ANYI GUDUN GARA 59-60

Start from the beginning
                                    

Tattare wurin tayi ta nufi dakinta

______________________________

Yasmin ganin kusan sati daya da tafiyar Amal duk ta kirata a waya Bata samun ta,Kuma ya isa ace ta dawo Dan haka yau ta shirya zata je gidan su,Tana fitowa falonsu mommy ta da Yaya Nasir ta tarar zaune sallama ta ma mommy Nan yaya Nasir ke tambayarta Ina zata je take fada masa tashi yayi yace muje na aje ki dama fita zanyi,ita dai Yasmin murmushi kawai tayi Dan tuni ta harbo jirgin yayanta shiru kawai tayi tunda be Mata maganar ba

Fitowa sukayi suka shiga mota , sun fara tafiya yake tambayarta wace unguwa tace unguwar Rimi ,har kofar gidan ya kai ta sannan yace ta gai da masa da Amal din in ta tashi tafiya ta kirashi yazo ya dauke ta ,cewa tayi "to yayi Yaya"

Ta shige cikin gidan ,ya dade kofar gidan Yana me jin dadin sanin gidan da yayi ,Kuma Yana ganin lokaci yayi da ze gabatar da kansa a wurin Amal

Ko da ta shiga ta isko ummee falo gaisawa sukayi cikin fari'a  ummee ke cewa "yau an ka wo min ziyara ne"

Murmushi  tayi tace "eh ummee, sannan tace Amal na Nan kuwa,Ina ta kiranta a waya Bata shiga"

"Amal ta koma gidan mijinta ai ,mijin ya dawo daga tafiyar da yayi"
Cewar ummee

Shiru Yasmin Tayi Tana mamakin abunda taji ummee tace,se dai Bata ce komai ba, cewa  tayi ummee ko Zaki min kwatancen gidan , ummee tace Bari driver yazo ya kaiki jaji ne kin San ba lallai ki gane gidan ba

Kiran driver ummee tayi a waya tace ya Kai Yasmin gidan Amal ,Yasmin a sanyaye ta fita a gidan ta shiga mota driver ya ja motar suka tafi,har kofar gidan Amal ya kaita

Fita tayi ta shiga ciki ,ta fara kwankwasa kofar falon ,Amal ce ta fito kitchen ta nufi kofar ta bude ,zaro ido tayi da taga Yasmin kafin ta rungumeta dan ture ta Yasmin Tayi a jikinta ta shiga falon 

Fuska ba walwala ,Take Amal ta gano laifinta zama tayi kusa da Yasmin ta kamo hannunta tace"Dan Allah kiyi hakuri da boye mikin da nayi Ina da aure,bansan yadda Zan Miki bayani bane shiyasa nayi shiru"

Kallonta Yasmin Tayi shekeke ,sannan tace to ki bani ruwa ko se na roka"

Da sauri tace "A'a"
Mikewa tayi ta nufi kitchen se da ta shige Yasmin Tayi murmushi tace miskila kawai kallon falon ta ci gaba da yi har idanunta suka fada kan farouk Masha'Allah tace,Ashe babban soja Amal ke aure gaskiya ta taya Aminiyar ta murna, ta fada acikin ranta

Ruwa da lemu Amal ta kawo Mata Tasha ,sannan tace "bani labari me yasa kika kasa fada min

Labarin yadda auren nasu yake tun farko taba yasmin,sannan ta kare da Kinga ba son juna muke ba fa ,kila ma auren ya kusa mutuwa,da sauri Yasmin ta rufe bakinta tace"kar kice haka ni yadda ki ka ban labari na lura ba karamin so yake Miki ba ma kawai ki saki jikinki kusha soyayyar ku malama"

Sororo Amal tayi Tana kallon Yasmin kafin tace"dawa za'ayi soyayyar Allah ya kiyaye ,mutumin da har yanzu be ce Yana Sona ba ,Zan wani shige masa"

"To Bari kiji idan kika yi Wasa tsaf wata zata kwace maki shi in kika tsaya Jan aji,in Zaki ji shawara ta tun da miskili ne ,to kizo ki fara Abubuwan da Zaki jawo hankalinsa akanki Wanda Dan dole ze bude Baki yayi magana,daga Nan cikin ruwan sanyi Zaki hukunta sa ya gano cewa Allura ma karfe ce"

Dariya Amal ta saki ,ita ma Yasmin haka ,se sallama suka ji ya shigo da sauri Yasmin Tayi shiru ,Amal Kam ci gaba tayi da dariyarta ,tunda ya shigo idon sa na kan Amal da yaga dariyar ta matukar yi Mata kyau har da murmushin gefen Baki yayi,duk Yasmin na kule da shi kafin tace"Ina wuni"

Yace lafiya Lau zama yayi daya daga cikin kujerin falon ,suka Kara gaisawa da Yasmin , ya saki jikinsa se tambayoyi yake Mata Nan ma yasan kawar Amal din ce

