Bayan ya shiga dakin mommy ya zauna a Kam sofa din dake kallon gado ya zubama zara2n yatsun kafarsa ido.

Mommy ce ta shigo dauke da wani karamin tray a hannu bayan ta ajiye gabansa ta hada mishi tea Mae kauri ta bashi ba musu ya karba ta dakko plate din da fried  yam take ta bashi.

A hankali ta dinga bashi a baki Yana ci yana kurbar tea din har ya koshi sae ta mike ta dauka kayan ta tafi dasu.

Tana fita ya sauke wata ajiyar zuciya ya kwata tareda lumshe ido yana alfahari da samun uwa irin mommyn sa.


Da misalin karfe 11 ya koma part dinsu ko da yashiga duk sunyi wanka hannunsa Rafeeq yaja suka shiga dakin sa yace"wae Mae yasa kace mu saka ido akan Farouq "

Smiling kawae safwaan yyi yace"da farko shine suspect dina amma yanzu kuma.." sae yyi shiru

Rafeeq yace"to gsky ba wani alamu da suka nuna hakan amma ni mafi tunanin..." Sae kuma yyi shiru

Smiling kawae safwaan yyi ya e"yanzu ni Kiran waya kadae nake jira daga nan zan fara aiki na"

Rafeeq yace"kaefa dan isakan soja ne"

Duka ya kaimshi amma ya kauce yana dariya.

Safwaan ya kira Tasleem bayan ta dauka yace"sis Ina Nabeela take"

Tasleem tace"ya ai ba,a nan take kwana ba"

Yace "toh idan tazo ki saka min ido akanta sosae"

Tace to kafin ya kashe wayar

Ya kalli Rafeeq yace"kaema ka saka ido akan ma'aruf sosae"

Cikin mamakin mgnr sa yace"ya haka kuma taya kake tuna nin dan uwanka zae aikata ma hakan"

Smiling yyi ya koma gaban window sae da ya gama kallon mutanen dake waje yace"mutum mugune  bro ko Kae kanka zaka iya zama suspect dina so stop wondering dan nace ka saka ido akan ma'aruf"

Yana gama fadan hka ya shige toilet kallon sa kawae Rafeeq yayi sae yaga kuma ya koma bude kofar iya kansa kawae ake gani yace"don't think too much saboda ba komae bane ke bayyana kansa lkc daya ba amma idan lkcn yyi shida kansa zae bayyana har kowa ya gani ka gane bro"

Ya Kara sa fada yana winking idon sa daya.

Bayan ya fito daga wanka ya tsaya bakin mirror yana goge jikinsa da karamin towel sae phone dinsa ta dauki Kara tsaki yyi ya cigaba da abunda yake yi can komae ya tuna yyi sauri ya rarymi wayar yana dauka ya saka a handsfree ya cigaba da shafa manshi.

Daga can ban garen da aka kira mutumin yace"Kae soja Mae ji dakae ji da kanka na matuqar burgeni gaka wnn idon naka kamar fitila basu da tsoro ko kadan, haka zarrarka na matukar burgeni, infact komae naka na burgeni gsky ka cancanci wnn aiki naka I salute you dude"

Shiru safwaan yyi baice komae ba sae cigaba da Shirin sa kawae da yyi.

Ya cigabda da fadin"Ina so ka janye  wnn auren naka da masoyiyarka ohh sorry na manta fa ashe auren dole ne ko lallai wnn tsohon naka anya ma kuwa ganai sonka"

Ciza lips dinsa yyi ya rufe idon sa ya bude

Shi kuma mutumin yace"au mgnr ta ma ciwo ne sorry toh kaji, amma zae fi ma ka janye mgnr zaka iya kirana duk lkcn da ka shirya hakan" daga nan ya kashe wayar.

Safwaan Kam smiling kawae yake yi kamar Wanda aka ma albirshi din wani abu sae da ya gama Shirin sa tsab kafin ya shiga wani daki dake cikin dakinsa. Gurin duk kura sae ba ya gyara shi yasa turare ya kunna AC karin ya kunna wata system ya shiga sarrafata ba dade wa yyi wani kayataccen murmushi da shi kadae yasan dalilin sa

ASHWAAN (Love Saga)✔️Where stories live. Discover now