Lumshe ido khalifa yayi gamida cewa SAFREENA !SAFREENA!SAFREENA !
Allah ya nuna min ke nan kusa  domin dole saida ke zan iya ɗaukar miki fansan abinda dauda ya miki
Nasan bazaki mutu ba batare da kinga karshen dauda ba bazaki mutu ba my safreena inaji ajikina kina raye sannan jikina yana bani kema kinfita awannan wahalalliyar JEJIN

Allah yasa kina hannu nagari safreena jiyayi hawaye yana shirin wanke masa fuska yayi saurin mayarwa shi kam kwata kwata ya manta ma a ina yake balle yayi tunanin dasuwa yake tare bai ankara ba yaji karan ta fi rap rap da sauri ya bude ido yaga fa ashe ba shi kadai bane rufe baki yayi a zuciyarsa yace badai sunji abunda nace bane muryan nabeel yaji yana cewa gsky zan so nasan wannan luv story din dan wlh daga ji zai bata onga

Ahmad zaiyi magana wayarsa ta dauki ringing ya dauka yace mufa gamu a kofar hotel din mun iso
OK kawai yace kafin ya ajiye wayar

Khalifa yace au wai dama mun iso ne saeed yasa dry yace ah lallai kam kayi nisa tun yaushe muka iso amarya yanzu muke jira dan mun rigasu isowa kasan shirin mata ashafa wannan amulka wannan agoge wancan dry suka saka dukkansu
basu wani jima ba amarya ta iso da kawayenta tasha kyau

Fitowa su khalifa sukayi da ango suka rakasa har wajan kofar motan amarya kawayen amarya sai wani kallon abokan angon sukeyi barin ma khalifa kamar zasu haɗiyesa

Ango ya kama hannun amaryarsa
A yayinda akayi layi domin rakasu

Anshiga an zauna anyi shagali ansha rawa anyi addua tare da fatan alkhairi dan kuwa basu tashi awajan ba sai sha biyu saura ahakan ma dan ango yace agajiye yake sannan gashi gobe zasuyi asubanci
aje daura din ma akwai wata dinner din dan haka suka tattara badin sunso ba kawayen amarya sai hari suke kawowa khalifa amma ko kallon inda suke baiyi ba hakan nan kuma wasu suka dinga cewa yana da girman kai dan ya gansa yana da kyau

Ko da suka koma gida sun gaji dan sai sha biyu da rabi suka isa gidan
Wanka sukayi suka zauna a parlor suna dan taba hira sama sama saeed yace nifa wlh yunwa nakeji

Ido khalifa ya ware waje yace ai kuwa gidan nan babu kayan abinci ko ƙyalli dan tunda aka gama gininta baifi sati acikinta ba nafita sannan rabona da gidan nan wlh saeed bazai ce maka gashi ba

Yace to kenn yanzu ko tea bazan samu ba
Wlh babu saeed
Nabeel yace ai da kayi mana magana mun biya mun saya kafin mu dawo inba haka ba zamu zauna da yunwa ne
Gwanda shi wannan ango ne bazaiji yunwa ba tunda aurensa akeyi mu kuma fa ?

Khalifa yace to ko zamu fita nema ne !
Nabeel yace Mee Nee Afita neman Mee karfe 1 yanzu wlh babu inda zanje azamanin yanzun nan tab inaa badani ba wai gaɗa a maƙabarta samm dry gabaki dayansu suka saka khalifa yace haba jarumina wlh bai kamata kadinga bada maza ba
Nabeel ya galla musu harara yace au haba
To wlh kuma ina baku shawara karku fita mu hakura da safe ido naganin ido muje

To shikenn nabeel mun hakura

Shuru wajen ya ɗauka nadan lkc kafin saeed yace khalifa ya kamata muyiwa juna introducing sbd kaine kawai baka sanmu ba
Muna kuma haka

Nidae sunana shine
SA'EED BASHIR AWWAL kuma ni haifaffen garin zaria ne mahaifina dan kasuwa ne nima kuma  ina business ta hanyar arkallan motoci
Ata ƙaice kenn sannan biyu ne kacal nida kanwata ihsan

Murmushi khalifa yayi gamida jinjina
Kai

Ni kuma sunana NABEEL ABDULSALAM GAMBO
nima dai dan zarian ne domin kuwa da mahaifin saeed danawa abokaine kuma sana'arsu daya wato kasuwanci ni kadaine awajan iyayena ni kuma arkallan gidaje shine business dina

Nan ma khalifa murmushi yayi batare da yayi magana ba

Ni SUNANA AHMAD GARBA ATULE MAGAJI ni dan daura ne kuma nan iyayena suke mukam munada yawa dan matan babana biyu ne kuma abotanmu a university muka hadu
a) a.b.u zaria daga nan shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninmu

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now