*FLASHBACK*
  Alh. Muhammad Karamat shine asalin sunan daddyn Rafeeq da Safa da matar shi Hjy. Amina mutanen kirki tun basu da komae suke tare dan sae Alh. Karamat yasha wahala kafin abashi auren Hjy. Amina sbd ita yar gdan masu kudin kyauyen su ce shi kuma bashi da komae. Bayan anyi auren ya tare da matar sa a family house dinsu dakin da mahaifiyar shi ta zauna kafin ta rasu. Shi kadae ne Allah ya ba ma mahaifiyar sa Baba hure, sauran duk baban su daya ne amma mama kowa da tashi. Sun sha wahala sosae cikin gdan sbd shine karami gaba daya  komae yayi sae ace ba dae2 bah ita matar tashi bata cika fitowa waje bah sbd bata da hayaniya ba karamin abu ke fitar da ita daga dakin ta bah. Haka suka ci gaba da zaman haquri da tsauwala acikin gdan. Yana Iya kokarin sa ganin ya faranta wa iyalinsa. Kullum kan hanyar neman aiki yake sbd shi kadae yayi karatu a gdan tare da taemakon mahaifiyarsa.
   Bayan ya dan fara kasuwanci a cikin garin ya tara kudin ya sayi gda dashi suka tare shida matar sa nan ma sae da aka ta rigima har gurin mae gari.  Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin jin dadi amma kash!!! Matsala daya har yanzu Allah bae basu haihuwa bah kullum cinkin addu'a suke ba dare ba rana.   Wata rana da bazu su taba mantawa bah itace ranar da Amina ta samu ciki Alh. Karamat na tsakar gida yana gyaran machine dinsa yaga Amina ta fito da gudu tana amai zuwa yayi ya taimaka mata har ta gama yana ta jera mata sannu daki ta koma ta kwanta saman katifa shi kuma ya fita yana jimamin abunda ya faru.
  Da dare ma haka ta kwana tana amai da laulayi washe gari tunda safe ya dauke ta suka je asibiti bayan anyi duk wani bincike daya kamata  angama aka shae da masa matar sa na dauke da ciki sati shida murna agurin sa ba'a mgn aka rubuta masa maganin da zata yi amfani dasu aka bashi. Bayan sun koma gda yake shae da mata da tana da ciki sati shida itama tayi farinci sosae sbd matan gidan suna mata gorin haihuwa rokanshi tayi da kar ya gaya wa kawo har sae cikin ya fito shi Kuma yace mata shknn dan yasan halin matan yan uwan sa wani lkc har gidan suke zuwa neman fada.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda kasuwancin Alh. Karamat sae kara haba ka yake yi dan yanzu har ya fara fita zu wasu garuruwa ya siyo kaya a ban garen Amina kuma cikin ta ya fito dan haihuwa yau ko gobe ganin baya zama gda sosae kuma labour zae Iya taso maya anytime yasa ta koma gdan su idan kuma ya dawo shi ke dauko ta in kuma zae koma sae ya mae da ta.
     Yau ta kama ranar laraba kama a yaune cikin ikon Allah Amina ta haifi santalelen yaro. A waya aka sanarwa da Alh. Karamat yayi farinci sosae yayi ta ma Allah godiya bayan kwana biyu ya shirya kayan shi ya dawo gda tare hado sha tara na arziki ma uwa da danta kowa yayi farinci sosae sae yaba masa ake tayi dan ya sayo musu kaya masu yawa abun sae son barka.
     
Bayan sati ya zagayo aka yi sunan biki inda yaro yaci sunan sa *Rafeeq* mutane sun so da yawa harda masu zuwa gulma abun sae son barka.  Bayan an gama kowa ya koma gda matan yan uwan sa kam suna komawa gda suka Shafa wa mazan su karya da gaskiya. Aiko bayan sallahr isha baffa Sani ya aika kiran shi. Yana zuwa ya gaeda shi yaki amsa wa sae wani fada na rashin dalili da yake ta mae wae akam ne zae karyar arziki bayan kasan cewa koh abinci wahala yake mana amma ka tashi ka siyo ma yaro kaya da sun ka fi kar finsa" ta inda yake shiga ba tanan yake fita bah saw da yyi mae Isar sa snn Alh. Karamat ya bashi haquri tare da kawo dubu biyar ya bashi yasea zance ya sauya nan ya fara sa masa albarka kamar shi mahaifinsa. Tun daga ranar baffa Sani ya dauki rakan tsana ya dora ma Rafeeq da Maman sa.
Haka rayuwa taci gaba fa tafiya kwanaki kuma saw gudu suke yi Rafeeq kam ya kara wayau da girma tayi bul2 dashi itama Amina tayi kyau sosae suna cikin koshin lpy  su dukan su Alh . karamat kuma kasuwancin shi sae kara habaka yake yi  kuma yana kula da iyalinsa sosae da sauran yan uwansa. Bayan arba'in mai biki ta koma gdan ta taci gaba da kula da danta. Wata rana da daddare suna bacci kwatsam taji an tada ta mike wa tayi zaune wasu mutane ta gani su uku  da suka a hannu hnkl tashe tace mae kuke so daya daga cikin su yace cikin uku ki zaba ko ki bamu kudi koh ranki koh in yanka wnn yaron kina gani hnkln ta yayi matukar tashi mike wa tayi ta bude wata akwatin garwa dauko musu kudin da baza su wuce dubu 40 ba ta  basu Wanda ya karba kudin yace kin tabbata suka dae ne dake tace ehh nan suka yi dariya suka fita suna tafiya ta kulle kofar dakinta ta hau katifa tana kuka Rafeeq ta dauko tare da rungumeshi tsam a jikinta wayar ta ta dauko ta shiga Koran mijinta. Yana dauka ta fashe da kuka hnkl tashe ya tambaya lpy nan ta bashi lbrn abunda da ya faru lallashin ta ya dingayi har tayi shiru ya mata alkawarin gobe zae shigo da haka suka yi sallama har aka fara kiran sallah r asuba bata kwanta bah sbd tsoro.
Washe gari misalin karfe 12pm karamat na cikin gidan sa hkr ya kara bata da kuma yi mata alkawarin ba zae kara barin su ba. Kayan su yace ta ha da zasu koma kano da zama. Bayan sallahr azahar koh da ya dawo daga masallai har ta gama hada duk abunda zasu buka ta, gidan su ya fara kaeta ta musu bankwana da daga can suka yuce family house dinsu aiko sunyi sa'a dan kowa nan dakin Sani suka fara Shiva nan ya kora mae baya nin halin da ake ciki ya kuma gaya mae cewa zasu koma kano da zama, fada Sani ya shiga yi bakakkautawa akan wane daliline zaka dauke ta daga nan koh dan kaga da farko ka bar gidan nan ban ma mgn bane yasa ka  zo min da wnn zancen shidae shiru kawae yayi shiko Sani yaci gaba si naga dae ga daki nan da ka bari idan ma tsoron kake ka tafi ka barta ai sae ka maeda ta nan koh kuma kudin abincin gdn nan wa zae ci gaba da bamu dan nasan da ka tafi yanzu baza ka kara dawo wa ba , ya juya ya kalli Amina yace idan ma asiri kika masa toh ki Sani bazae yi tasiri akansa ba damage na kula run ranar da kika shigo gdnn komae ya canza idan ranta yayi dubu toh ya baci dan mgnr da Sani ya mata da ba yayan mijin ta bane da... Shima  kanshi mgnr dan uwan sa ta kona masa  rae dan dae babu yanda zae da shine hkr yashiga bashi tare fada mae insha allahu komae ba xae canza bah kudi ya bashi daga nan aka dinga sa mae akbarka shidae yana mamakin halli iron na Sani ace ba abunda ke faran ta mae sae kudi. Aiko rakiya ya musu har waje yana cigaba da sama sa albarka.washe gari suka wuce kano. Anan suka cigaba da rayuwar su duk bayan kwana biyu yana zuwa gurin yan uwan sa kuma yakan je musu da shatara na arziki amma duk da haka Sani sae  yayi korafi .  itama Amina tana dan kasuwancin ta kuma cikin ikon Allah komae na tafiya dae2.

*Some Years Later*
 
   A dare daya Allah ke halittar bature wani gda mae mugun kyau na gani  da ka Gandhi kasan irin gdn nan da nera ta zauna ma wa komae na zamani aka sa aciki gate aka bude sbd motar da zata shiga bayan  anyi parking car din a parking space wasu yara gida biyu suka fito da gudu suka shiga cikin gda mutumin da ya kawo su yyi ta kiran su amma ina sun Riga sun tafi maigadi ne yazo yace kaga abu babban  drivern gdan karamat tafa wa suka yi suka gaesa sae baba maigadi yace a'a yana ga yaranka suna gudu ne Abu yace was sun tsere ne dariya kawae baba maigadi yayi yace Allah ya shir yasu Abu yace amin bari na kae musu kaya da suka bari yace toh afito lpy. A bangaren yaran kuma suna Shiva cikin gda Namijin yace eeeeyyyy na riga ki ita kuma maccen tasa kuka sae ga Maman su ta sakko ga guru safa taje tana fadin ummi kin gan yaya naming dariya ko ummi tace kyale shi yi hkr Rafeeq kuma da yazo hugging dinta ta matsa shima kuka yasa yana gaya mata ai tsera suka yi shine ya riga shigowa duka wa tayi kasa tayi hugging dinsu tace aje acire uniform ayi wanka da sallah sae aci abinci kafin lkcn islamiyya yayi suka ce toh anan suka cire kayan kowa ya gudu dakin shi wanka suka yi tare da yin sallah snn suka zauna dining cin abinci nan ma sae da sukayi fada sae da Ummi ta raba su, Rafeeq ya kalli safa uave yarinya zan daena wasa dake ne dan na girmeki da shekara goma ita kuma safa ta kalli ummi tace ummi wae ya girme in da 10yrs ummi tace 4 sure 😝 Rafeeq ya mata yana dariya ummi tace Rafeeq ya isa Maman kyaleshi kinji (Aysha shine asalin sunan safa sbd sunan kakarta ne ake kiranta da safa).........


Yawan comments
Yawan typing

Yours

Neeshar_jay 🎀

ASHWAAN (Love Saga)✔️Where stories live. Discover now