Amal se mamakin wanna shishigin nasa take
Yasmin ce ta mata signal da ta bashi ruwa,Bata fuska tayi se da taga Yasmin din ta harareta sannan ta Mike ta dauko ruwa da lemu
Ta kawo gabansa dukawa tayi Tana zuba masa ,tuni idanunsa suka masa kyakyawan gani ,lumshe idanun sa yayi ,Mika masa cup din lemu tayi se da ya hada da hannunta ya Dan rike kafin ya sake ta

Yasmin yi tayi kamar Bata ga abunda ya faru ba, Amal ce tace Mata zo muje daki kiga wani Abu mikewa sukayi suka shiga daki

Suna shiga mikewa yayi jiki a mace ya nufi dakin sa

Suna shiga kan stool din madubi Yasmin ta zauna kafin tace"kawata mutumin Nan fa na lura ba karamin sonki ya ke ba wallahi Kinga kallon da yake Miki kuwa

"Kamar wani maye ,anya ba so yake kawai ya sameni a bagas kuwa ba"

Yasmin tace"to miye Dan ya same ki ba sadakin sa  ya biya ba,ke dai kiyi Amfani da shawarar da na Baki ,shi da kansa ze bude bakinsa ya fada Miki Yana sonki ko ba shi kike son ji ba, daga Nan Kuma dole ki saki jiki ya gurji Amarcin sa "

Duka Amal ta Kai Mata ,da sauri ta goce Tana dariya tace"Ehh Mana gaskiyar ke nan,in Kuma kika na ganin Wasa ne ki zauna Nan se dai kiji yayi auren sa ya barki "

Yawwa Ina kayanki suke na lefe na diba Miki kayan da ya Dace ki dinga sawa
Nuna Mata su tayi

Ta jawo su kuwa ta shiga budewa,har ta cimma English wears nan ta zabo Mata masu kyau ,tace to gasu Nan se ki dinga sakawa

Kallon ta kawai Amal ke yi har ta fitar da kayan ,sannan tace "Yasmin yanzu kina ganin ya Dace na saka kayannan karfa ya ga zakewata da yawa"

Yasmin se da ta Harare ta tace"ya gani Mana ba mijinki bane "

Shiru Amal tayi Dan ta San tsab Yasmin zata balbale ta da fada in tace ba zata saka ba

Bayan ta gama Nan ta shiga Mata hudubobi kala kala ,Wanda ita Amal mamakin yadda yasmin din tasan wasu Abubuwan da yawa take
Daga karshe tace"in kinyi Amfani da abunda nace kin taimaki kanki in ba haka ba wannan basamuden mijin naki ko ta karfi se ya kwaci hakkinsa ,sannan ko soyayyar da kike son ya bayyana Miki  ya Kiya Kuma ya je yayi aurensa da ya gano Baki iya kula da shi ba"

"Zanyi tace "kamar wata yarinya,Yasmin dariya ke cinta amma Bata yi ba ,Dan ta kula Amal na matukar tsoron gamonta da soja ga Kuma kishi

Se dai a ganinta shawarar da taba kawarta shine daidai in ba haka ba yadda matan yanzu suka lalace tsab wata zata kwace Mata shi ko a cikin barikinnan ma
Har dai kabilun ciki da suke shiga kamar tsirara

Ta dade se zuwa marece ta Mata sallama Akan zata dawo, Dan taji kwanakinnan exam din su zata fito

Har kofa ta rakota
Nan take ce Mata ta gwada Abubuwan da ta fada Mata yau fa
"To" tace mata

se ga farouk ya fito shima ze fita  cewa yayi muje na aje ki gida
Ba musu ta bishi ita Amal  gida ta koma bayan sunyi sallama

Da Daddare bayan ta gama sallar Isha'i ta dauko kayan da Yasmin ta fitar Mata ta kula duk ba na mutunci a ciki se wata English gown red se dai ba har kasa ta Kai Mata ba ,sannan spaghetti hand gare ta ,ita ta saka ,ba karamin kyau ta Mata se dai fa ta fallasa asirin jikinta Baki daya ,ita kunya ma ta fara ji Tana Shirin cirewa taji anturo kofar dakin an shigo,shine ya shigo kuwa ,kallonta yake yi ba ko kiftawa ,takowa yayi ya nufo inda take hijabin sallar ta ta dauko zata saka karbe hijab din yayi ya jefa kan  gado ya wani  rungumota sosai,take ta fara kicikicin kwatar kanta Ammah ta kasa ,sunbarta ta ya shiga Yi kafin Naga Yana kokarin cire zip din rigar jikinta ya Kuma nufi bed da ita ,gaba daya ya fara fita a hayyacinsa ,in Banda kuka babu abunda Amal take ,juyata yake yadda ransa ke so ganin Abubuwa sun fara gudana na nufi hanyar fita
Leemat se ingizani take na koma na dauko Rahoto,Raliya da su ummu afaf na jawo ni,muna cikin wannan jayayyar ne na jiwo karar Amal tuni Alkalamina ya fadi kasa..................✍️


*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now