1

130 7 0
                                        

🌺SHATU🌺 1


Kayya! Kayya!! Kayya maryama barni nayi sbd kuka na a halin danake ciki a yanxu shine zai sauqaqa min abinda nakeji a zuciyata shine zai rage min nauyin da naji zuciyata tayi  shine zai taimaka min daga yin na zuci daii ta fada tana fashewa da kuka.

Cike da tausayawa ta kara matsowa kusa da ita tana share mata hawaye tace " naji da wannan ma amma ba kowane irin kuka bane ke zamowa maslaha ko sauqi ga zukata da gangar jikin mu ba in tai yawa ma sai dai akasin ta ta afku dan haka ki daina  kukan nan ki ta addu'a in sha Allahu komai zai zo da sauqi da yardan mai duka".

Tana shessheka ta muskuta ta dora kanta a kafadar maryama kwallan suna cigaba da kwaranyowa.

Ina ma goggo habi bata dawo dani ba,ina ma Allah ya kan bar wani dan wani yaji dadin rayuwa,ina ma dan adam yana sanin abinda zai faru dashi a rayuwaa...dah tabbas sai nayi abinda zan gujewa duk wata mummunar abinda zai faru da..toshe bakin ta da maryama tayi shi yai dalilin data hadiye sauran harufan.

Sharrin da aka laqaba miki in shi bai sa kin saki layi ba toh babu tantanma sabon Allahn da kike shirin tafkawa zai sa ki saki layi wlhy ta fada cike da zafi zafi,kuma naga alama ba kadai bappah bane ke buqatan agajin gaggawa ba harda ke malaman jinya zan kira su sam miki gado sannan su zurkuda miki alluran bacci ko kunne na ya san salama da zantukankin nan tana mai yin kuka da dariya a lkc guda sbd samun salama a zukatan su.

Shikenan na daina. Allah ya bawa bappah lafiyaaa.

Tsayawan da likita yayi a gaban su baba waziri,hajiya babba da anty asibi yana musu magana shi ya janyo hankalin su ita da maryama suka karisa gun.

Karisawan su dai-dai likitan ya gama magana ya juya. Da harara aka tarbesu zuwan su 'ta san da harara na tabo toh tabbas ita sai an rasa gurbin da wasu zasu san guri a jikinta sai yasa a lokuta da dama take daukan shi harara a duhu.' Dama ta san ko mutuwa zatayi ta saura baza su fada mata mai likitan ya fada musu ba iyakaci a bita da karkarwan ido sai yasa kansu tsaye suka fuskanci baba waziri bayan su hajiyan sun marawa likitan baya ta hanya da suka ga ya bi.

Toh shatun bappah mai majina a share hawayen ya fada yana zolayar ta,toh muje mu dakin da aka fito dashi likita yace jikinsa alhmdlhy kawai farfadowansa zamu saurara amma in sha Allahu garau zai tashi sai dan abinda baza a rasa ba. Nan suka doru a bayansa maryama tana riqe da hannuta.

Tasan zolayar ta da baba waziri yake kawai yana so ya kawar da yanayin dake kan fuskar tane ya maye gurbin da murmushi,amma tasan da kamar wuya. Zolayar sa bazai kankare dungumemen sharrin da aka laqaba mata ba,abinda ya faru bazai sa ya dawo tarihi ba,sannan bazai hana a yanke mata hukuncin da ake wanzarwa ba, jinyan mikin dake zuciyarta da bakin fentin da aka goga mata duk ba daya da zai yassare mata. Abinda tafi tunani kila zuwa jibi iwar haka indai an sallami bappah toh ta dade da zama abincin tsutsotsi.

Da taimakon riqe hannunta da maryama tayi suka kai ga dakin da aka mayar da bappah suka shige da sallama.


maryammuhdkabir@wattpad.

#SUBHANALLAHI.....

#vote
#comment
#share
#SHATU

SHATUStories to obsess over. Discover now