Cikin kuka ta ce "dan Allah Umma kar ki boyen komai ni kai na na fara zargin wani abu duk da har ga Allah bana zargin kanwata da cin amanata haka mijina, ina so ki gaya mun gaskiya dan girman Allah Umma da gaske Maryam ciki nai da ita wa yai mata dan wallahi ko kofar gida bata fita sai da ni."

Umma tazo ta rungumeta ta fashe da kuka "tabbas Nafeesat sai hakuri dan Maryam da Arfan sunci amanarki sun zalunce ki sun munafinceki sun cutar da ke, sun hadu sun zaluncemu gaba daya Maryam dai ciki nai da ita kuma mijinki shi yai mata wannan ba abun boye-boye ba ne dan shi dan duma nai zai bayyana."

Wani numfashi ta din ga fitarwa da kyar  tana nishi da sauri Umma ta mike, "wayyo Allah! zoki duban ita Mama" gaba daya sun gigice cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ta ke kiran Maryam.

Kafin ta karaso numfashin ta ya tsaya cak da gudu Maryam ta kwalla kara tai office din Doctor, wanda suka taho da sauri dauke ta su kai daga dakin suka sanja mata wani dakin nan ka shi ga kokarin ceto rayuwarta.

Abba ko da ya farka ya ga ba Umma ba almunta abun ya bata masa rai sosai tun yanzu ke nan iyalinsa sun fara juya masa baya saboda yarsa tayi cikin shege suna ganin laifinsa nai, to gaba kuma mai zai faru.

Daddy nai ya din ga kwantar masa sa hankali sosai sannan yasa ya kira masa sulaiman babban dansa, amma shi ba shi da hali shi ya sa bayayi da shi sam amma yanzu lokacinsa yazo dole ya nemeshi tun da ba shi da mai kula dashi.

Awa daya ya karaso hankalinsa a tashe ya zauna shi ya din ga jinyar mahaifin nasa shi da Abba, dan Momy tana wajen dan ta da har yau idan ya fara allura ake masa ta bacci ya koma saboda ba abun da ke bakin sai Maryam.

Satinsu biyu a asibitin Abba jiki ya warware matan ba wadda ta kara tako kafarta dubasu, dan suna cikin tashin hankali domin Nafeesat jiki yaki numfashi ma sai da oxygen Sulaiman ke kula da shi.

Kullum Daddy sai ya je yaga su Nafeesat dan hankalinta ba karamin tashin yai ba yadda yaga gaba daya na'ura ke sarrafata, har kuka sai da yai duk da zuwa yanzu hankalinsa ya fara tashi akan rashin lafiyar Arfan amma sam yaki nunawa.

Jikin Abba yai sauki yau aka sallameshi suka koma gida tun da ya shi ga gidan yake jin sam ba dadi, amma ya dake dan jikin nasa sai godiya dan yaso ya tabu maganarsa ma hardewa ta ke abun duniya ya ishe shi.

Arfan watan sa biyu a asibiti aka sallame shi suka koma gida amma bai normal ba su suka bukaci hakan, ya rame yai baki idan ba kyakykyawan sani kai masa ba bazaka taba tunanin cewa shi ba ne, dawowarsu gida ya tunkari mahaifinsa da maganar auren da ya ke so a daura masa da Maryam.

Wani mari Abba ya zabga masa wanda sai da yaga taurari "ashe baka da hankali Arfan? har yanzu baka san annabi ya faku ba, duk wannan wahalar da ka sha bata zame maka aya ba, ko kasan abun kunyar da ka jaza mana kayiwa Maryam ciki."

"Alhamdulillah ya Allah! Allah nagodema ba abun da zai hanani auren Maryam a yanzu tun da tana dauke da cikina, naji dadi Abba" wani kallo yai masa "baka da hankali Arfan ka manta kana auren yayarta?" shi fa yama manta sai yanzu ya tuna "kuma ina so ka sani an riga anwa Maryam miji ko da baka auren yayarta ba kai ba ita kaji da lalurar da ke damunka."

Cikin tashin hankali ya mike "tabbas na yarda Abba da gaske kai ma san Maryam kake, to wallahi bazan taba hakura na bar maka ita ba  dai mu zuba ni da kai mai rabo ka samu, amma wallahi Maryam tawa ce ni kadai" sai kuma ya fara tari ya durkushe a wajen.




