"Cutie ina suka kai ki bayan sun ɗauko ki ya aka yi kika zo har nan garin"??

Bata yi nauyin baki ba ta ce
  "Hubby they took me to a psychiatric hospital and made me mad for some time kafin matar gidan nan ta taimake ni ta dawo da ni nan she treated me with sympathy""raba jikin shi yayi daga nata in total shock ya ce

"Psychiatric psychiatric hospital whattttttt"???? A yadda ya karasa maganar sai da muryar shi ta rankaya har cikib gidan wanda yayi sanadiyar shigowar ƴanuwan shi ciki muma da ke tsaye saman balconyn sama muka karasa saukowa a haukace ya ce
"Psychiatric?the took you to a psychiatric hospital baby"?? Tana hawaye ta girgiza mai kai ai sai ya sulale ƙasa yana jimami wannan wani irin sakaci yayi dayawa ne haka da har za a ɗauke mai matar shi a kai ta wata uwa duniya dan ma a muzanta shi har psychiatric hospital suka kawo mai matar shi anya akwai muzanci irin wannan kuwa a duniya?anya ba zai ɗau law a hannun shi ba kuwa akan wanda ya sa aka kawo mai matar sa psychiatric ɗin nan ba?

Da zuwan ƴanuwan shi suka yi saurin ƙarsawa gare sgi suna tambayar ba'asi amma kasa furta komai yayi suka juya suka kalle ta itama ɗin banda ruwan hawaye babu abin da take yi dan haka sun san ba zasu sami sa ba daga wurin su tashi suka yi suka karasa shiga falon tsayawa suka yi suna gaida matron nima muka gaisa daga nan ta ce masu su zauna suka zauna ita kuma ta nufi inda take tsaye ta kamo ta ta zaunar kusa da ita tana rarrashin ta ta sa aka kawo masu abin taɓawa babu abin da suka taɓan a ciki kawai jiran bayanin ta suke ta tambaye su ko ba matsala in ta faɗa ganin hankalin mijin Aishan baya tare da su suka ce ta yi bayanin ta kawai ba sai ta jira shi ba.

Tiryan tiryan ta labarta masu komai tun daga farkon ganin ta da ita da taimakon da Dr Ladan yayi mata na kai ta asibitin Barnawa har taimakon da ta samu daga masu kula da motocin shive da ficen asibitin da masu gadin asibitin da nurses ɗin wurin ta ɗora da cewa

"Duk waɗannan gwagwarmayar bai sa ta daina nanata sunan mijin ta a baki ba dan ko bacci take yi sunan nan na nan ban taɓa ganin soyayya irin tasu ba tun da nake Allah ne ya haɗa su"ajiyar zuciya suka sauke yayin da shi kuma ya miƙe ya iso gaban mu ashe dama hankalin shi na kan mu bamu sani ba riƙo hannun matar shi yayi yana kallon ta kamar bai taɓa ganin ta ba sai ranar

"Cutie duk ina raye aka maki waɗannan hurtful things ɗin? ya jinjina kan shi shi kaɗai ya san raɗaɗin da yake ji a zuciyar shi dan haka bai iya furta komai ba ya ma yayyen shi alama da su mai godiya

Godiya sosai suka yi wa matron haɗe da roƙon ta akan zuwa bayar da shaidan da zata yi a kotu ta amince ta ce ai taimako ne kuma bata san randa na ta zai faɗa a wani hali ba in bata taimaka ba tun tana dama ba toh haka itama za'a mata kuma tace in aka yi la'akari da tarihin ta bata taɓa yi ma na kusa da ita hassada ko kyashi koh mugunta ba shi yasa Allah ya sa ta faɗa hannun nagari

Gam ya riƙe matar shi idanun nan jazir ya ɗaga ta ya ce ma matron

"Am greatfull  for your help ma'am thank you so much Allah ya baki lada"da amin ta amsa sannan ya juyo gare ni da ke zaune ina admiring soyayyar su ya ce min

"Ms siyama you owe me alot if not for you i wouldn't have found my wife Allah ya saka maki da alkhairi nagode"!! Murmushi kawai na yi ina jijjiga mai kai raka su muka yi har motar su suka tafi na juya na ce da matron

"Anya ma'am ba zan bi bayan su ba kuwa dan ina jin labari na ba zai cika ba muddin ban bi bayan su ba"darawa ta yi ta ce

"Toh the great journalist kuma novelist kina iya bin bayan su mana sai islam ya kai ki"kiran shi tayi a waya ya ce mata yana daf da shigowa gidan ta dakatar da shi muka futo tare ta mai bayanin inda zai kai ni ta mana addua'ar safe trip da sauri na sallame ta akan sai mun haɗe a kotun ina mai yi mata godiya

Tun da suka shiga motar ban da kallon juna babu abin da suke yi in bai masu ba sai su rungume juna a haka har suka isa gida inda a nan ne suka tadda cincirindon jama'a kama daga family har zuwa abokan arziƙi ciki har da su salma da Barrister dan tun a hanyar su ta dawowa ɗaya daga cikin yayyen Abdulrahman ya kira ya sanar da su zuwan su shi yasa suka taru a gidan suke jiran dawowar su.

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα