ƙarshe, yasa ta dakatar da ita tun da farko.

      Shima dariyar yayi, ita kuwa gwanar bata so haka ba kawai tayi shirune dan ba yadda zata yi, kamota yayi yace, "Ƴar ƙanwata amman dai ƴar jarida zaki zama ko?"

      Dariya tayi sobada an taɓo mata inda yake mata ƙaiƙayi tace, "Eh! Yaya ina san na zama ƴar jarina ina girma."

        "To..! Shikenan sai ki maida hankali a karatunki, indai kina son zama cikakkiyar ƴar jarida."

       "Insha Allah! Yaya zan dage don nima na cika burina, kamar yadda kaima zaka cika naka a yanzu."

        "Yauwa! Aymanata Allah ya taimaka."

       Su duka suka amsa da, "Ameen Ya Allah."

      "Kai Ayman me kake zan zama?"

      "Yaya nima ban sani ba yanzu sai na ƙara girma zan zaɓa."

     "To..! Ayman ɗin na Allah ya raya mana ku."

    Suka kuma amsawa da, "Ameen Ya Allah."
   
        Hira suka shiga yi cikin nishaɗi da annashuwa, sai da suka jima suna hira sannan aka kira sallar magriba kowa ya tashi yaje ya gabatar da sallah. Abdallah yayiwa Umma sallama dan daga masallaci zai wuce wani wajen, tayi masa fatan alkhairi  ya fice yana jin daɗi a ransa.
   
   
   
   
              _*<<<<<~•~>>>>>*_
    
   
         Safa da marwa kawai yake yi, duk hankalinsa yabi ya tashi gumine keta tsatsafo masa, idan ya gaji sai ya haɗa kansa da bango yayi shiru, lokaci ɗaya ya fita a hayyacinsa.
   
       Kallansa kawai Safna take yi, gaba ɗaya kanta ya ɗaure, ta kasa gane ainahin abinda ke faruwa, tambayoyine barkatai dake yawo a cikin kanta game da Yassar da yarinyar da suka taikamawa, ko tantama babu akwai wata alaƙa a tsakanin, dan duk kan alamu sun bayyar da haka, gani ba damar da zata tambayesa ko ya san yarinyar, yasa ta kama bakinta tayi shiru dan ta san halin kayanta.
   
       Dr. Ne ya fito ya doso ina suke, tun kan ya buɗe baki yace wani abu Yassar yace, "Dr ya take? Fatan dai tana lafiya ƙalau babu abinda ya sameta?"
   
        "Ka kwantar da hankalin zo muje office sai muyi maganar a can."
   
        Bin bayansa suka yi har zuwa office ɗin Dr. Ɗin zama ya yi suma ya yi musu nuni da su zauna, sanna ya fara magana, "Malam wannan yarinyar wacece a wajenka?"
   
        Tafe kansa yayi ya kalli Safna ta ke gefensa, itama kallansa take yi tana jiran jin mai zai ce. Juyowa yayi yace, "Dr. Ban san ta ba." Nan ya kwashe labarin yadda aka yi suka haɗu da yarinyar har suka kawota asibitin ya basa.
   
        "Hmm!" Dogon nufashi Dr. Ya ja sannan yace, "A gaskiya yarinyar nan tana cikin halin ha'ulayi, tana buƙatar taimakon gaggawa, a binciken da mu ka yi mata mun gano an yi mata Fyaɗe, kuma an ji mata ciwo sosai sakamako ƙanƙarar da ta yi da yawa, akwai buƙatar ayi mata aiki, sannan kuma a akwai tsofafin gocewar kashi a gwiwar hannuwanta da targade a yatsun ƙafarta, ga kuma farfashewar da gwiwoyin ƙafafuwanta. Muna buƙatar wani nata ya tsaya mata, sannan sai mu fara mata aiki da dace da ita."
   
        "Dr. Zan tsaya mata, Wallahi ko rayuwata kuka ce na ba da ku dasa mata zan baku a dasa mata."
   
        Girgiza kai Dr. Yayi yace, "Baka tsoron wani abu ya biyo baya a kan haka?"
   
        "Bana tsoro Dr. Dan Allah ku tashi kije ku yi mata duk abinda ya dace a yi mata, komai tsadar sa zan biya."
   
        "To..! Amma yanzu dai kafin mu fara mata wani abu, muna buƙatar sa hannuka dan ka da wani abu ya ɓullo daga baya mu shiga ciki."
   
        "Ba damu bani na sa."
   
      Wata takarda ya miƙo mata da biro yace, "A nan zaka sa hannun."
   
       Karba yayi zai sa hannu Safna da ta gama ruɗewa ta riƙe hannusa tace, "Yanzu ka yarda ka shiga matsalar da baka san menene silar ta ba? Baka tsoron wani abu ya biyo baya ka shiga matsala? Dan Allah ko ba zaka yi tunani akan kowa ba ka yi tunani a kaina da ɗan dake cikina, yanzu idan wani abu ya sameka ya zamu yi?"
   
       "Kiyi haƙuri Safna ba zan iya ƙyale wannan yariyar ba cikin halin da take ba, Wallahi a yadda nake ji a game da ita zan iya rasa komai akanta, dan Allah ki fahimce ni, indai ban taimakawa wannan yarinyar ba, to ba zan taɓa samun nutsuwa ba a cikin raina ba."
   
        Ba yadda ta iya ta saki hannusa ba ta ce masa komai ba, ta share ƙwallar da yake zubowa kawai, dan kalamansa sun girgiza mata zuciya, a cikin ranta take tambayar kanta, _Shin wai wacece wannan yarinyar da har Yassar yake jin zai iya rasa komai akan ta?_ Shi kuma ganin ta sakar masa hannunsa, yasa ya saka hannun da Dr. Ke buƙata ya miƙa masa takarda yace, "Dr. Sai me kuke buƙatar?"
   
       "Ka cike file kawai."
   
        "To..! Miƙo min."
   
       Miƙa masa yayi ya cike ya miƙa masa, dubawa yayi ya ga ya cike komai ban da abu ɗaya yace, "Yassar baka saka sunan yarinyar ba?"
   
        "Ban san sunanta ba."
   
        "To..! Taya zamu tsaya mu jajirce wajen dubata baka ba mu sunanta?"
   
       Ji ya yi kamar ya ɗauke Dr. Da mari a ransa yace, _Kamar ba yanzu nan na gaya masa cewa ban ba taimaka mata kawai na yi, ta ya zai san sunanta bacin ban san ko wacece ita ba._
   
       Karɓar file ɗin ya yi bai ce masa komai ba ya saka suna yace, "Sai ka tashi ka je ku dubata na cike duk wani abinda kuka buƙata, amma kuma Wallahi kuka bari wani abu ya sameta, sai na yi ƙara ku nasa an rufe muku asibitin da kuke takama dashi, kuke yin yadda kuke so."
   
        A je file ɗin Dr. Yayi ya fita cikin gaggawa jin furucin da Yassar yayi masa, dan ya lura da alama babban mutum ne zai iya aikata komai.
   
       "Honey wane suna ka saka mata bacin baka santa ba?"
   
        "Karki damu, sunan mafi soyuwa a wajena na saka mata."
   
        Kin mamaki tace, "Wane suna?"
   
       "Yasmeen Abubukar Ishaq."
   
       A razane ta kallesa ta tace, "Wacece Yasmeen?"
   
       Cikin murya mai kama da ta kuka yace, "Yasmeen itace wacce nafi so a duniyar nan, Yasmeen ƙanwata ce ta jini uwa ɗaya uba ɗaya, Yasmeen rayuwatace, Yasmeen farin cikina ce, Wallahi Safna Yasmeen itace komai nawa." Ya ƙarashe maganar yana goge hawaye.
   
       "Dama kana da ƙanwa baka taɓa gaya min ba?"
   
       "Taya zan faɗa miki bacin nima ban san a inda zan gan su ba ita da Ummana, sun bace min a cikin duniyata..." Ya ƙarashe maganar yana kuka.
   
        "Amma ya yakamata ka gaya min nifa matarka ce."
   
       "Hmm! Ke matatace amma ko da sau ɗaya kin taɓa tambayata, me yasa ba na dariya? Ba na nishaɗi? Ba na walwala da annashuwa a cikin rayuwata? Baki taɓa ba to taya ni zan gaya miki abinda ko a cikin mafarki ba na fatan ya zo min a matsayin tunani, abin baƙin ciki ma ko kammanin Ummata bana iya tunawa ballantana ma na iya tuna a wane wajen suke, soyayyar suce kawai ba ta gushe a ciki cikin zuciyata ba, ta ya kike tunani zan iya fesar da kalaman da suka kasace kamar gubane a gare ni?"
   
   
       Yana gama faɗin haka ya fice a office ɗin ya barta a nan tana kuka, wanda shi a ganinsa na jin daɗi take yi, dama zai samu damar yin kukan da take yi da ya more.....
   
   
   
        _Ku yi haƙuri da wannan ba na  jin daɗi ne daurewa kawai na yi, na yi muku shi ganin kuna nemansa.👏🏻_
   

   
_*See me next page✍🏻*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#JannatMN*_   

 
   
  

*©JANNAT M. NASIR•*

YASMEEN.Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin