DR MUHRIZ
(FITATTU BIYAR)
NA ZEE YABOUR
WATTPAD ZEEYABOUR
HASKE WRITERS ASSO
*Home of expert and perfect writers*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI'*
ALHAMDULILLAH DA ALLAH YA BANI IKON FARA RUBUTA MUKU WANNAN LITTAFI YADDA NA FARA LAFIYA ALLAH YA BANI IKON GAMAWA LAFIYA
MASOYANA A DUK INDA KUKE INA MUKU FATAN ALKHAIRI, NAGODE KWARAI DA SOYAYYAR KU GARENI
*Free page 1*
A hankali ta bud'e idanun ta, tana bin d'akin da kallo, yayin da kallon ta ya tsaya kan hannun ta dake sak'ale da drip, ko shakka babu asibiti ne, asibiti na masu hannu da shuni, irin wanda sai masu gata da galihu ke zuwa, ba irin ta ba da kare ma yafi ta daraja a idon wasu, wa yayi shisshigin kawo ta, sam asibitin ba kalar ta bace, ya zama dole tayi gaggawar tafiya, kafin a kawo mata bill da bazata iya biya ba, a wulak'anta ta,
Tashi tayi zaune, kanta na tsananin sara mata, Ta shiga k'ok'arin fisge drip d'in,
"Ke Nana me kike shirin yi?" Matashiyar budurwa ta fad'a tana shigowa da sauri, ta kama hannun ta tana k'ok'arin dakatar da ita, Rinannun idonta ta d'ago ta kalleta tace "Aunty Sakeena ke kika kawo ni nan?", Ta d'aga kai sama tace "Eh, wani abun ne, ko nayi laifi yin haka", Ta k'arasa tana kafeta da kallo, sanin halin ta, "A'ah Aunty baki yi laifi ba, amma wannan asibiti tafi k'arfi na, Dan Allah ki mayar dani asibitin murtala can na saba zu..."
Kallon da ta jefa mata yasa ta kasa k'arasawa, "Ban san sai yaushe zaki saki jiki dani ba Nana, ki d'auke ni tamkar yayar ki da kuka fito ciki d'aya, kamar yadda na d'auke ki k'anwata jini na", "Ko kad'an ba haka bane Aunty Sakeena kawai dai..." Tayi saurin katse ta "Kawai dai me, kin ga Dan Allah bana son sake jin komai, koma ki kwanta kina buk'atar hutawa", Ba tare da musu ba, ta mayar da kanta kan pillow ta kwanta, a ranta tana jinjina girman soyayyar Aunty Sakeena gare ta, wacce basu had'a komai ba, jini ko kad'an bai tsaga a tsakanin su ba, hasalima tafi k'arfin ta, amma a ko da yaushe take k'ok'arin had'a kanta da ita, take nuna mata tsantsar k'auna tamkar yar'uwarta ta jini.
"Bara naje gida na taho miki da abinci, tun d'azu naso tafiya, na jira tashin ki gudun kada ki tafi" Cewar Sakeena tana mik'ewa, Tamkar tace ta bar shi, sam bata jin cin abinci a halin yanzu, gudun b'acin ran Sakeena yasa tace "Toh a dawo lafiya", "Ki kula da kanki plss idan kina buk'atar wani abu, ga telephone ki kira nurse", Ta amsa da toh tana kai dubanta ga telephone dake gefenta sai a lokacin ta lura da ita,
Idanunta ta mayar ta rufe, tana tuna abunda ya faru da ita ranar yau, da yayi silar kawota asibiti, hawaye masu zafi ke bin gefen kuncin ta, yayin da zuciyarta ke rad'ad'in ciwo, tana jin ina ma Allah ya d'auki rayuwarta ta huta da dukkan bak'in cikin da take fuskanta, sam bata san dad'in rayuwa ba, bata tunanin rayuwarta zata tab'a daidaita, taji dad'i, tayi rayuwa kamar sauran mutane har ta koma ga mahaliccin ta, duk da cewa bawa baya cire rai ga rahamar ubangiji.
Mota ce bak'a wulik mai azabar kyau da had'uwa tayi parking harabar makeken asibitin, jin tsayuwar mota yasa ya bud'e idanun sa dake lumshe ya lula duniyar tunani, fuskar sa sam babu walwala, da sauri driver ya fito ya bud'e masa murfin motar, K'afar sa ta dama ya fara saukewa k'asan interlocks dake shimfid'e farfajiyar asibitin, sanye take da tsaddadden black cover shoe, cike da k'asaita ya fito, yana kai duban sa ga agogon dake d'aure a wutsiyar hannun sa, tsaki yayi ganin ba k'aramin makara yayi ba, Ya soma tafiya cikin hanzari, driver sa na take masa baya rik'e da briefcase d'in shi, mai d'auke da muhimman takardun shi,
Tun daga bakin k'ofa yake amsa gaisuwar ma'aikata, yayin da mafi yawa daga ciki suke bin shi da kallo, suna yaba tsarin sa, kama daga kyawun halittar sa, zuwa ga suturar dake jikin sa, Matashin saurayi ne wanda ba zai gaza shekaru talatin a duniya ba, mai cikar zati da hibba, fari ne sosai, farin da ya had'u da hutu gami da halitta, Allah ya bashi baiwar kyau, kwarjini da farin jini, wanda babu macen da zata d'aura idonta a kansa ba tare da taji zuciyarta ta d'arsu ba, hatta maza yan'uwan sa yana matuk'ar burge su, suna son mu'amala dashi, duk da kasancewar sa mutum ba mai son hayaniya ba, da shiga al'amuran mutane, wanda hakan yasa mutane da dama ke masa kallon mai girman kai.
