ANYI GUDUN GARA 41-42

Start from the beginning
                                    

Ji tayi ya Kara Mata wani Abu akai
Dago fuskarta tayi kawai se taga karamar bindiga a kanta , idanunta ta fara kyafkyaftawa bakinta na motsi tuni idanunta suka lumshe tayi baya ta zube akan carpet
Tsaki yayi ya Mike ya nufi fridge ya dauko ruwa

Yana zuwa yau be yi da mugunta ba ya zuba ruwan a hannunsa ya shafa a fuskarta ai ko ta kawo numfashi

Komawa yayi ya zauna ita ma Tana bude Ido ta gansa ,ai se ta saki kuka

Tsawa ya Mata yace"rufemin Baki Kona sa bindiga yanzu na dauke kanki, Kuma maza goge hawayen nan"

Da azama ko ta maza ta goge ,Tana Jan ajiyar zuciya

Kallonta yayi na 'yan sakanni ganin ta samu natsuwa se ya fara magana kamar haka "kina jina ko idan kika sake ganina kika yi kuwa ko kika dauke numfashi to ranar ba'abunda ze Hana nasa wannan bindigar da kike gani na harbe ki kowa ma ya huta"

Tsinto muryarta yayi Tana cewa "Dan Allah kayi hakuri kar ka kasheni"

Ba karamar dariya ta basa ba ,ya kula bakaramin tsoro ne da ita ba se dai ya kanne beyi ba yace

"Ni wanna ba matsalata bace yanzu ya rage naki ki ,sannan kulum se kin fito falonnan kin zauna da safe kafin na fito ,Ina fitowa ki daga kanki Kita kalo na da murmushi Ina karasowa ki gai Dani har se na fita ,

Abu na biyu ban son kazanta dole ki fito ki dinga kula da gidannan ,abinci Kuma Zan Nemo masuyi Dan nasan ba'abunda kika iya tatsitsiya dake

Daga yanzu ke Zaki dinga wanke min uniform dina kina jina "

da sauri murya na rawa tace "ehh"
Zanga karshen tsoron da aka ce kinayi na masu uniform , tunda da kika tashi duk kika tsallake sauran kaki ki ka fado kan soja

"Ni nama fara zargin ke kika je kika ce kina Sona, ko ba haka bane?"

Hawayen da ke ta zubo Mata take sharewa murya na rawa tace
"A'a wallahi nima ba'a son Raina bane kaddara ce kawai Ammah me zesa na auri soja"

Wani Abu yaji yana taso masa tundaga zuciyarsa yazo kan magoransa ya tsaya be fito ba, yana mamakin yadda har ta bude Baki a gabansa Wai bata son soja,lallai ya kamata ya koya Mata wani hankali


Cewa yayi "zo nan"

Rarrafowa ta fara yace "Mike tsaye kizo nan yayi nuni da gabanshi "

Kafafuwanta na hardewa ta tako ta tazo fizgota yayi kamar zata fado jikinsa yayi azamar matsawa ta fado gefen sa kafin ta daidai ta se saukar hannunsa taji Akan bakinta

Duk da yaji labban nata akwai taushi Ammah be Hana ya fasa abunda yayi niyya ba ,wata irin murza yake ma labban nata da zafi zafi Aiko tuni hawaye ke zuba a fuskarta ta ta kokarin ta kwaci kanta ta kasa

Se da ya gaji Dan kansa ya saketa Aiko nan take labbanta sukayi sutum ,sutum

"Kalle Ni"

Dago rinannin idanunta tayi ta kalle sa ,se da gabanta ya fadi ganin yadda idanun nasa ke rikitar da ita , sunkuyar da Kai take kokarin yi

"Ki kallan na ce"

Kallon sa take tana kuka ,yace "daga yau duk na sake jin kince dole aka Miki a aurena ,ko Kuma Baki son soja ko me kaki jikin kine ze fada Miki "

Kuma masu kaki kisa a ranki daga yau kin fara sonsu kina jina ta daga Kai
Yace da Baki Zaki ban amsa

Tace "Ehh"

Tashi yayi ya dau bindigar sa ya nufi dakin sa

Ai Amal kukanta ta ci gaba dayi anan Tama kasa tashi banda azaba Babu abun da labbanta ke Mata

Motsin fitowar sa taji da sauri ta hadiye kukan da take ,matsowa yayi ze fita yace"ki tashi kije kiyi sallah ,Kuma alkawarin harbinki na nan matukar Baki bar wanna sakarcin da kike ba

Yana fita ta dago Kai tace"Allah ya saka min a fili"
Tashi tayi ta nufi dakinta

Bayan ya fito daga massalaci ne yaya Sadiq ya sake kiransa be daga ba kasancewar ya gane number ,gida kawai ya nufo yana tunanin kurciya irin ta wannnan yarinyar da aka lakaba masa

Da ya tuno yadda take kuka,se da ya Dara
Nace to fa🤔

Yana shigowa dakinta ya nufa ko da ya shiga Tana kan daddumar da ta gama sallah

Gai da shi tayi ya Amsa ,sannan yace yawwa waye Abubakar sadiq a kano ,dago Kai tayi se kuma ta sunkuyar da shi ganin ita yake kallo

Ta fara da"Ahm yaya nane Dan yayan Abba nane,Kuma shi yake auren yayata"

Tabe Baki yayi yace "to ya Kira suna son magana dake ,duk kika yadda kikayi magana akai na Zan gane"

Ya aje wayar kan madubi ya fita

Ba karamin dadi taji ba jin cewa yaya Ramla ce ke son magana da ita tashi tayi ta nufi madubin ta dau wayar Aiko se ga wani Kiran ya shigo.................✍️



*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now