"Maa ki kalla Babyn mu ta fiki kyau"wata muguwar Harara ta banka mata tace

"Kaii wannan yarinyar wata rana sai na yanke maki baki akan wannan shegen maganar taki,toh waye ke son wani kyau,kyan ɗan maciji wuce ki bani wuri".

Hannu ta miƙa ta amshi yarinyar,"Na shiga uku na mutu ni Mahfuza wannan yarinyar sai kace ƴar Aljanu?"



"Auzu billahi Minash-shaiɗan,ke wacce irin mace ce nikam?"

Bata san maganar ta ta fito fili ba,tsabar kiɗime war da tayi,tace


"Ahmm....ahhhm Masha Allah"gaba ɗaya kunya ta rufe ta.


Aunty Momy tace"Ke kika sani,kaii Mahfuz ka.."bata gama rufe baki ba,su Maman Yara suka yi sallama a ɗakin,,suna shigo wa kuma Du'a ta motsa hannun ta,da sauri Aunty Momy taje gare ta,bakin ta taga yana motsi alamun magana.

Kara kunnen ta tayi don son jin me take faɗi"Wayyo zai kashe ni,Baba mutuwa zanyi,wallah kashe ni zai yi ku taimaka min.wayyo Maman Yara wayyo zan mutu"sai juya kanta take Ga kuma hawaye dake bin gefen fuskar ta,Aunty Momy gaba ɗaya ta tsora taTo meke nan hakan yake nufi?,Ganin babu amsar tambayar ta yasa ta juya  suka shiga gaisawa da su Maman  Yara.



"Ya masu jegon?"Maman Yara ta tambaya.

"Alhmdulillah"Aunty Momy Ta bata amsa.

Ita kuwa Mama tana riƙe da Babyn,sak lokacin da Du'a tana jaririya.Maman yara tace

"Toh Masha Allah,naga bacci take"

"Eh wallah,ai tun da aka fito da ita bata tashi ba,ƙilan ko sai anjima"

"Ayya toh Allah tashe ta lafiya"gaba ɗaya suka amsa da Amin.

Karɓar Babyn Maman Yara tayi tace"Masha Allah,yarinya sak Du'a lokacin tana yarinya"

"Allah?anya kuwa Wannan bata fi Maimunatu kyau ba?"Inji Aunty Momy.


Dariya Mama tayi ita Sai dai daria duk kunya take ji,wai yau ita ce da jika.

Haka suka yi ta hira,sai kusa ƙarfe biyu na rana suka ce zasu wuce Maman Yara tace"Me muka samu ne".

Aunty Momy tace"Ai ina ƙoƙarin tambayar shi kinan kuka shigo,gashi kuma har zaku wuce bata tashi ba,nasan zata so ganin ku kuwa".

Murmushi Maman Yara tayi tace"Ayya toh idan an fitar da sunan a faɗi mana,zamu dawo insha Allah ko zuwa gobe".

"Toh madalla,Allah ya kaimu,ku tambaye shi idan kun fita nasan yana nan".

"Ahh ba'ayi haka ba,ai ba sauri ake ba,nima abinda yasa na tambaya nayi tunanin ko an fitar mata da suna ne"


Ta juya ga Mama tace"Maman Du'a kinyi shiru baki cewa komi,ina su Aliyu ne har zamu tafi basu shigo ba".

"Ai kinsan halin su da kunya,bari nayi masu magana su zo ku gaisa".

"Laa barsu ai yanzu Samari haka suke".inji Aunty Momy.

"Toh ai shikinan,mungode Allah ya saka da alkhairi Allah ya bar zumunci".

"Laa babu komi ai mun riga mun zama ɗaya ni ce da godiya".

Fita suka yi,domin taka masu,suna fita kuwa sai ga Baban Mahfuz yana iso wa suka gaisa Gaba ɗayan su duka gaidashi ya miƙa masu hannu suka yi musaba,cike da girmawa.

Ya Aliyu yace"Ama mu bamu ga Babyn ba".

"Baku so gani ba,da kun shiga kun gani wai ku manya,kwa dawo daga baya tunda yanzu kunga tafiya zamuyi ko"Cewar Maman Yara.



KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now