Sixteen - Bazan Barki Ba

Začít od začátku
                                    

"Naseera da kinji abinda ke faruwa anan da kinji tausayina kin kwantar da hankalin ki..."

"Nima daka san abinda ke faruwa a nawa kirjin daka kyale ni," itama ta gaya mashi. Runtse ido tayi cikin takaici. Mahfooz bazai taɓa ganewa ba, ta lura bayaso ya gane. Amma ai so ba hauka bane, dole ya duba lafiyar sa. A ina aka ce ayi makahon soyayya. Kamar yadda bayaso ya gaya mata labarin Fauziyya haka itama bataso ta gaya mashi komai game da ciwon ta. Ko miji da mata akwai sirri koda kaɗan ne, kuma wannan auren cetan rayuwa sukayi. Bayan sun bar nan bazasu sake ganin juna ba.

Magana ya soma yi a natse, kana ganin kalar idansa kasan ya canza. Bai ciko da hawaye ba amma yana hanya, "Tunda nake ban taɓa samun soyayya mai ɗaurewa ba, iyayena sun tafi sun barni ina ƙarami. Yar uwata mai sona... Mai k-kaunata ta ta-fi," in'ina ya soma saboda zafin bacin ran daya shiga. "Naseera ina sanki, kada kema ki gujeni,"

Bazata ce bata karaya ba, haƙiƙanin gaskiya ta tausaya masa matuƙa. Hawaye siriri ya soma sauko mata a idanu, koda munafinci ne Mahfooz ya nuna kaunarta a fili, yadda bayan iyayenta bata taɓa samun wannan ba.

"Mahfooz ni annoba ce!"ta furta saita fashe da kuka. Durkusawa tayi ƙasa tana sheƙawa."Idan kasan asalin waye Naseera na tabbata zaka guje ni da gudu, yasa tun wuri nace maka ka rabu dani...."

"Hey shhhh!" saiya tsaida ta tareda duƙawa shima. Tallabo mata kumatu yayi yana share mata hawaye. Bata hanashi ba, itama tana so a rarrashe ta. Tanaso a jaddada mata cewa ita ba annoba bace, kuma babu wani abu dake tareda ita. Tanaso a ƙara mata ƙwarin gwiwa. Yanda komai ya cunkushe mata tasan tana dab da kamuwa da ciwon zuciya inda kirjinta zai buga ta mutu.

"Ki sani Naseera nayi maki alkawari, ko menene ke damun ki bazan taɓa rabuwa dake ba. Basai kin faɗa min sirrin kiba, nima nasan sirri abu ne mai wuyan faɗi. Yana ɗaukar lokaci kafin ka faɗa. Amma ki sani koma menene, duk duhun dake rayuwar ki nayi maki alƙawari zan zamo maki haske a cikinta. Kamar yadda kika zamo tauraruwa cikin ɓakin rayuwa na, haka zan zame maki. Bai dameni ba koda aljana ce ke, eh zan cigaba da kasancewa dake. Lone wolf dies but not the pack. Inaso ki zaman min bindiga, ni kuma zan zame maki harsashe Naseera, domin mu taru mu harɓe maƙiyan mu, da duk wani wanda zai cutar damu cikin rayuwar mu."

Nisa yayi yana ajiyar zuciya, soyayyar Naseera sake tasiri takeyi cikin zuciyar. Ita kuma shiru tayi tana sauraron sa. Ta wani fanni ta samu natsuwa cikin kalaman sa. Taga gaskiya cikin idansa. Riƙo hannunta yayi yana murzawa a hankali yana murmushi, sunkuyar da kanta tayi ƙasa. Mahfooz yanada bala'in kwarjini, an sha gaya mata tanada kwarjini amma tana ganin nashi zai ninka nata.

"Naseera Abdallah Kwarbai, ki sani ni Mahfooz Abubakar Gwaiba bazan taɓa barinki ba. Duk runtsi duk wuya, ina tareda dake. We're a team. Inaga tun bayan dana buga ma Nigeria kwallo, ban taɓa shiga nishaɗi ba sai ranar da aka aura min ke. Kuma nayi alwashin I'll forever protect you,"

Murmushi tayi kaɗan, hawayen har yanzu suna fita amma ba da gudu ba. Zatayi magana kenan sai Nenne ta kirata dole ta fita ta barshi mashi ɗakin.

Ɗakin Charo taje domin ta riƙe babyn, ita kuma Charo zata zagaya kewaye. Anan Naseera ta sake kallon yaron soyayyar sa yana shiga birnin ranta. Itama babu haufi tanaso ta mallake nata yaran na kanta. Sai maganar Mahfooz ya rinka mata ruri cikin kunnen, kawar da tunanin take kokarin yi amma yayi kanekane cikin zuciyar ta.

Idan Mahfooz yace yaji ya gani meyasa take gudun sa? Balle idan tana shan ARV ɗinta bazai taɓa kamawa ba, itama zatayi rayuwa mai kyau kuma zata haihu. Tabbas Ummanta zataji daɗi idan ta ɗauki kaddaran ta tareda mancewa da komai.

Ta ƙofa ta kalle inda take kyautata zaton zata ga Mahfooz, anan ta gansa zaune akan tabarma suna hira da Bamanga. Murmushi ta tsinta kanta tanayi, da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tsoron kada wani ya ganta. Bata ji daɗin data lura da cewa kallon Mahfooz ne ya sakata nishaɗi.

DIYAR DR ABDALLAH Kde žijí příběhy. Začni objevovat