Kallon shi Du'a tayi tace"Haba mana mai yasa kayi hak.."bata k'arasa ba,ya daka tar da ita ta hanyar cewa


"Ci abinci kinji"bata kuma ce mashi komi ba,ta saka hannu suka fara cin abincin duk da rabi shi yaci saboda gaba d'aya bata jin dad'in bakin ta ji take kamar wadda ta tashi daga ciwo.....





Haka yinin Ranar ta kasancewa Du'a a gidan miji wanda ko a mafarki bata tunani,ji take a jikin ta,wani kala daban,duk da da k'awayen ta suka yini a gidan sai daf da magriba suka bar gidan.






Bayan tafiyar su Halima kuwa,wanka tayi tayi sallah ta gyara jikin ta,bata fito ba,a d'akin ta ta zauna saboda darasin da Maman Yara tayi mata ciki harda shi.

Misalin Bakwai da Rabi Mahfuz ya shigo a bakin gado ya tarar da ita tana ganin shi ta tashi tsaye ita bata je gare shi ita bata zauna ba,bud'e mata hannun sa yayi,ta nok'e kafad'a tayi yayi murmushi ya iso har inda take yace



"Rowa ko"dariya tayi ta sunkuyar da kanta k'asa...


Turo k'ofa tayi ta shigo.......






Comment N Share




*UMMU NABIL*
*KISHIYA*

















®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼











*NA*








*UMMU NABIL*









*NO.21*







Yana matsowa kusa da ita,zaiyi magana dai-dai lokacin da Mahfuza tashigo,kawai yaji ta haɗe bakin su wuri guda,mamaki ne ya sashi kasa aikata komi,saboda bai taɓa tunanin zata iya yin haka ba.

Ita kam Mahfuza tsayawa tayi tana kallon ƴar yarinya da iya kissa,kuma tasan don ta ganta,jiyo muryar ta tayi tace





"Ohh,muje kayi wanka nasan ka gaji dewa ko?"ta faɗa cikin wata irin kasalalliyar murya,wanda tasa zuciyar Mahfuz bugawa da sauri da sauri,cire mashi kaya ta fara yana ɗan taya ta har ya cire suka shige toilet suka bar Mahfuza tsaye da bin hanya da kallo.






Kuka ta fashe dashi,ta fita a ɗakin saboda mugun takaicin da ta ƙunsa.

Bayan ya shirya fita suka yi dama ta riga tayi girki, dining suka isa,Mahfuz ya kalli Du'a yana murmushi yace


"Farin cikin Mahfuz,kinsan mi?"ita ma murmushi ta mayar mashi saboda taji matuƙar daɗin sunan daya kirata Dashi Tace




"Ina jinka"

"Ina son ki"murmushi tayi ita ma tace"Nima ina sonka"

"Toh nagode,yanzu sauke mana abinci ƙasa,banson cin abin ci a sama kuma bana ci da cokali kinsan saboda mi?"ya tambaye ta.




"A'a sai ka faɗa"ita ma ta bashi amsa.


"Saboda al'adar ya hudu ce,cin abinci da cokali,shi kuma ci da cokali manzon Allah(S.A.W) yace,sai dai idan mutum yana da larurar kuturta,ko dai wani ciwo wanda bazai iya ci da yatsun sa ba shine zaici da wani nau'i na cokali,kema daga yau inason ki daina kinji"




"Aikuwa cin abinci da cokali yafi daɗi,kasan idan da hannu ne zubewa yake"ƴar dariya yayi yace

"Ai duk wani abu da Allah da Manzon sa,suka ce a bari toh idan kika bibiya yafi daɗi saboda shaiɗan yana taya ka aiwa tar da abin"




KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now