"Haka muka yi zaki tafi ki bar ni ciki"? dubawa na yi na ga wata rigar na yi saurin miƙa mai ya ce
"Saka min mana cutie yau me ke damin ki ne sai ƙara min headache kike yi"saka mai rigar na yi ya ce
"Good wify"yana murmushi alwala ya saka ni yi shima yayi ya riƙe hannu na har muka dawo bedroom ɗin mu ya ajiye ni saman gadon mu ya nufi Waldrop ya buɗe ya nemo min abin da zan suturta jiki na ya miƙa min shima saka kaya yayi ya shimfiɗa mana sallaya muka fara sallar tare yana jan mu har muka idar ya ɗaga hannu yana ta addu'oi ina amsawa a rai na da amin muka shafa ya juyo ya kalle ni

"Cutie ya gajiyan biki da jama'a"? Da kai na amsa mai sannan na ce
"Alhamdulilah"
"Toh MashaAllah na ji daɗi yanzu sai barci ko"? Nodding kai na nayi sai ya miƙe tare da ce min in tashi na tashi ya naɗe sallayar na naɗe hijabin dama doguwar riga ce marar kauri a jiki na dan haka ban cire ba na tsaya jiran next command ɗin shi sai ko ya ja ni zuwa ɗaya side ɗin ya kwantar da ni shima ya zaga ya kwanta tare da matsowa kusa da ni ya kwanta da kai na a saman jikin shi ya ja mana duvet ɗin gadon tare da kashe bedside lamp ya tofa mana addua'ar bacci ina jin shi yana kai hannun shi wani wurin na fara riƙe mai hannun cikin magagin barci ya ce

"Don't i wanna sleep"salin alin na bar mai hannun ya cigaba da wasan daga karshe dai bacci ne mai nauyin gaske ya ɗauke mu dama ga gajiyan biki sai muka sha baccin mu mai daɗ...

**********
5:10am muka farka da sauri muka yi alwala muka yi sallar nafika kafin mu ɗora da farali addu'oin zaman lafiya muka rinƙa yi da gode ma Allah daga karshe muka koma bacci kamar dai jiya haka yau ma yana wasa da hannun shi a saman kirji na har barci ya ɗauke mu kuma.....

10:45am ƙararrawar ɗakin ya buga ni na fara farkawa na ga haske dal na yi miƙa haɗe da yin salati na zauna ina kallon jiki na sai na yi murmushi na juyo baya ina kallon innocent face ɗin shi yayin da yake bacci very handsome and gentile dan gasgata ba mafarki nake yi ba na kai hannu na ina zagaye fuskar shi in na ga kamar zai juya kan shi sai in yi saurin cire hannu na in ya koma sai in mayar haka har sau uku ina yi sai da na ji wall clock ɗin ya buga 11am na lalaɓa na miƙe na shiga toilet na wanke fuskata na yi brush na fito ban tayar da shi ba na sauko ƙasa na nemi kitchen na shiga ban gama regaining strength ɗi na ba dan haka fast food na haɗa mana da ruwan zafi mai kayan ƙamshi na kwashe su a tray na hauro har cikin ɗakin da tray a hannu na chan saman  centre carpet na ajiye a hankali na shige cikin toilet ɗin na yi wanka na fito duk yana bacci lallai kamar ma ya fi ni gajiyar bikin doguwar rigar material purple and white na saka an ba shi shape ya kama ni sai daga bakin shi ya buɗe kamar buba gyalen kayan na ɗaura na shafa turaruka na ɗan yi makeup ba dayawa ba na miƙe na dawo inda yake na yaye duvet ɗin na fara taɓa fuskar intensionally dan ya farka ya ko buɗe idanun shi a kai na sai ya rufe ya kuma buɗewa ya zuba min cat eyes ɗin nan nashi nima shi ɗin nake kallo na ce
"Goodmorning hubby"lumshe idanun shi yayi ya ce

"Morning cutie how was your first night in your home"?murmusawa na yi na ce

"Good"zai yi magana na ce
"Tashi ka yi wanka it's almost 12noon"ƙala bai ce min ba ya miƙe yana zura kafafun shi ƙasa ya sauka daga kan gadon ya ce

"Yes boss lady"dariya muka yi wato da tsokana ta ya farka

"Ko za'a raka ni ne"?saurin ce mai a'a na yi yana dariya ya karasa shiga ciki gyara gadon na yi na fita zuwa parlor dan in bashi space waya ta na laluɓa na ƙunna kiran ummi na fara yi tana ɗauka ta fara ci na tarar mun tara jama'a mun gudu mun bar su sai a sannan abin ke bani dariya gaisuwar ban gajiya na mata muka yi sai anjima falmata na kira ta ɗauka na ji tana cewa baba na bari mana kar ka faɗi a ƙasa
"Hey kina ta surutu"dariya ta yi ta ce
"Wallahi yaron nan akwai fitina barna yake son yi"muka gaisa na ɗauka ta manta abin da ya faru a jiya sai na ji ta fara ƙorafi dariyar kawai na yi na ce
"Falmata kan shi ke ciwo fah shi yasa muka dawo gida"wani shewa tayi ta ce
"Kun ji real house wife toh ya jikin nashi"?
"Da sauƙi"
"Toh Allah ya kara lafiya"Da amin na amsa na tambaye ta da yaushe zasu zo
"Wa ɗin wai mu?ai sai kun dawo daga honeymoon zamu zo ina mu ina zuwa gidan soyayya"dariya muka yi na ce mata sai anjima tunda tsokana take jin yi

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now