15

340 19 0
                                    



     •✨•✨•✨•✨•✨•

Shirin biki ake ranga ranga from both site na couples 'din bikine Wanda kowa yake lale marhabun dashi,kasancewar ashraf shine namiji babba agidansu Kuma shine auren farko daxa'ayi na babban 'da namiji agidan,to ta 'bangaren amarya Ummi Aisha ma hakan take shiri ne aketata yinsa bikin fari Kuma bikin babbar 'diya agidan....Ankon dasu Waliyya suka fitar yayi Kyau ba 'karya kafin kace me ya 'kare ansake ordering wasu,kowanne event da ankonsa sede ba a tsawwala ba iya nagida-nagidah ne kawai xasuyi amma saboda halin karamci da dattako irin na hafst shiyasa har ma'kota wasu sukai dashin xubin 'daukar farko dukde akan suma su samu suyi ankon Ummi Aishan.

Sosai hafsat da 'yan uwanta suka shiga gyaran Ummi Aisha,gyara ne akeyi matashi wanda yakama daga gyaran jiki ciki da wajensa,harwani 'kamshi ne yake tashi na musanman inde taje waje koda kuwa giftawa tai,yakaka kala itace wadda ke mata gyaran jikin,yanxu kam babu laifi Ummi Aisha tafara maida jikinta duk 'kasusuwan wuyanta dasuka futo kamar sar'ka sunkoma ciki ta'kara fari hasken fatarta ta bayyana sosai,jikinta kuwa harwani luwai luwai fatarta tayi kamar na jarirai,sosai akayo iv cards kala kala na events 'din Wanda 'kwara uku daga ciki na gidansu ashraf ne xasuyi;bu'dan kai,barbecue day da kuma dinner se katin 'daurin aure na musamman da aka bugoshi,sosai akabi dangi da abokanan arziki aka raba masu katinan gayyatar,tun biki na rage sati 'daya gidan ya cika taf da yan uwa na maiduguri,jimetan yola,hadejia da Kuma 'yan kaduna angyare gidan tsaf har fenti aka sakeyi,sosai captain adam yabada ishashshen ku'di aiwa Ummi Aisha komai dakansa kuma tun sanda aka kawo lefe yatafi dubai yai mata siyayyar kayan gadaje da kujeru da komai ma daxa'a sanya agidan na kitchen ne kawai yabada ku'din asiya mata anan,ranaku suxo su wuce harde bikin Ummi Aisha ya rage saura kwana uku Kuma haryanxu ashraf baya kiranta awaya ba Kuma yaxuwa gidan koda ta kirashi baya 'dauka,

Washegari;

Xaune Ummi Aisha take ta kifa kanta tana rera kuka ahankali acikin 'dakinta,knocking 'kofar 'dakin akai da sauri ta mi'ke tana goge hawayen nata gudun kar agano kuka take kuma bataso ta tada hankalin ammin nata,itakam batasan me ashraf yake nufi da hakan ba,bu'de kofar tayi Waliyya ce tashigo janye da akwatinta da alama taxo kenan har agama biki,rungume juna sukai kowanne da murmushi a fuskarsa sun 'danyi hira kafin waliyya tace;

"Tawan meyafaru?!"

"Me kika gani bestie?!"Ummi Aisha tace hakan tana 'ko'karin 'ka'kalo murmushi,

"Haba tawan,ai baxaki 'boyemin damuwar kiba shekarar mu nawa tare?!kinsan halina nasan halinki wallahi kuka kikai Kuma akwai abinda ke damunki dan Allah menene?!"

"Bakomi bestie"

"Allah fa nace"

Hawayen datake 'boyewane ya xubo,tai saurin sa hannunta tana gogewa,

"Bestie bansan me ashraf yake nufi ba bansan meya 'boye cikin zuciyarsa ba,bakya ganin wannan auren da mukai akwai wani wani 'boyayyen lamari cikinsa?!nifa inaganin yasa ankawo lefen nanne kawai saboda wani abu daya 'kudurta azuciyarsa banso ingayawa ammi ne kada tasa damuwa aranta"

"To ke ki kirashi mana tawan"

Ummi Aisha tasa hannu ta'dakko wayarta agefen kujera ta mi'kawa waliyya,

"Duba kigani"

Kar'bar wayar Waliyya tai tagani sau 22 Ummi Aisha tana kiran ashraf be 'daukaba ga texts 'din datai masa nan ba'adadi,Ita kanta bataji da'diba bakuma taso ta nuna mata kada ta'kara tayar matada hankali,

"Babu komai tawan kicigaba da addua kawai kinsan dama dole ya'danyi fushi na wani 'dan lokaci  amma I assure u komai xedawo yadda yake da yardar Allah,aida bedamu dake ba kotakaina baxe biba amma muna waya dashi muna shirya duk yarda xa'ai komai yacemin ma xasuje bridal tea party 'din shida abokanansa amma baxasu da'deba"

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now