Ghania

246 13 0
                                        

                                       Page 1 to 100

GODIYA
Ga Allah subahanahu wata'ala. tsira da Amincin Allah su sake tabbata ga Annabi Muhammady (saw).

SAUDAUKARWA

GA MAHAIFIYA TA HAJIYA LAMI SHEHU da mahaifi na Dr shehu Abdul da kuma mijina Mahmud A.

GODIYA,JINJINA
GA masoyana na nesa da na kusa, duk Ina jinjina masu Allah ya bar zumuci Amin.
*************************************************

Baki da aiki yi sai barci da anyi magana Sai ki wani juya fuska don munafurci yau ko kina kuka jini ne Sai kin fita kin sayar da awara nan kuma karki tsake ki min kwantai don wallah yau ba mai kwatan ki dama wanan wujuwujun baba nan naki to shima ya tafi cin rani kinga daga ni sai ke in na ga dama na dama ki na sha in kuma na sake gani dama sai na karkarya ki dama ba auki ne da ke ba bare na sha wuyar kaddamarwa maza tashi ki fice min da gani
Dama Kina dauka ki fara bi ta layi da mutane suka
Fi yawa ki sayar ki dawo ki dauki abinci sayar wa na
Ranan maza je ki dauka.
Baba larai banyi sallah asuba ba fa kuma gashi yau da ciwo ciki na tashi wallahi yauwa nake ji ki taimaka ko koko ne a bani .
Ghania ni zaki sa a gaba kice Kina ciwo ciki? Aaa lalle magana sabowa ya fito wato ki sani gaba na baki koko uban ki mai ya bari a gida da zan dama koko dashi Ina hakan nan ya yi tafiyar shi in Banda dubu 3000 da ya bari nake juyawa muna sana'a shine zan dauko na baki sallah kuma tun yaushe aka yi ta Kina nan Kina barci a sara Ina zaki ji.
Tun kan rai ki ya baci ki zo ki fata min da gani.
A hankali take tafiya har tazo wani lungu ta sauke bukatin awara ta ta fitar da goran ruwan ta tayi alwala tayi sallah sanan ta dauki awara ta tayi sabo
Layi don jama'a su fi taruwa a wurin.
Tun daga nesa sangir ya hango ghania ya shiga washe baki yana taba Bilal kai !kai!! Kai!!! Gafa mu mutumiyar ka . Bilal ya murmusha yace ni a tunani na duk kauye nan yariya duk kyauta bata isa ta wulakantani ba Amma dubi ghania nan har zagi na ta sha yi don kawai na taba hannu ta Amma ba komai zanyi magani abu.
Kai tun yaushe kake ce wa zaka yi magani abu . Ni fa da Ina da dama kaman na ka yaro na dan mai gari da tuni na sa an min aure da ita muga karshe iskanci ta .kana gama shan amarci ka tsako banza.yariya da ko kirge dangi bata fara ba wani dadi zaka ji a nan inji umar? Shawara daya ce kawai ka dau nawa ka yi wuri ka sanan ma mai gari Kawai kai kana so ta kaga
Daga nan sai a maku aure inji sangir.
Busha hanci yayi yace duk naji bayane ku Amma ku sani ni Bilal bana kaunan yariya nan sai sha'awar ta Amma a hankali zan yaudare ta har ta amince min na aure ta sai daga baya nayi wasi da ita .
A take suka sa dariya har ghania ta iso ta gaida su ta wuce .
Amma fa yariyan nan akwai ladabi kana gani in ka mata haka dan mata adalci? Ni dadi na da kai uwar
Akwai imani da shishigi naga tun da muka fara zance yariya nan kake ta wasu maganganu da ban gane ba. Wallah Bilal ba haka bane haka kawai na ji yariya nan na mugu bani tautsayi ka san marainiya ce ba uwa uban kuma kullum yana kano ci rani kishiyar uwa duk tabi ta sata gaba abin ba dadi sam to dalili da yariyan ke bani tautsayi kenan.
A haka suka watse kowa yayi gaba don sana'a su
Bilal ne kadai baya sana'a Wai shi a dole dan mai gari yin sana'a a wurin shi zubar da aji ne.
Kuji fa? Taya ya yin sana'a ya zama zubar da aji sai ince Allah kyau ta .
Don Allah baba ga awara na ki sayar min duk naira goma goma ce ko wani daya bari na gudu na shiga aji don ma yau ban zo da wuri ba gashi har an kusa guga tara da gudu ghania ta boye bayan wani kato itace ta cire kayan jikin ta ta sa uniform ta fito tana ma baba sallama don kar a tare ta a kofar shiga baba cikin tautsayi ghania ta dauki goma a kudi taliya da take sayarwa ta ce yi maza ki tafi insha Allah ma ba mai duka min ke ghania ta amin baba a guje ta tafi tana daga ma baba hannu har ta shiga aji su da yake a baki makaranta suke talla ita da baba .
Damuwa duk ya cika baba yau kusan shekara uku kenan da ta San ghania ba zata manta ba kullum tana gani ghania na kawo kosai ko awara da tuwo madara kayan kwalama tana sayar wa a nan baba take tambaya ta ko ita ma tana so shiga ne don ta lura da yanda kullum hankali ta na kan yara a cikin makarata. Ghania tayi kuka sosai kafi daga baya take fadi mata ba mai sa ta da ma mamata na da rai me to ta rasu tana zama da kishiyar mama ta ce ta gaya mata duk azaba da take gana mata tautsayi sosai ya kama baba sai da aka yi kwana uku ta tambaye ghania ko tana da sha'awar shiga boko ?
Da fara'a ta tace tana so a biyo baba ta shigar da ghania primary school da malamai suka gwada ta sai suka yanke shawara sa ta a aji uku don ghania na da ilimi sosai a boye kullum ghania zata zo makarata in ta kawo awara ta sai ta ba baba ta sayar mata ita kuma ta shiga aji.
Baba Na gama tunani hawaye na fito mata tace da yardan Allah ghania zaki dawo abin alfahari da kowa hatta makiyan ki sai su so ki.
Ana buga masu tara ghania ta fito a guje ta chanza kaya zuwa kayan gida taje ta dau shinkafa ta ta ba
Baba larai kudi awara sai murna take yi tana washe baki ko ke fa yanzu yi maza ki kai shikafa nan kofar primary in kin ga dama ma ki kai dare ni buri na shine naga kudi kuma ina gani yanzu dauka da wuri don na san an buga tara.
Da wuri take tafiya don ta samu ta dawo ta ba ma baba ta samu ta wuce aji don da gidan su da makarata su a akwai nisa sosai a haka ta iso ko sayawa bayani ma baba bata yi ba ta gudu bayan itace da take chanza kaya ta sa uniform ta fito har ta fara tafiya baba ta ce zo nan ghania tun jiya nake ji Kina cewa ciwo ciki anya ba yunwa bane maza zauna ki ci taliya nan dama nazo da koko Sai ki sha haba ace mutum kaman inji baya gajiya Haba yar nan
Kashe kanki kike so yi ne?
Allah baba baza ki gane bane yunwa kam naji shi har na gaji yanzu kwatakwatw bana ma marmari abu a baki na .
A naji sha koko zai rike maki ciki , da sauri ta shanye ta shiga ciki makarata tana daga ma baba hannu.

GHANIA( pretty girl) by Mrs Mz.Histórias para pegar e não largar. Descubra agora