Sauya fuska yayi yace dr wlh bansanta va kawai tsintarta nayi ahanya acikin wnn halin
DA mmki dr bakura yake kallonsa yace baka santa bafa kace ? Ko sunanta ma baka sani ba kenn ?

Eh Dr bansanta ba dan allah dr kamin wata alfarma ga card dina ga kuma kudi ayi mata duk abinda yakamata zanje gida wayata ta mutu kuma nasan zasu nemeni hnklnsu zai tashi zanje nataho da kanwata
Ga shi yanxu har 11:30

Murmushi dr bakura  yayi domin ya fahimci gskyr abinda yake fada masa yace to ba damuwa card din da kudin yakarba
Gdy yamasa yatashi ta sauri yafita gashi NABEEL ya dauke masa chaja amota  balle yasa chaji mtssw

Handlam quarters

Awata katafaren gate madaidaici yayi horn gateman ya bude masa yashiga da sauri ko tsaya parking baiyiba yafice amotar
Kai tsaye parlon yashiga ya hau kwala kiran sunan

MADEENA!MADEENA!MADEENA!

da sauri wata yar budurwar yarinya da baxata wuce kimanin 19yeas ba ta fito idanunta da alama kuka tayi rungumesa tayi takara sakin kuka
Sannan tace haba YAYA SAMEER  meya sameka nida mami hnklnmu yatashi munata kiran wayarka switch up duka biyu

Dagota yayi yace oh kash yadafa kansa kuyi hakuri ku
gafarceni wlh matsala aka samu kanwata ina hanyar dawowa na tsinci wata yarinya.....nan yabata lbrn abinda yafaru
Cike da al'ajabi madina tace innalillahi wato dai yaya idan mutum bai mutu ba yanada sauran kallo

Yace kedai bari wlh karkiga jejin datafito  saikin tsorata
Kuma phones dina duk sun mutu ba chaji
Chazar motata kuma nabeel ne yadauka sbd rashin M irin tasa
Murmushi ta hauyi jin yakira sunan nabeel ta juya zata shiga daki saiga kiran mami wanda duk hnklnta baya jikinta

Dauka madina tayi tace mami ga yayan yadawo miqa masa wayar tayi tashiga domin ta shirya su koma hospital din tunda bawani nisa ne dasu sosai ba

Hakuri yabawa mami tareda bata lbrn abinda yafaru nan itama ta tofa albarkacin bakinta

Sannan tace ai angama bikin gobe ma zandawo
To allah dawo mana dake lpy maminmu ta amsa da ameen sukayi sallama

Sameer ruwa kawai yawatsa yasaka jallabiya yafito yasamu madina tana jiranshi da basket din abinci domin yace bazai iya tsayawa yaci ba saiya je hospital din

Kafin su isa dare ya tsala domin kuwa sai karfe 1 suka isa har lkcn doctors suna kan safreena

Basu samu daman samun numfashinta ba kuwa sai gefen asuba
Duk suka fito agajiye ba yadda suke sbd sun sha matukar wahala akan safreena sannu kawai ake jera musu
Gamida yimusu fifita duk da ac dayake tashi awajan

Suma su sameer da madeena basu rintsa ba yanda sukaga rana haka sukaga dare

Saida misalin karfe 11 tukunna aka farayiwa safreena treatment
Su sameer sunje gida dan dr bakura yace akawo mata riga marar nauyi

Sameer kafin suje gida wata yar madaidaiciyar shop mall ya tsaya ya saiwa safreena dogayen riguna kala shidda domin kayan madina bazai mata ba dan madina batada auki ko kadan

Haka dai sameer da madina suka dinga sintirin asibityn har mami ta dawo aka daura da ita
Kulawa sosae safreena tana samun shi masha allah

------------------
Bayan wata uku

Abubuwa dayawa sun faru awannan lkcn

Wanda sai awannan lkcn khalifa yasamu daman farfadowa daga azabebbiyar ciwon dayasha idan ka kallesa saika tsorata sbd wata uwar raman da yayi