*******************



Sai ga Zubaida da dankareriyar sarkar gwal da bangles da komai ta kawo mata  "gata nasan nayi kuskure ki yafemun kin san lefan da yawa ba'a ganewa, wallahi ban san zaki ganeba, kuma bani kadai bace Kulu ma ta dauki sarkar diamond, sai atamfofi da muka dauka da lesuna ni dai shi ka dai nasan na dauka."

Cikin kuka Haule ta ce "ba wannan ya kawoni ba Malam Mato, Zubaida ita tai wa amaryarka asiri har yanzu ta ke ta bari, ita tai mata asiri ta ke zub da mugunyar ruwa, ita tai mata asiri kake jin ta na wari da hamami, kuma ita ta tunzura ni na aikata abun da na aikata a auren Malam da Indo har Malam ya sakeni ba wanda ya sani.

Ita ta aikeni nayo masa sata ana hidimar bikin nan dan kar yaiwa Maimuna kayan daki, shi nai ya kamani yai mun saki daya amma ba wanda ya sani.

Malam Mato Zubaida ita ce ta fara kai ni wajen Malam ita ta zugani na hana yata auren kowa sai mai kudi, ita ta zugani na lalata tarbiyyar yata ita ta bata tawa tarbiyyar har na bata yata ta" rushe da kuka.

Daga Malam Mato har amaryarsa an rasa mai magana dan gaba daya sun yi suman zaune suna mamaki! Zubaida ko duk ta tsure ta takure sai soshe-soshe ta ke kamar mai karzuwa tana hararar Haule tana kifta mata ido.

"Malam Zubaida ta sa na sai da komai nawa na dakina na bata kudin da zummar za'a dawo da hankalin Malam kai na ya mai dani dakina, da yadda yata zata samu zaman lafiya da mijinta ashe Malam kasheni taje ta ce ayi.

Mallakeni ta kai kudin akai mata ta din ga karbar kudi a hannuna sai da tasa na kadar da komai nawa, wallahi Zubaida kin zalunceni wallahi Allah ba zai barki ba sai yai mana hisabi, kin ci amanar kawance da aminta ashe kawancen yanzu ya zama masifa? Ashe kawa neman ganin bayan kawarta ta ke a wannan duniyar?"

Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! Abun da Malam Mato ya furta kenan "tabbas Haule kin yi ganganci, gaba dayanku kun yi laifi mai girma amma ke nafi tausayawa kuma ki godewa Allah da ya ganar da ke gaskiya.

Kuma tabbas abun da ka shuka shi zaka girba a duniya Zubaida kin cuci kan ki kin zalunci kan ki, kin zalunci mutane da dama musamman wayanda suka amince miki, so uku kina sawa ana sakin mata a dakin su amma ban taba yarda ba sai yanzu, hasali har kanwarki kin kashewa aure saboda san zuciyarki amma muka gaza yarda.

Ba abun da zance da ke sai kije dan kan ki duniya ce tafi bagaruwa jima wanda baizo bama jiransa ta ke, ke kuma Haule ai kin ga izina kin ga sharrin kawaye ko? kin ga illar yadda da kawaye ko? ko yanzu kin ga izina saboda haka sai ki kiyaye, kije kita istighfari  ki nemi yafiyar Malam sai Allah ya sassauta miki.

Ke kuma yau zaki girbi abun da kika shuka, tuni ta fara kuka tana 'dan girman Allah Malam kayi hakuri wallahi na tuba wallahi bani kadai ba ce nake wannan aikin, wallahi nima zugar kawaye ce suka dorani a wannan hanyar amma na tuba ba zan kuma ba."

Tun da kwayene sai ki koma gidan su ku zauna da su da saboda haka kije na sake ki saki uku dan bana fatan na bude idona naganki, kuma kwayar gero ban yarda ki dauka ba a gidan nan sai Haule tayi lissafin kayan ta an biyata masu binki ba shi a biyasu ragowar a baki kayanki.

Wani ihu ta zunduma na bakin ciki tai kan Haule da bugu, da gudu Amarya ta tare ta dan itama dama da nata haushin nan ta sauke fushin ta akan ta.

*To fans muje zuwa, ni ce taku a kullum a koda yaushe.*



         *Feedyn Bash*



Pls
Share
Comment
Vote

*My phone number 08106795647*

DAN ISKAN NAMIJIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt