Ta cikin duhun da dare yayi da hasken da fitilun motoci masu wucewa ya samar, ta kurawa jaririyar idanu wani abu yana mata yawo a cikin kirjinta.
Hawaye suka fara mata zarya a kumatu.
Shin me 'yar karamar halitta irin wannan jaririyar tayi? Meye laifinta? Wani laifi ta aikata da za'a banzatar da rayuwarta a tsakiyar tasha? Wace uwa ce zata iya aikata irin wannan abu?!.

*

Sai karfe tara da rabi na dare suka isa Daura. Ta samu acaba ta loda mishi kayan tsarabarsu, suka kara tarar wani suka hau zuwa gidan aurenta.
Mamaki ya kamata ganin yadda aka fente ilahirin kofar gidan da fenti ruwan zuma mai haske, sabanin ruwan madara data bari. Ko dalilin da yasa Amadu yake ta ta kara kwanaki ne?.

Sai kawai ta dira daga kan acabar, ta sallamesu su duka. Yaran unguwa da suke ta wasanni suka mata caa suna mata sannu da zuwa. Da yake a lokacin, kaf yaran unguwar kusan kowa dan dakinta ne. Duk wanda ya jajubo wata matsala tashi ya nemi 'Mama Halima', kamar yadda suka sanya mata sunan.

Ta kara tamke goyon jaririyar data saba a bayanta, ta rungume Iman dake barci akan kafadarta. Hannun Abbas yana cikin nata ta sanya kafa ta shiga cikin gidan, yaran kuma suka bita da kayanta.

Tsakar gida tarwai, an shafe ko'ina da sumunti, an fente kowane lungu da sako.  Taja tayi tunga, sakamakon ganin halittu biyu zaune rashe-rashe akan shimfida a tsakar gidan, masu sunan mijinta Amadu da Ummah. Wata shedaniyar yarinya da tana a shekarun da basu wuce sha shida ba, ta mata sallama a kofar daki tana amaryarta lokacin, ta mata zagin kare dangi ita da abokiyarta Hauwa, suka kuma gargadeta da cewa duk daren dadewa, sai ta shigo gidanta, hakkinta, ta kuma yi waje da ita.

Hakan bai dameta ko ya d'ad'ata da kasa ba a wancan lokacin, yanzun ma babu abinda ya dameta din. Haushi daya taji a cikin ranta, na yadda Amadu bai bata girman daya dace ya bata ba, wannan ai cin mutunci ne kawai da cin fuska. Ace ya rasa lokacin da zai karo aure sai daya kasance bata gari sannan? Kodayake, da walakin... wai goro a miya. Dama can yasan abinda ya shuka, shi yasa ta dameta da ta tafi-ta tafi.

Sai da suka ji hayaniyar yara a kansu sannan suka ankara dasu. Amadu yayi wani tsalle ya mike tsaye kamar makaryacin da aka kama ya nannaga karya, to meye ma bambancin? Ya hau kame-kame da soshe-soshen wuya da keya.
Bata ko kula shi, ta juya tana wa yaran godiya, suka tafi. Ta dauko makulli ta bude daki, ta loda kayansu a ciki. Bata ko tsaya cire gyale ba, ta sake ciccibar Iman ta kulle dakinta.

Amadu yana tsaye a kofar dakinta har lokacin ya kasa iya furta wata kalma mai ma'ana. Sai da yaga tana kara kulle dakin sannan bakinshi ya samu, ya fara tambayarta ina zata je? Bata ce mishi uffan ba, ta kara jan hannun Abbas suka fita. Ya bita har kofar gida yana tambaya da magiya, tayi banza dashi. Da dai yaga ba saurararshi zata yi ba, sai ya garzaya ya koma wajen amarya da itama tayi fum! ta hau kamar fulawa. Akan me zai kulata ita kuma ya shareta kamar wata sakara? Nan fa ya hau ban hakuri da lallashi.

Rabi kawai sai ganin Halima tayi da yara, har ta rufe gida Halimar ta buga mata. Ta hau salati tana tafa hannuwa tana tambayarta lafiya? Sai kawai ta fashe mata da kuka. A ganinta hakan ba karamin zubar da mutunci da kima bane, ba kuma karamin ci baya bane, mijin aurenka ya nuna maka bacin ranka a banza yake a wajenshi. Bai damu da damuwar da zaka shiga ba, bai kuma taba damuwa da hakan ba.

Rabi dama tasan za'a rina hakan. Ta ja ta cikin gida ta zaunar da ita a daki tana lallashinta. Yara kam suna ganin gado suka haye suka hau barci. Sai data nutsu, sannan Rabin ta hau yi mata nasiha da ban baki, cewar duk abinda Allah Ya kaddarawa mutum dole sai ya faru dashi, kuma auren Amadu din Allah ne Ya kaddara za ayi. Ita ba ma don Amadu take yin kukan ba a lokacin, saboda jaririyar dake bayanta ne.

Rabi na cikin magana ta katse ganin Halimar na kokarin sunto abu daga bayanta, ita tsakaninta da Allah hankalinta bai kai kanta ba.
Ta rafka salati mai karfi, tace "a ina kika samo d'a ke kuma!".

WANI GIDA...!Where stories live. Discover now