KO da khalifa ya farka sunan safreena kawai yake ambata  yana kokarin fita da kyar zakin dawa ya lallabashi ya zaunar dashi aka kawo masa abinci yaci yasa aka kaimasa ruwan wanka yayi wanka tukunna zakin dawa ke tmbyarsa wanene shi bai boye masa komai ba yabasa lbrn
al'ajabi zakin dawa yashigayi shida matarsa yana jinjina kai

Tab lallai wannan dauda anya akwai digon imani atare dashi kuwa gsky allah yana sonku kuma insha allah dauda bazaiyi karshe mai kyau ba

To yanzu ita safreena ina za aganta cikin muryan kuka khalifa yafara roqon zakin dawa dasu koma jejin yadubo safreena

Ido waje zakin dawa ke kallon khalifa yace halifa kasan me kake fada kuwa ?
Kodana tsintoka kafin muzo nan mun debi kwanaki13 kafin kuma ka farfado saida ka kwashi wata uku yanzu watan ka uku kafin ka farka cikeda tsoro da mamaki yake kallon zakin dawa kafin yasa kuka kamar karamin yaro

Zakin dawa yace ai kawai tunda kai ka rayu kana iya zuwa ka dauki fansa akan wannan azzalumin
Amma ita wannan yarinya saidai mubita da addua allah ya jiqanta da rahma

Cikin kakkausar murya khalifa yace aaa aa baba safreena bata mutu ba inaji ajikina safreena tana raye baba kamin alfarma 1 tak

Zakin daya yace fadi naji idan baifi karfina ba

Baba sonake nafita ajejin nan inaso nashiga gari domin bazan taba yafewa dauda ba safreena kuma zan koma na cigaba da mata  addua allah yasa da rabon fuskokinmu su sake haduwa
Wasu hawaye masu zafin gske suka wanke masa fuska

Zakin dawa yace ba damuwa amma kabari jikin ka yakarayin kyau kafin katafi
Khalifa bazai iya musu dashi ba dan haka yace to yadinga kwararo masa addua da ftn samun lada mai yawa awajan ubangiji na taimakonsa da yayi dan yace babu abinda zai iya biyansa saidai allah ya biyasa tunda baya zaman gida amma sbd lpyrsa gashi bai shiga jeji ba

Safreena kuwa watan ta biyu a asibity ta farka amma saidai kash kasa gane mutane tayi jitake kamar yaune aka haifeta su mami da madina sunyi tmbyr duniya ta fadi sunanta amma tace bata sani ba dan haka sameer yasa mata sunan (NAJMA) dashi aka bude mata file

Koda sameer yayiwa dr mgn dr bakura yace a gsky sakamakon buguwan da kanta yayi jini yashiga kwakwalwarta zata iya tunowa da abinda yasameta amma fa saidai atuna mata wajajen da ta taba rayuwa ko kuma ta hadu da wani wanda tasani kuma gsky tana bukatar kulawa sosae dan kar adingayin abinda zai daga mata hnkl
Gdy sameer yayiwa dr bakura sbd ba karamin kulawa yabawa safreena ba
Wanda suke kira da najma yanzu

Mami ce da kanta tayiwa safreena wanka ta gyara mata gashin kanta ta wanke mata shi tass ta shiryata ta shafa mata body lotion nanda nan safreena ta dawo gal da ita amma har yanzu kafafunta a kumbure suke tana dingisawa mami tashafa mata turare kala2 sai wani kamshi safreena take fitarwa mami ta zauna ta baje mata gashin kanta wanda har gadon bayanta tana busar mata dashi da handdryer tanayi tana shafa mata man gashi mai kamshin gske da laushi

Sameer ne da madina sukayi sallama suka shigo dakin cak ya tsaya yana kallon safreena ji yayi duk jijiyoyin jikinsa yadaina aiki ya kura mata ido ko kiftawa ba yayi
Wani bakon yanayi ya ziyarci zuciyarsa

To fa

More comments more typing

Comments

And

Share

By Mmn ahlan✍🏻

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now