Tun da suka shiga gidan take kallon gidan auren ta kamar an chanza mata shi dan kuwa har lokacin brain ɗin ta ba wai gama dawowa normal yayi ba still effect ɗin antidepressant ɗin da aka ta banka mata bai bar ta ba tana ɗan ganin dishi dishi dan haka tallafo ta yayi har suka ida shiga gidan a hankali suka rinƙa takawa har suka iso falon inda ganin jama'an ya saka ta jin wani irin wahaltacen ciwon kai kowa tashi tsaye yayi yana al'ajabi da gudu salma ta karasa ta kai mata runguma at the same time ta sake kuka sai yi take yi dan ta san definitely zata tambaye ta about falmata me zata ce mata?aminiyar ki da kika damu da ita ita ce tayi sanadiyar ɓacewar ta har aka kai ta wani uwa duniya sai kuka sharrrr daga bisani ɗagowa ta yi ta fara magana

"Salma ki daina kuka ai ga ni na dawo gida komai ya tafi it's now all in past ki daina kuka kin ji"?? Ai ko kamar daɗa tunzira ta ta yi sai wani kukan ya ɓalle mata ta shiga yi dan tausayi da ƙaunar Aishan da ya shige ta fiye da da she is too gentile and kind bata chanchanci a mata haka ba falmata of all people amma me ya sa ta yi wannan ɗanyen aiki toh ko dai saka ta yi aka yi ne bata  faɗa ba?? kan ta ya kasa booting dan har ta fara birkicewa dan haka mijin ta na ganin haka ya san me ke ran ta sai yayi saurin janyo ta yana rarrashin ta

"Salma ina falmata tun da na shigo ban gan ta ba"!!! Tsit falon ya ɗauka dan kuwa an rasa me courage ɗin sanar da ita inda falmata take in ma an sanar da ita ɗin me za'a ce mata yayi sanadiyar kai ta inda take?again duba da halin da take ciki na rashin gama farfaɗewar ta ba za'a so ta kuma shiga wani hali ba shi yasa aka mata shiru ita kuma salma ta kasa daina kukan dan ita kadai ta san raɗaɗi da ciwon da ke damin ta a zuciyar ta ace childhood friend ɗin ka ya maka wannan abin how on earth hankali zai ɗau wannan gurɓataciyar aika aika?

Sake maimata tambayar ta tayi tana lumshe ido alamun exhaustion nan ma rasa mai bata amsa aka yi sai ta fara jin tsoro kar dai an ma falmata wani mummunar abu ne zata yi wani maganar yayi saurin tallafo ta yayi hanyar upstairs da ita dan saura ƙiris ta faɗi a wurin saboda gajiya yayin da sauran ƴan falon suka zazzauna zugum dan har shi kan shi uban gayyar ba'a sanar da shi komai ba har lokacin bayan tafiyar su ne ake mayar da zance wanda Abduljabbar ne ya mayar da zancen kamar dai yadda matron ta ba su labari abin mamaki abin al'ajabi haka aka rinƙa alhinin wannan abu kamar wasar kwaikwayo mahaifiyar falmata da ta zo gidan sai Allah wadai ta ke da halin ɗiyar ta duk kunyar Aishan ya gama kama ta tamau wannan shi ake kira da ɗan kuka mai janyowa uwan sa jefa

gabaɗaya falon cike tam yake da jama'a yayin da su kuma suka ƙarasa ɗakin ya taya ta yin wanka duk a gajiye take haka da kyar ya gama yi mata wankar ya dawo da ita bedroom ɗin su ya saka mata doguwar riga marar kauri wanda bai matse ta ba ya kwantar da ita kamar jira ta ke ai ko ta shiga barci sai kallon ta yake kamar hoto kamar kar ya kifta idon shi dan kar a ɗauke masa ita kallon ta yake yi babu ji babu gani bugun ƙofar ɗakin ne ya dawo da shi daga hayyacin shi yayi saurin share hawayen da ke tsiyayo mai ya tafi ya buɗe ƙofar matar yayan shi ne maman big daddy kallon ta yayi ya ce

"Matar yaya  ya aka yi"?? Tsaf ta san kuka yake yi dan haka ta ce mai

"Abdulrahman kuka kake kan yi har yanzu bayan ga ka ga matar ka nan?akwai wani ni'imar da ta fi wannan ne a gare ka a halin yanzu"? girgiza mata kai yayi yana goge hawayen idon shi sai ta cigaba da magana
"Ka fito mu tafi falo amwai maganar da ake son yi game da yarinyar da ta sa aka ɗauke matar ka"a 360 ya ɗago ya ce

"Don't joke with this issue matar yaya kina nufin an gano yarinyar"? Girgiza mai kai tayi ta na tunanin ko ta wani fuska zai kalli abin dan haka ta matsa mai alamun ya zo su tafi juyawa yayi ya kalle ta kamar kar ya fita sai kuma ya fara tafiya itakuma ta tufe ƙofar suka sauko har downstairs tana baya yana gaba

Zama yayi itama ta zauna ga jama'a cike a falon a lokacin mahaifin salma ya buɗe taron da addu'a game da taya shi murnar dawowar shi gida shi da matar shi cikin ƙoshin lafiya kafin ya ɗan yi nasihohi gameda yanayin rayuwa da matsalolin su kowa sai jinjina kai yake yi daga haka ya yi shiru dan Barrister Umar ya cigaba da maganar..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now