"dan haka ki natsu ki dawo hayyacin ki muna da babbar battle a gaban mu we have to put family relationship aside and face the reality did you understand dear"?? Ƙala bata ce da shi ba ta yi shiru tana kallon shi juya kan da zata yi ta hango falmata a raɓe gu ɗaya a 360 ta miƙe ta nufe ta tana ɓarin baki wurin tambayar ta

"Falmata kin ji abin da suke faɗa?wai sunan ki ke ta zuwar masu baki sai furta shi suke yi wai  ɓacewar Aisha da saka hannun su har fah da yayan ki a cikin masu supporting ƙarerayin wannan ɗan iskan please dear je ki faɗa masu ba ke ba ce ki faɗa masu su daina ɓata maki suna"!! Tana hawaye ta ida maganar tana kallon falmata dan jin me zata ce ga mamakin ta sunkuyar da kai falmata ta yita kasa ɗagawa jijjiga ta ta shiga yi tana mata magana cikin tsawa

"Will you say something?ki je ki gaya ma yayan ki cewa ƙazafi ake son miki ki sanar da shi cewa baki da masaniya akan wannan sharrin da ake son laƙaba maki"!! Kusan duka mutanin dake wurin su suke kallo yayin da Barrister Umar ya karaso yana ƙokarin jan matar shi dan ya san ta shoga ruɗu ne ga gaskiya tana gani amma ta kasa amincewa ta gasgata gaskiyar riƙeta da yayi ai ko ta fincike ta damƙo falmata tana huci

"Ba zaki yi magana bane wai ko me falmata kina gani ana son ɓata miki suna amma kin kasa ƙaryatawa speak up will you"?? A tsawace ta karasa maganar sai dai abin da ya girgiza ta ta gani haɗe da birkita mata tunani dan kuwa kuka taga falmata ta fashe da shi tana sulalewa ƙasa ta saki hannun ɗan ta tana kuka mai cin rai da nadama haɗe da dana sani kasa cewa komai salma ta yi ta tsaya a wurin tana jallon falmata still tana so ta ji falmata ta karyata wannan allegation da aka mata amma ina kuka ya ci ƙarfin falmata sai yi take yi zuwa lokacin kabeer da iyayen su Barrister Umar sun rigada sun iso ganin falmata na kuka a durƙushe mijin ta ya karasa da sauri ya na tambayar ta lafiya

"Baby me ke faruwa haka me ya saka ki kuka what happened kid sis"? Ya ƙarasa tambayar yana directing tambayar zuwa ga salma da ke tsaye ƙiƙam kamar marar numfashi ganin babu amsa daga gare ta sai ya tambayi umar
 
"Umar talk to me meke faruwa ne wai ban gane ba duk kun min shiru what is going on"? a ruɗe ya ƙarasa maganar rasa abin faɗa mai Barrister umar yayi sai kawai ya sunkuyar da kan shi ƙasa cakumo Barrister Umar kabeer yayi ya ce

"Will you say something"?? Idanun Barrister umar yayi ja sosai kamar zai yi kuka yana jimamin sanar da shi matar shi ce ke da hannu a ɓacewar ex lover ɗin shi kuma babbar aminiyar matar shi haka zalika babbar aminiyar ƙanwar shi yana tir da irin halayyar ƙanwar ta shi yana da ya sanin haɗa jini da ita yana jimamin abin da zai aiwatar dan duk abin da za'a yi sai dai a yi amma alƙawari ya ɗaukar wa kanshi wannan extensive case ɗin shi zai yi handling no matter what and how the outcome may be dole ya juyawa family ɗin shi baya dan kare haƙƙin wanda aka zalinta ta nan ne ƙaɗai zai gyara sunan family ɗin shi daga ɓaci gabaɗaya da tarnizhinf image ɗin gidan su a idon duniya dan haka ya ɗago yana kallon Kabeer bai san ta yadda zai ɗau maganar ba

"Big bro she was behind everything she was behind her friend's abduction ita ta saka aka ɗauƙe Aisha"shock of his life da bai taɓa tunanin zai riske shi tun yanzu ba ya ji shiru yayi a tsaye yana kallon Barrister Umar kamar wani marar laka a jiki kafin daga baya ya ce mai

"Umar,ka saurari abin da ka faɗa kuwa? falmata my wife your blood sister jinin ka kake wa irin wannan zargin? anya ba biyar ka aka yi ba akan ka zo ka haɗa wannan ƙaryar ba tunda kai alƙali ne"?? Kafin a bada amsa sai suka ji murya na cewa

"Ko ɗaya babu wanda ya biya shi kuɗi dan nima shaida ne akan Majeed tare da falmata suke aiki"juyawa suka yi gabaɗayan su suka zuba mai ido wannan ɗin ba kowa bane illah Aqeeb wanda shigowar shi kenan tare da Ibrahim suka ji last words ɗin Kabeer..

Da azama ya ƙarasa gaban shi ya ce
"Aqeeb me kake faɗa ne haka she is your sister In-law koh dan ka rasa Aisha kake son saka kowa a blame game ɗin ka kar fah ka manta nima na rasa Aisha amma haƙuri na yi me ya sa kake son yi ma matata sharri Aqeeb are you insane"? A iface ya bashi amsa da

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now