SHIN YAHALATTA MACE TASA HOTONTA A DP NA WATSAPP KO FACEBOOK?*_

70 1 0
                                    

*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

_*SHIN YAHALATTA MACE TASA HOTONTA A DP NA WATSAPP KO FACEBOOK?*_
:
_*Amsa:*_
:
_Mace *budurwa ko matar aure ko bazawara haramunne tasanya hotonta a facebook ko watsapp ko wasu fagage na internet,* Saboda al'amura masu yawa duk cikinsu akwai:_
:
_Sanya *hoton yana kore siturcewar da Allah ya umarci mata dasuyi acikin alqur'ani da sunnah,,* haka Allah yahana mace tadunga *karya magana gamazajem daba muharramanta ba*._
:
_Allah yashar'antawa *matan Annabi Sallallahu Alahi wasallam damatan muminai sanya hijabi suturce dukkan jiki daka maza dan tsarkake zukatan Muminai mata da daukesu daka guraren fitina da tuhuma,* dakuma *tsare farjinsu dana bayinsa muminai maza,* idan mace tasan wannan zai bayyana gareta cewa *sanya hotonta asocial media mutumin kirki dana banza zaiganta,* airin wadannan gurare *wanda hakan yaci karo da shari'ar Allah madaukakin Sarki.*_
:
_*Sanya hoton bude kofar fitinane da sharri ga mace* dakuma wadanda *suke ganin hoton, Nawa mukaji kuma muka shaida labarai marasa dadi masu kona zuciya ta dalilin hakan*, Mata *masu kirki da kamewa salihai suka fada komar marasa tsoran Allah fajirai suka yaudaresu da lafuzzah dakuma dadin baki*, da alkawuran na dogon buri, *harsai sunbiya bukatarsu dasu saisu juya musu baya,* daga nan babu abunda *yarage mata sai tabewa da asara da nadama, da kaskanci, wani lokacin shikenan sandiyar rasa duniyarta da lahirarta kenan, Allah yakiyaye.*_
:
_*Fajirai nawane suke amfani dawadannan hotunan dacanja musu kala tahanyoyi nazamani idan suka samu fuskar yarinya maikyau saisu sakashi ajikin fajirar mace,* dakanan shikenan takama nadamar abunda tajanyowa kanta da ahlinta, *lokacinda nadamar bazatai mata amfani ba.*_
:
_Abunda *wasu daka cikin mata suke qudurcewa wai sanya hoto mai hijabi wannan bai sabawa shari'a ba,* idan tasanyashi da hijab cikakke nashari'a kuma tarufe ko ina har fuska wannan yana halatta yayin bukatar hakan, *amma haka kawai babu wata manufa domin bazai amfani wanda tasaka shiba,*_
:
_*Amma idan fuskarta tana bude* koda tarufe jikinta baki daya *shima yana tattare dasharrin da muka ambata.*_
:
_*Imamul gazhali* acikin ihya'u ulumul deen ( 2/53) yace: Mazaje basu gusheba abisa shudewar zamunna face fuskokinsu abude, mata kuma suna fitane da nikabi,_
:
_*Alhafiz bin hajar* acikin fat-hul bari ( 9/424) Yace: Al'adar mata bata gusheba ada dayanzu cewa *suna suturce fuskokinsu daka Muharramnsu.*_
:
_Sannan *duk wani mai hankali yasan kyakkyawan waje wajan fitinuwa da mace shine fuskarta*,_
_fuska *itace abunda maza suke jarabar san ganinta, dashine kuma ake kiyasta kyawun mace darashin kyawunta*, dan haka *sanya hotonta awatsapp ko facebook dasauran wurare na internet bude kofar fitinane da sharri,* da wulakantata dakuma wulakanta hoton nata,_
:
_*yana halattane  lokacinda yake kasancewa* lokacin bukata da lokacin da'aka nema,_
:
'''wallahu A'alamu.'''
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*--------------------------*

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU 3Kde žijí příběhy. Začni objevovat