LAMBA TA BIYAR

632 39 1
                                    

*KISHIYA*









®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼





*NA*




*UMMU NABIL*






*_Aysha Aliyu ta gaban goshin Ummu Nabil,ga page naki nan na baki yau abin naki ne ina matuk'ar jin dad'in comment naki,Our queen of comment😍😘_*





*NO.19*





Tun bayan da sukayi sallar Asuba suka tashi,suka koma bacci basu tashi ba,sai misalin k'arfe tara da rabi,kafin su fito sai da suka yi wanka abinsu tsaf dasu suka fito,dinning suka nufa wayam babu komi,tsamanin su Mahfuza tayi masu abincin da suka karya dashi ama shiru,kallon Du'a yayi ita ma kallon shi tayi,ya bud'e baki zaiyi magana kinan sai gata ta fito,da wata er fingilar riga,hamma tayi sannan tace



"Kun fito kinan wallah kuwa kamar kasan yunwa nake ji,sosai jiya dama banci komi ba na kwanta"ta kalli inda Du'a take tace



"Amarya ya kika tashi,baki kawo mana abincin namu ba,ohhh na manta bai shaida maki idan anyi girki anan ake ajiye wa ba,kije ki kawo mana"


"Ai bata fara girki ba,ko kin manta jiya aka kawo ta,ke tsabar rashin mutun ci kina nufin baki yi abinci ba,ko kuwa ke ranar da aka kawo ki washe gari kinyi girki,ina ce daga gidan mu aka kawo maki,saboda yanzu ansan ku biyu ne,ansan ke zaki yi mi yasa kika je,kika zauna baki yi ba,wallah Mahfuza ki shiga hankalin ki,na fad'a maki banson shashanci,idan baki cikin hankalin ki,toh ki dawo hayyacin ki"Kallon shi tayi tsaf sama da k'asa tace




"Kaga don Allah karka d'ora min ciwo,daga tashi na,yoh ina na samu nayi sallah ma,kaga nifa ko tashi banyi ba,kuma saboda wulak'anci ko kazo ma ka tashe ni,kuma yunwa ce ma ta tashi ni"kallon Du'a yayi yace


"Wuce ciki barin samo maki abinda zaki ci ko"daka tar dashi tayi tare dayin murmushi tace

"A'a barin sa akawo mana a gida dama su Halimatu zasu zo,k'ilan ma suna kan hanya,karka damu"kama hannun shi tayi suka bar Mahfuza tsaye da sakin baki da kallon hanyar da suka bi.



"Iyyye lallai yarinya kin taro dai-dai dake dani kike zancen mijin nawa zaki wani ja hannun shi,ina tsaye ki barni da kallon hanya"



Kowa ma tayi d'aki tayi………



_Kuyi hkri bana samun isasshen comment shisa ga wannan a haka a haka dai zamu ida nufi insha Allah_



Comment N Share

*UMMU NABIL*

KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now