Page 13-14

632 21 15
                                    

*🎍🎪🎍(WANI SALO)🎍🎪🎍*

~-------------------------------------~

*Written-by✍🏻*
              *Sa'adat alkali D/tsafe*

      *JINJINATA AGARE KU WRITERS.. KAMAR HAKA*

*Fadeela lamido- _tsuntsun dayaja ruwa_
*zeenaseer- _rayuwar mu ayau_
*Faty afreen- _mijin yarinya_
*sadnaf- _daga taimako_
*®zuwairat(ummu Maryam)- _kawarta ce sanadi_
*zee London- _Tun ran gini_
*mummyn nawwal- _ummu Abiha_
*khaleesat haydar- _Batul_
*safiya Huguma- _Abadan_
*Aysha ali garkuwa- _rubutaccin al'amari_

   __________________

*_sauran da basuji sunayin su ba kuna rai na dik ina miqa jinjina ta agareku...👍🏻 {writer's,, allah yabiya ku yaqara basira da hasken ido, allah yakare mu daga sharrin mahassada ameen_*👏🏻


*(13-14)*...gsky ni,,wallahi dik nagaji dan allah kusauke  ni, agida kuqarasa rabon, Invitation, din"wllh kyana nakejin naman ciyo,, tabd'i jam, kinma isa wllh karma kifara inji aysh.. komy dake za'ayi karma kifara mana wani jaye2. raliya tace lallai kam gsky zee kidaure har agama bikin nan,, munsan yanda kike ji tinda daman ke ba maci ce mai son hayaniya ba, dayar dake cikin qawayin amarya ce tace, dan allah kumata uxuri nayau kawai ciyon kai fa ba dadi„ aysha badan taso ba haka suka sauke zee a gida sukacin gava da rabon invitation dinsu gidan sauran qawaye, wayar aysha ce dake kan cinyar ta, tafara rinigin saurin dauka tayi„ dan ganin angonta ne kasim ke kira, hello" dear' ykk? ya shirye2??, tace alhamdulilah my hubby, albishirin ki? tace goro, kuna inane gamu zamu dawo gida munje rabon, iv ne,, ok tohm kuyi sauri kudawo gamunan zuwa,, yau dai zakiga emran abokina danake tabaki labarin sa ,, aaaa…haba?😳  da gske kakeyi? allah kuwa tabb" kace yau tare kake da babban baqo kai amma gsky naji dadi" yaushe kuka shigo zariya ne? bamu jimaba muna masauki yanxu haka, kinsan fa da qyar ya biyoni sai da nahada sa da mamyn sa,  sannan yayar da mukazo tare, wai shi wllh gsky natakura shi,, nace masa ai byma ga komy ba dan wllh dik *events* din da za ayi sai yaje, heheh gsky wanan abokin naka halin sa sai shi,, toshi da zayyi tsaye ayi komy dashi? bako emran ba kasim yabata amsa„ lallai kanada aboki kam, hmm,kedai bari ina ma kinka sani harda sharadi ya gindaya man idan zamuxo gunki nafada miki karki kuskura kibari wata qawarki tara kaki dan shi gsky baya son kallo … tohhh fa"🙄 wata sabuwa… wani abu yakeda shi ne wanda baya son a kalla? 😃 kedai sai muxo kiyi yanda yace kisa abude mana qofar baya tanan zamu shigo,, toh shikenan ba matsala sai kunzo,,yawwa"

bayan sunyi sallama ne, aysha kecewa Babbar mgn kunji wani abin mamaki kuwa? su raliya suka ce a..a saikin fada, nan takwashe komai, tindaga farkon lbrn da kasim ke bata. akan emran har wayar nan da suka qare yanzu,,bata rage musu komy ba tasanar dasu,, dai2 kuma lkcn da suka iso gida, bayan sunfito daga mota ne, teema kece wai ni kunsan wani abu? nifa ganin nake dik yanda akayi mutumin nan musaki ne dan inhar ba nakkasashe bane taya za ace wai mutun baya son agansa, d'ai daga cikin qawayin amarya mai suna hanna, tace gsky nima haka nake gani, atare sukace aiko wllh yau sai munyi ganin qwam 💃🏻💃🏻💃🏻

Gsky nima baza a barni abaya ba sai naje  angano

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 24, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WANI SALOWhere stories live. Discover now