Soyayyata Da Majnun

86 7 0
                                    

Soyayyata Da Majnun

     By; Najaatu Naira

        FKD Fans Writers 《《 01 》》

Ina zaune gefen gado,
Dad'da'dan iska na suraromin ta window, cikin ni'ima na lumshe ido ina murmushi kamar anmin kyautan hajji,
Dauke nake da hoton muradin zuciyata wanda akullun saina daurasa saman kirjina nake samun damar barci.
"Habeeb Ma'aruf" kenan,
Nadago hotonshi ina kallo da akoda yaushe yake shagaltar da nutsuwata gami da tunanina.

Allah sarki rayuwa wani nataccen hawaye ya sulcemin, nayi sauri nagoge dan gudun kar Umma tashigo tasameni ayanayin da nake ciki,

Kaddara kenan, kaddara maisa lokaci yaja, shekaru shadaya kenan rabona da Habeeb amma jinake tamkar yaune, banta'ba musulta kamannin Habeeb ko yanayinsa da kowani 'Da namijiba,
Hotonsa na'ajiye gefen gado nazubama ido, yabude hakora yana murmushi, Allah maikullun sainayi lattin makaranta sabida kallon hoton, wani lokaci harsai Umma tashigo da muciya dakina takoreni,
Akintace nasan bazaifi shekara shabiyu da'akadau hotonba,

********
Munfito daga makaranta KASU tare da Qawata Habiba Muna gefen titi muna kwasan kwalleliyar ranan da ake makawa,
Wata galleliyar sabuwar mota blue kirar Peugeot 407 tafaka agabanmu,
Bamu ko 'dagakai munkallah inda yakeba saima matsawa da mukayi danmubashi damar yin parking.

Muna matsawa yana matsowa harya'kure mana yamatso yayi parking daidai gabanmu,
Tsaki nayi hadi da kallon motar nace wulakanci kawai.
Habiba takalleni cikin yauki tace "da Allah kyaleshi, muma in Allah yayarda zamui abun hawannan kodan muwuce wulakanci",
"Sallamu Alaikum Yanmata"
Muryan da mukaji maidadin saurare yasa gaba daya muka 'dago kai muka kalleshi,
Dogon namiji baki,
Yanada 'yan manyan ido da siririn hanci,
Yanayin tsayinsa da fadin kirjinsa yayi daidai da maishirin film din india Prabhas saidai shi wannan ba'kine.

Tsab muka karemai kallo kan muka kauda fuska, barin Ni dahar nahada da'yar guntun tsaki.
Da sauri yafito yatari gabanmu yana murmushi yace "haba 'yanmata ana sallama kuna kauda kai kodan kunga kunada kyau saikuma kudinga wulakanci?",
Murmushi Habiba tayi yanda yai narainarai da fuska, nikuwa sai lamarinsama yafaraban haushi nace "dan Allah dakata Malam munada abunyi katare mana hanya, kabamu waje muwuce",
"Anki, anki abaki wajan kuma kimin shiru inyi magana, kina wani shan 'kamshi dankinga anasonki, so nake na taimaka maki",
Wani irin kallo na'dago kai naimai hadi da'dan kasalallan murmushi nace "daga gani kafiya surutu, nikuma kaga mutane masuson 'dumi haushi sukeban",
Da dukkan alama maganar bataimai dadiba, ya'kuramin ido yana murmushi yace "Toh badamuwa, ina zaku inrage maku hanya",
"Hayi zamu" nafada atakaice.

Kokadan banjin 'dar din fadan sunan anguwanmu domin nasan ko lift mutun yayi niyyar bamu dazaran yaji sunan unguwar yake janye motarsa ya'kara gaba",
Duba da yanayinsa danaga nandanan yachanza yana dogon nazari naimai wani irin kallo nace "bazaka iyaba ko? To tafi kabamu waje musamu adaidaita sahu",
"A'a muje, zan'iya mana meye aciki, kinga idan naje dole zansan address dinki",
Sai alokacin na'dago kai mukai ido hudu, kallon danaga yanamin nayi sauri nakauda kai hadi da fadin "bazamu ba, kai tafiyarka kawai",
Dasauri Habiba tariko hannuna, murya 'kasa- 'kasa tace "Qawata bansan iskanci fa, dan Allah kibari yakaimu inma tsoro kike Abba yaganki saiki sauka gidanmu inya tafi kihau Bus ki qarasa gida,
Shiru nayi nadan muntina domin maganarta abun dubine duba da ko 'yan napep dakyar muke samu sukaimu.

Habiba ta'dago kai takalleshi tana murmushi tace "naroketa tace muje",
Murmushi yasaki dahar siririyar wushiyarsa tafito yace "toh nagode sosai",
Ban ankaraba ya janyo jakata yarike yace "barin rage maki nauyi",
Nadago manyan idona na kallesa nadan yatsina fuska nasaki guntun tsaki ganin yanata wani rawan kai,.
Yana bude motar nayi wuf nashige baya Habibama tabiyoni muka zauna,
Shiru yayi nadan muntuna yana rike da stearing mota yace "haba dan Allah yanzun saiku maidani Driver?,"
Yajiyo yakalleni yace "Malama kidawo gaba dan Allah"
Idona nabude tareda dan manyan labbana nace "Malam idanfa bazakaba bamu matsama ba",
Yanda nayi maganar yasan gab nake da barin motar,
Baice uffanba yatada motar yatuka har garinmu da 'yancikin gari ke zagi wai bayan gari.
"Hayi Rigasa"

Adaidai qofar gidansu Habiba Zaria Road yayi Parking,
Zamu fita ya datse motar yace "Haba 'yanmata babu introduction,
Ni sunana Amin Adam, kwanannan nadawo 'kasar, ina fatan zamu kullah zumunci"
Habiba tadago kai tace "sunana Habiba" ta dafani tace "itakuma Qawata sunanta Raina",
Tsaki nasaki hadida gallamata harara nace "waya tambayeki? kibari nafada dakaina mana"
Amin dake gaba yayi murmushi yace "Raina inason mukullah zumunci, ina nufin dankon soyayya dake"
Nayatsina fuska cikin siririyar murya nace "munada 'yan'uwa kuma banason soyayya dakai"
Yayi fari da ido yace "really!, toh Aboki fa?"
Naimai wani irin kallo mai nar'kufanci nace "bana abota da maza",.
Murmushi yasake yi yace "toh dan Allah kozan iya zama Driver ki? yaso duk sanda zaki fita anguwa kamar Opay saiki kirani",
Dukda yanda yayi maganar ya burgeni saidai zuciyata bata ra'ayin bashi dama, yama za'ai nabashi dama nida banta'ba tsayawa dawani 'Da Namiji da sunan soyayyaba, sai soyayyar Habeeb da nake dako tun bansan meye so ba bare ma'anarsa har kawo yanzu,
Na yatsina fuska nace "idan bazaka bude mufitaba Malam kamaidamu inda ka daukomu",
Ajiyar numfashi yayi yace "toh fine, bazan matsa makiba, amma zaki sake ganina",
Azuciyana nace for ur dream,
Nabude motar nafice Habiba taimai godiya tabiyo bayana,.

Votes, Comment and Follow.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 14, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Soyayyata Da MajnunWhere stories live. Discover now