Zuwa can anjima tafara tashi daga jikin khalifa yayinda ta kwace hannunta daga hannun sameer idonta arufe
Salati tafara tana kiran sunan ALLAH kanta ne taji yana jujjuya mata da sauri tariqe kan hannun bibbiyu
Memorynta ne yafara dawowa ahnkl tafara tuno rayuwarta na baya da kashe mata iyaye da baba dauda yayi da gudunsu ajeji ita da yaya khalifa da rayuwar da sukayi ajejin har izuwa rabuwarsu

DA rayuwarta tare dasu sameer na mantawa da komai datayi har izuwa yau dataji sunan khalifa da 4eyes's din da sukayi

Da sauri ta bude ido tana waige waige tagansa kusa da ita  kuka mai tsuma zuciya ta saki gamida daga hannayenta biyu wanda suke rawa kamar mazari tana shafan fuskarsa. Domin ta tabbatar shidin ne ko kuma gizo ne

Shima hawaye yakeyi

Cikin muryan kuka tana shafa fuskarsa tace ya..yay...yaya...kha...khali.....khalif....khalifa...

Daga mata kai yayi alamun eh my safreena nine ya riqo hannunta

DA sauri ta rungume sa tana kuka tana mgn dan Allah yaya khalifa karka sake tafiya kabarni zuciyata bazata ɗauka ba

Hannu  biyu yasa shima ya rungumeta yana hawayen farin cikin sake ganin safreena arayuwarsa
Haqiqa adduar bawa bata fadi ƙasa banza saidai jinkiri gashi Allah ya amsa du'a'insa yasake hadasa da safreena

Duk gabaki daya sun Zama abin kallo

Jama'ar dake wajan kansu ya ɗaure sun kasa fahimtar komai
Amma banda mutum uku
Ahmad
Nabeel
Saeed

Mami ce tace waini balaraba meke faruwa ne kam kun samu aduhu fa kuyi mana bayani mana yanda zamu fahimta kufitar damu a ruɗani

Nabeel ya bude baki zai magana bai ankara ba sameer ya fizgi safreena daga jikin khalifa ya rufesa da duka kamar Allah ya aikosa

Kokarin shiga tsakani akayi amma ina sameer idonsa ya rufe da kishi. ganin tabbas fa zai iya rasa najma idan baiyi da gske ba Duka kawai yake kaiwa ta ko ina wa khalifa

Safreena tashiga tsakaninsu tana hana sameer wanda idonsa ke rufe bisa tsautsayi ya kai mata duka tasaki ƙara zata fadi ihsan da madina suka tarota

Ahmad nabeel saeed kokarin riqe sameer sukeyi amma yana zillewa

Sameer baiyi auni ba yaji sauƙan maruka hudu a fuskarsa da sauri yadafe kuncinsa sbd marin ya shigesa nan da nan ya samu natsuwarsa sakamakon tozali da idon mahaifinsa da yayi  ranshi abace

Ganin fadan nasu bana ƙare bane  yasa mami ta kira dad tace mishi kazo gidan biki ya zama gidan fada ga sameer na dambe shine ran dad yabaci suka taho dukkansu shida dadyn nabeel da dadyn saeed

Dad yana huci cikin muryan tsawa yace sameer kalan tarbiyyan dana baka kenn ? Irin ilmin dana baka kenn? Ina hnklnka yake ? Ina natsuwar taka take ? Wannan shine abinda zaka sakamin dashi kenn?

Dadyn saeed ne ya dafasa yace alh ya isa haka yanxu dai ba asi yakamata muji dalilin wannan fadan

Caraf madina tace dadyna wlh duk ya khalifa ne yajawo domin da baizo ba da yanzu muna can muna gudanar da shagalinmu cikin kwanciyar hankali

Kwace yakeso yayiwa yaya sameer najma wai yake kira da safreena

Nabeel yace madina ki rufawa mutane baki bakisan komai ba

Cikin tsiwa tace au yaya nabeel kaima bayansa kake bi kenn lallai kam ansamu waje sosae
To kai din waye khalifa ?

Tsawa nabeel yamata yace banace ki rufe bakinki ba

Lallai khalifa kasamu waje dama kam ance duk wanda yasamu waje saiyayi shanyarsa kuma wlh.....

Hannu safreena ta dagawa madina gamida cewa
Ya isheki haka madina
Shin kinsan waye YAYA KHALIFA kinsan wacece ni

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now