Dan baxata tab'a mantawa da wata rana da Mama ta tsaida ita tayi shara ta makara ba karamin duka yayi mata ba har sai da takaiga da kyar take iya d'aga hannunta,

sannan yace mata "duk ranar da tasan ta makara kada ta kara zuwa tayi zamanta," duk da shiyasace ta zauna amma intaje washegari sai yayi mata dukan fashi saboda....., 

Shiyasa ma yanxu inta makara sai dai ta tafi wajen Yayah Ahmad ya koya mata karatun...., 

Jawo wata bako tayi ta zaro wata shegiyar riga duk tayi wani fari tsabar kodewar da tayi ta saka,

sannan ta d'auki kayan ta fita tana kuka ta fara wanke wa kamar yadda Mama ta umarceta......

"yauwa Jafar Allah yayi maka albarka kayi min daidai, inajin da baka buge mata wancen shegen bakinnata ba da zagina xatayi...." 

"Dallah Mama kiyi shiru wallahi duk laifinki ne ai sai da nace miki a koreta itama daga gidan man, amma kika wani ce aa toh ai gashinan na tabbata kika cigaba da zama da ita wata rana sai tasa wuka tayankaki kowa ya huta kuma wallahi ni babu ruwana...."

"haba d'an albarka kayi hakuri komai ya kusa zuwa k'arshe kada ranka ya b'aci ka saki ranka kaji ko yaron kirki, akwai abinda nake jirane sai munbi komai a hankali ita wannan ba kamar sauran bace shiyasa....kaji ko yarona."

"Ba wani nan Mama kedai kawai kice kina santa ne, ai tunda muka iya cin nasara akan uwarta Kubrah tofa wannan yarinyar baxata gagaremu ba, kodai Mama harkin manta wacece Kubarah ne?  ita kumafa yarinyace sosai duk² bata wuce shekara 10 bafa wai kice tagagaremu gaskiya bazaiyu, yakamata ki d'auki mataki akai dani wallahi bazan zauna ina had'a inuwa d'aya da wannan yarinyar ba nima tafiyata zanyi na barki kamar yanda kanina yayi....."

dum² taji gabanta ya fadi zuciyarta ta fara bugawa da k'arfi takiyanke ta riga tuno d'anta abin santa Kabeer duk son da takeyi yiwa Jafar da Adam baikai wanda takewa Kabeer,

kuma takasa sanar dasu gaskiyar lamari  akan d'an uwansu....,

Wallahi boka ka cuceni daka rabani d'ana yanzu yazanyi idan narasa Jafar shima.

Kai wlh bazai yuba dole ki bar gidan nan Yasmeen,

koda xanyi yawo tsirara saina rabaki da gidan nan wallahi wannan alkawar na dauka....

dole gobe naje na samin jummai akan wannan maganar musan ya zamu b'ulo mata....,

Murmushi yak'e ta saki sannan tace "yanzu Jafar harkana iya tunani tafiya kabarni? haba yarona kasan bazan iya rabuwa dakai ba, amma gashi kai kana tunani rabuwa dani ko, kayi hakuri indai akan waccen shegiyar yarinyar ce nayi maka alkawarin saita bar gidan nan kusa bada jimawa ba, kuma bazata tab'a dawowa ba kaji yarona ka kwantar da hankalinka, ai kasan koh wacece Mamaka?"

Dariya yayi "yace gaskiya Mama ba bakida mutunci ko kadan nasan wannan kad'an ne daga cikin abinda zaki iya aikawata, zan baki lokaci amma fa idan kika wuce babu abinda zai hanani tafiyata......"

hhhhhh! itama dariya tayi tace "wallahi kaima Jafar ba k'aramin hatsabibi bane kai, dan kama fini had'a indai wannan ba damuwa gobe zanje gidan jummai mutattauna ta yarda xamu b'ulowa lamarin."

"hhhhhh! wokee Mama zan zauna ina mai tsumayen jin labari mai dadi..."

"Toh..! Mama nidai zan fita"

"Harka fito Adam?"

"Eh! Mama na fito..."

"Toh..! Shikenan saika dawo, amma fa kada ka manta yau duk inda zaka nemo min kud'i ka nemo ka kawo min kaji koh"

Hhhhhhh! "kefa Mama maiyar kud'i ce wato ma duk duk inda xa'a nemo miki kud'i a nemo akawo miki koh tom kada ki damu...., koh kin manta wanene danki koh? Baki san waye Adam ba kenan?"

"Kajini da ja'iri taya zan manta suwaye yarana,  bacin na san Allah ya azurtani da jaruman yara masu nemo nakansu koh ta halin yaya, taya zan manta?"

Hhhhhh! Dariya sukayi tare da tabawa sannan Adam yace "Shiyasa muke sanki Mama ke kadaice kike yaba halinmu, kaf fadin gari nan zagin mu akeyi wai bama da tarbiya"

Jafar ne ya cabe da cewa "ai bama kisan wani abuba Mama, wai naje wajen wata yarinya babanta yace kada na kara zuwa k'ofar gidansa,  wai shi baya gayyar marassa tarbiya gidansa, na kuma komawa washegari daya fito ya gani ya daukeni da mari sannan ya koreni, aikoh ranan yayi hanyar yamma dama kinsan babu mutane a tawajen, nida abokaina muka tare masa hanya mukayi mushi dukan tsiya muka barshi nan a yashe mukayi tafiyarmu abinmu, yanxu haka yana can kwance sai jinya yake ko k'ofar gidannasa dayake tak'ama dashi baya iya zuwa. "

"Allah yayi maka albarka Jafar,  kayi min daidai wallahi ina goyan bayanku duk shegen da ya taka ku kuma ku takasa, kunji ni koh?"

"Eh! Munji"

"Yauwa yaran kirki, ai saika wuce ka tafi bance ka ragama kowa ba, kajini koh?"

"Uhmm naji"

Hanyar waje yayi zai fita yana zuwa gab da k'ofar futa yayi daidai da lokacin data kwaro ruwan da tayi wanki dasu, aiko sai akan k'afarsa sannan ya fallatsar masa akan k'afar wandonsa harya jik'a masa....

A fusace yayi kanta ya d'auke ta da kakkauran mari,  ta tafi zata fadi ya damk'ota  ya had'ata kanta da bango sannan ya damk'i yalwataccen gashin kanata....

_See me next page✍🏻_

*Vote*
*Like*
*Comment*
_*#Realtakowa*_️

YASMEEN.Where stories live. Discover now