EPISODE 31

829 56 13
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

31

Ba kunya Adam ya kawo kayan lefe cikin gidansu akan za'akai gidansu Abida, duk abunda yake Hajiya Hassu bata masa magana iyakarta dashi in ya gaisheta ta k'ura masa ido, shikuwa ya sunkuyar dakai don har tsoron kallonta yake, haka aka nemo aunties dinshi suka kai, daga ganin rawar k'afar da Babar Abida keyi sukaji sun raina musu, dama dai yanayinsu talakawane don Abida har suyar awara tasha yi bakin layi kafin tayi Candy, bawannan ne damuwa ba illa zalamarsu da ta fito fili...

  Fuska ad'aure ya shigo ya kalleta " Khairi na rasa me kikayiwa zuriyar mu ne, kiji tsoron Allah ki gyara tsakani na da mahaifiyata, narasa karyar da kika gaya musu, don bana shakka akan dalilin ki take fushi dani" da yasan wutar tsanarsa dake ci azuciyarta da ya daina yarda suna had'uwa,ta ja wani mahaukacin tsaki ta kwanta ta bashi baya, juya bayan da tayi take wani abu ya bi jijiyoyinsa ya k'ura wa bayanta kallo, take yaji bazai iya sake magana ba ya shiga tuno soyayyar da suka zuba, yayi missing d'inta gashi bai isa ya had'a Abida da Khairi wajan diri da komiba, shiga yayi tunani da salon soyayya irin nata...

Jira take taji ya rufeta da duka tunda yanzu bata da ciki ai bazai ji tausayinta ba, amma sai taji shiru ba masifa ba duka,  juyowa tayi taga yanda ya kafe yana bin halittar ta da kallo,take taji haushi da sauri ta tashi tayi  shigewarta toilet, cikin borin kunya ya d'aga murya yace " Aikin banza meye bansaniba, kije kiji da matsalarki" koda yafita tunowa kawai yake da ita a idonsa, sai da shaidaniyar zuciyarsa ta tuno masa affairs da Dr sannan ya watsar da tunanin ta.

Labarin mutuwar auranta ya isa ga Maryam Tafida inda tazo ta sameta takanas, bayan jaje da ta mata sai asannan tacewa Khairi dama tariga tagano abubuwa na faruwa amma bata tab'a tunanin abun zai kai hakaba, sun jima suna hira inda Maryam ta nuna mata taja mutumcinta in yadawo 'kome', don tabbas yana sonta sosai amma kar tayi tunanin rabuwa dashi, murmushi Khairi tayi ta ce mata ita yanzu ba d'igon soyayyar Adam aranta don haka babinta dashi ya riga ya k'are, ita kuwa Maryam tace in kika huce zaki son soyayya d'ayace kuma kin damk'ata ga Adam...

Tuni Khairi jini ya tsaya mata hakan yana nufin tagama iddarta, tana iya aure koda kuwa aranar ne

  Koda Dr yaji gulmar an saketa kuma harda maganarsa ciki, gaba d'aya hankalinsa ne ya tashi ya nemi number d'inta, domin da bashi da ita ya k'irata yace zasu zo shida H.O.D matsayin  dubiyarta, taso hanasu amma sai tace gara suzo kila tasamu inma da wani zargin azuciyar iyayenta su wanketa...

A falon babansu Adam aka saukesu tunda har yanzu tana gidan, sun samu tarb'a mai kyau daga wajan Alhaji Abdullahi kafin shigowar Khairi saida suka nunawa Alhaji ba wata alak'a mai k'arfi tsakaninsu, asalima jarumtarta ne yasa sukan sakata acikin al'amura sosai, su anasu tunanin gidansu Khairin ne, kana ganin fuskar Dr Umar da H.O. D kasan mutane ne masu kamala don ga kwarjini nan kwance kan fuskarsu don haka ma shima Alhaji Abdullahi bai yi kokonton maganarsuba. ...

Cikin mutumtawa suka gaisa sannan suka jajanta mata, inda suka nemi yafiyarta aganinsu harda laifinsu awajan zafafawar lamarin, nuna musu tayi bakomai dama k'addarartane, da zasu tafi suka ajiye mata 50k ta nuna bazata karba, kallonta Dr yayi yace " Haba ai bawani abu bane tunda bamu zo da lemon dubiya ba" murmushi tayi ta rakasu tare da musu godiya sosai..

Daidai lokacin Adam zai shigo gidan, aikuwa cike da masifa ya nufi Dr zai cakumi wuyansa yaji muryar mahaifinsa " Karka kuskura kace zakai masa hauka, dama irin abunda kake yi kenan k? fice min agida" sai alokacin ma suka gane gidansu Adam ne, da maganarsa suka isa hanya don bak'aramin mamaki ya basu gefe d'aya ya basu tausayi daga shi har Khairin..

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now