1

9.9K 187 32
                                    






PORTUGAL 🇵🇹

..... Ita ce mutum ta uku cikin jerin masu fitowa daga cikin jirgin, kallo d'aya xaka mata ka karanci tashin hankali dake tattare da fuskarta, sam babu fara'a ko murmushi a tare da ita, sai idanun ta dake nuna alamar tasha kuka sosai, tana rungume da jaririnta kyam kamar wani xai kwace mata shi, d'ayan hannun ta yana Jaye da trolly d'in ta.

Doguwar rigar atampha ce a jikinta, sai qaramin gyale da ta rufe gashin kanta da shi, kana kallon ta xaka san hutu da wayewa suna aiki a tattare da ita, kyakkyawa ce matuqa, ga tsayi ga kuma diri da Allah yayi mata baiwa dashi.

A hankali ta cigaba da saukowa daga matattakalar jirgin cikin qasaita, tana gama saukowa ta zuge trolly d'in ta shiga janta da qasa tana tafiya cikin nutsuwa batare da ta kula da kowa ba.

Patrick ta hango ya nufo wanda dama tuni ta dad'e da sanar dashi xuwan ta, shi ke kula da gidan mahaifin ta dake qasar, ya fad'ad'a murmushin sa bayan ya karbi jakar hannun ta yana gaidata, fuska babu walwala ta amsa mashi tayi gaba abunta.

Suna isowa mota ya bud'e mata da sauri, ta shiga motar ya rufe kafin ya saka kayan a booth cike da tunani iri iri,

Afiya bata taba xuwa qasar da irin wannan damuwar daya gani a tare da ita ba, bama wannan ba baby dake hannun ta na waye a ina ta samu kuma menene dalilin ta na xuwa qasar batare da mahaifinta ba bayan ya san duk lokacin da xata xo tare suke xuwa.

Ta sauke glass d'in motar tana kallon sa fuska a d'aure,

what are you waiting for?jiki na rawa ya xagaya motar ya shiga yana fad'in sorry ma.

Ba wata doguwar tafiya suka yi ba, suna isowa bata jira an bud'e mata motar ba ta fito, Suzana ma'aikaciyar gidan tana ganin ta taxo da sauri ta rungume ta har jaririn dake hannun ta cikin tsantsan farin cikin ganin ta a yau.

Banda murmushi da Afiya ke yi na dole ba komai d'auke a fuskarta, yanayin ta ya saka suzana tsaida idanu akansa wanda sai a lokacin ta ankarar da baby dake hannun ta.

Wow madam, you mean your baby?

Batare da Afiya tayi magana ba ta miqa mata yaron kana ta nufi d'akin ta tana share wasu kwalla.

Baturiyar ta bi Afiya da kallo kafin ta maido da hankalin ta kan baby dake hannunta. 

*

Busan sarewa da kid'an jauje sune suka cika gidan mai martaba sarki mera, kasancewar kowa yana cike da farin cikin xuwan jikan nasa wanda a gobe ne ake rad'a masa suna.

Daga ciki kuwa xukata ne suka yi xafi daga bacin rai da suke ciki, a fusace aiman ya tashi ya bar falon xuciyarsa na tafarfasa, tafiya yake yana xare alkyabbar jikin sa, anan farfajiyar gidan yayi jefar da ita ya nufi sashen sa cikin hanxari.

Nabila na qoqarin tashi tabar falon, sarki ya dakatar da ita da hannu, jiki na rawa take kallon sa saboda tsananin tsoron sa.

Yace ki fad'amin gaskiya akwai cikin Aiman d'ana a jikinki.

Cikin tabbatarwa ta gyad'a kanta tana goge wasu hawaye da suka xo mata, Aliyu da rumaisah suka rufe idanun su cikin takaici da baqin ciki, Umma kuwa tamkar ta rusa ihu a gurin saboda toxarcin da yau ake wa d'anta sam bata yarda da xancen nabila ba, tasan d'anta tasan abinda xai iya aikatawa da akasarin sa.

Sarki ya dubi wambai yana fad'in, a rufe ta tare da bata kulawa har xuwa lokacin da xata haife abinda ke cikin ta.

Hankalin nabila ya tashi matuqa dan ba haka taso taji ba, ta fashe da kuka mai tsanani, tsawa wambai ya daka mata wadda yasa ta nutsuwa ba shiri, nuni yayi mata da hanyar waje jiki na rawa ta tashi ta fice yabi bayanta.

MULKI KO SARAUTA 2 Where stories live. Discover now