Passage da zai sada ka da ofishin sa mak'il yake da mutane masu hannu da shuni, wanda suke jiran isowar nasa, ba tare da ya kai duban sa gare su ba, ya k'arasa office d'in sa, ya shiga, girman sa kad'ai abun kallo ne, ya had'u iya had'uwa, ban da kayan ayyukan likita dake ciki zaka rantse wani hadadd'en wurin hutawa ne, komai tsaf sai sanyin Ac da k'amshi ke tashi, kasancewar kullum yana samun gyara na musamman, Mutum ne shi mai tsananin tsafta, dama likitoci an san su da tsafta, sai dai shi tasa a jini take,
Zama yayi kan lumtsattsan kujerar sa, Driver ya ajiye jakar cike da girmamawa ya fita, Medical glasses d'insa dake cikin case, ya d'auka ya goge, ya saka, wanda ya k'ara fiddo kyawun sa,
Nurse ta shigo rik'e da files na patients da zai duba a ranar, ta ajiye gaban sa, tana gaishe sa cike da ladabi, ya amsa ba tare da ya d'ago kai ya kalleta ba, a tsarin sa baya kallon mace, yana da matuk'ar wuya ya kalli mace, sai idan aikinsa ya fashi duba fuskar ta, shima ba tsayawa yake ya k'are ma halittar ta kallo ba, da yawa idan yayi treating patient, ko a hanya ya gansu baya gane su, su ke k'ok'arin yi mishi magana, ya amsa ba tare da ya gane ba, but lokuta da dama yafi basarwa tamkar bai ji ba,
Ya umarce ta, ta kira patient na farko.
Sakeena ke ta faman jera kulolin abinci cikin basket tana sauri, ta koma wurin Nana ta barta ita kad'ai, "Ke" ta jiyo muryar mahaifiyar ta cikin tsawa, A razane ta juya tana kai dubanta gareta, Tsaye take cikin tsadadden lace, kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin daula, fuska babu annuri tace "Kar kice mun Nana kike shiryawa wannan abincin", Cikin sanyin murya tace "Kiyi hak'uri Mummy, bata da lafiya tana asib....", "Dalla rufe mun baki, yarinya kamar ta shanye ki, banda komawa baya yaushe zaki zauna kina mata hidima, kar ki manta a k'ark'ashin mu take, ita ya dace da miki hidima ba ke ba, ni wallahi tsorona ma ta gurb'ata miki tarbiya", Zata sake magana ta katse ta, "Maza ki mayar da abincin nan, ki wuce d'aki ba inda zaki sake fita" Ta fad'a tana ficewa kitchen d'in, ta koma sama bayan ta gargad'i direbobin akan kada wanda ya fita da Sakina, masu gadi tayi warning d'insu kar su bari ta fita, sanin zata iya fakar idonta ta fice.
Sakina tsaye tayi cikin takaicin halin mahaifiyar ta, yayin da tausayin Nana ke ratsa zuciyarta sanin bata da kowa da zai taimake ta, gashi ta kaita asibiti mai tsada, tana gudun abunda zai biyo baya, "Ya ilahi" ta furta, ganin bata da wata mafita.
DR MUHRIZ NA KUD'I CIKIN LITTAFAN FITATTU BIYAR
ANNURIN ZUCIYA NA HAJJA CE
SILAR WAYE NA FEEDHOM
DR MUHRIZ NA ZEE YABOUR
YARIMA FAYAD NA ZAINAB BAWA
GIMBIYA SUHAYLA NA NANA DISO
LITTAFI BIYAR AKAN 500
HUD'U AKAN 450
UKU AKAN 400
BIYU AKAN 350
D'AYA AKAN 200
TURA KUDINKI TA WANNAN ACT D'IN
3126584401 FIDDAUSI MUSA FIRST BANK TARE DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08036953516
KO KUMA
ACT NUMBER: 0003075326 ZAINAB M BAWA JAIZ BANK SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08161146563
KO KATIN WAYA MTN TA WANNAN LAMBAR 07065283730 TARE DA SHAIDAR BIYA......
ZEELISH🌺
YOU ARE READING
DR MUHRIZ
General FictionTun tasowar ta bata san dad'in rayuwa ba, ta taso cikin rayuwar tsangwama, kyara da hantara, a lokacin da take tsaka da gwagwarmayar rayuwa k'addara mai girma ta afka mata wacce ta k'ara jefa rayuwarta a rud'ani da kyamatar al'umma, Ta rasa gata, ta...
