*WANDA YA TUBA DAGA ZUNUBI, KAMAR WANDA BAI TABA YI BA NE

45 1 0
                                    

*WANDA YA TUBA DAGA ZUNUBI, KAMAR WANDA BAI TABA YI BA NE !*

*Tambaya*
Assalamu alaikum Malam. abokina yana son ya auri wata yarinya wadda ni na san abin da ta yi a baya ba mai kyau ba ne, shin don Allah in bayyana masa ko in yi shiru ?

*Amsa*
Wa alaikum assalam, Kana iya bayyanawa mutukar ka san ba ta tuba ba, kuma kana da tabbacin ta aikata, ai daga cikin wuraren da ya halatta a ci naman Mutum akwai wajan neman aure.

Amma in ka tabbatar ta tuba, ya wajaba ka yi shiru, saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taba aikatawa ba ne !!

Allah ne mafi Sani

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

25/06/2020

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU 3Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα