MATAR DATTIJO page 47

Start bij het begin
                                    

A fusace ta dube shi, kai saurara ba wa'azi na kiraka kayi min ba idan xaka bani shawarar yadda xan samu mafita, na sanu damar barar da cikin yarinyar nan,kuma na koreta a gidan nan shi ne abinda nafi bukata, amma bana bukatar kasa ni a gaba ka rika yi min maganar banxa.

Kansa a kasa ya fara yi mata magana, subhanallah dan Allah ki tsaya ki saurare ni mama, ki daina furta wadannan maganganun, duk abin nan da kike tunani ba shi xai xama mafita a gare mu ba, kuma wannan ba shi xai sa dady ya rabu da matarsa ba tunda don yana sonta ya aureta.

Abinda xamu duba mama gaskiya duk wani gyara daga wajen ki yake kece kika bada kofar faruwar duk abinda yake faruwa a yanxu, mama ke da dady kun wuce a ce ana jin kanku kuna fada, amma har yanxu dady bai wuce xagi a wajenki ba, ba ki daina fada masa duk abinda kika ga dama ba,kinga wannan matsalar dole ta tsayawa dady a rai har yayi tunanin kara aure, sannan yarinyar nan da aka auro bata xo miki da fitina ba,ina ji Aunty take kiran ki sannan duk ladabin da ya kamata tana yi miki, bai kamata a ce kin nuna bakya sonta ba, sannan har ki rika fitowa fili kina cewa xaki xubar da cikin da ke jikinta a ganina duk wannan bai kamata ba, matsalar da dady ke fuskanta ne ma yasa ya bar gidan nan ya tafi da matarsa tunda yaji irin abinda kike fada, gaskiya ki gyara mama ki nemi gafararsa tunda kinga aljannarki a karkashinsa take,har fitar nan da kike yi ba da ixninsa ba duk ki nemi yafiyarsa ya yafe miki.

Tun jiya nake kiran number shi taki shiga, amma xan cigaba da kira insha Allah sai na yi muku sulhu.

Sai da ta gama saurarensa tsaf sannan ta watsa masa wata harara tare da daka masa tsawa.

Ban taba tsammanin kai mahaukaci bane sai yau munir, dama ashe baka kaunata duk xaluncin da ake yi min baka gani ba sai ramuwar da xan yi, to baxan ji nasihar taka ba kaje ka nemi uban naka kace ya sake ni tunda dama ba sona kake yi ba,ka fi son wannan jakar matar uban naka kaje na barka da su, kada ka kara shiga harkata ko abinci na dafa baxan sake baka ba,sai dai kaci na kaxamar matar babanka, tashi tayi ta shige daki.

Bin ta yayi yana bata hakuri, kiyi hakuri mama ban fada miki wannan maganar don ranki ya baci ba, dan Allah ki yafe min wucewa tayi ta bar shi yana mata magiya.

Daki ya koma ya rika tunanin irin wannan hali na mamansa da yadda xai yi ya shawo kan matsalar gidan su don abin ya dade yana ci masa tuwo a kwarya fargabar abinda xai biyo baya ne ya hana shi magana.

****

A bayan dattijo nake ya Goya ni da towel yana rarrashina kamar wata baby saboda gajiyar da ni da yayi a daren jiya,kuka na rika yi masa a kan ya mayar da ni wajen innah na cigaba da rayuwar da babu takura a cikinta, rarrashina yake yi yana min albishir da xai mayar da ni a lokacin, wayar dattijona aka kira  hannu yasa ya dauki wayar tare da karata a kunnen shi, gaisawa naji suna yi ashe innah ce ta kira  take tambayar lokacin dawowar mu
Cike da girmamawa ya bata amsa da mun dan yi nisa innah nan da sati biyu xamu dawo sallama suka yi ya kashe wayar.

A firgice na kalle shi, haba dattijona yanzu har sai mun yi sati biyu a nan Allah guduwa xan yi, sakko da ni yayi ya xaunar da ni a cinyarsa, jan kumatuna yayi indai kinga mun tafi daga wajen nan sai dai idan na tabbatar baba xai mayar min da ke dakina,idan ba haka ba kuma sai dai mu shekara a nan, kuka na fara yi masa ina masa magiya ya mayar da ni.

Wayar shi aka sake kira ta dade tana ringing sannan yasa hannu ya dauka, yana duba wayar yaga sunan maman munir, jifa yayi da ita gefe ya cigaba da yi min magana.

Rausayar da kai nayi ina masa magana bai kamata kayi watsi da wayar da tayi maka ba ka sani ko kiranka tayi ta roki gafararta, lumshe idanu yayi sannan ya fara min magana.

Nasan da cewa alkhairi baxai sa maryan ta kira ni ba don haka baxan dauki wayarta ba,lallaba shi nayi har ya dauka sai dai yana dauka ya ji...........

MATAR DATTIJO CompleteWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu