"Shi ɗin ya ɗau ɗawainiyar dinner ɗin"? Murmusawa yayi ya ce

"Eh shi ne"
"Me yasa sai shi ni bana so"
Dariya yayi ya ce

"Cutie you are still childish ai baki san maƙiyi ba in yayi alƙawarin ganin bayan ka sai ya cinma burin shi a halin da ake ciki ya chanza plan yanzu nuna min yake yana supporting ɗi na kuma a yadda na gaya mai shine tunda kika mai wannan cin zarafin sai na wulaƙanta ki a duniya hanyar da zan rama mai hanya ɗaya ce shine in aure ki in mayar da ke a karkashi na sai yadda na yi da ke in ya so bayan na gama muzanta ki sai in kore ki daga gidan na kora irin ta kare korar wulaƙanci bayan na tabbatar da cewa na naƙasa ki na naƙasa maki businesses ɗin ki har rasa inda zai saka ranshi yayi ranar da muka haɗa plan ɗin dan murna toh Mrs Abdulsalaam kin ji abin da ake shirya maki ni kuma yana ganin ni ɗin wawa ne kamar shi na buɗe mai ciki na shi kuma yana chan yana haɗa min gadar zare wai zai mana komai na honeymoom ɗin mu a nan yake son ya cika burin shi dan so yake a hanyar mu na zuwa kar mu dawo kin ga ai babu wanda zai zarge shi da saka hannu a mutuwar mu kasancewar shi babban ɗa shine yake son cika burin mahaifin shi da bai karasa ba kuma fah na gaya maki suspects ɗi na har da wannan yayan ƙawar taki dan haka ki kiyaye su again i want to apologize ba zamu tafi honeymoon ba koh ya gama processing komai zan amsa in mai godiya amma ba za mu tafi honeymoon ɗin ba a nan gidan gonan nan zamu zauna har sai bayan 3months zamu dawo gidan mu a wurin kowa mun tafi honeymoon kin ga in ya ga plan ɗin shi bai yi working ba zai ɗaura plan B mu kuma a lokacin zamu tafi ainihin honeymoon ɗin mu a ƙasar da kika fi sodan haka ko da wasa kar ki nuna mai cewa you are not intetested in this marriage dan na gaya mai kin gama fadawa a tarkon so na kenan ki yi duk yadda zaki yi ki yi sourcing information a wurin shi kin gane ai"??

Doguwar ajiyar zuciya na yi
"Oh duniya budurwar wawa wai shi ya rantse sai ya ga bayan ka ne?bai ga duk yadda yayi Allah na nuna mai ishara ba ne?Allah ya raba mu da maƙiyan mu"da amin ya amsa min

"Kin san yau kyaun ki na daban ne cutie you were just like a glamour kin ki kyau dan haka dole in biya wannan kwaliyar"sai a nan na tuna ashe fushi nake da shi sai na haɗe girar sama da ta ƙasa na ce

"Riƙe kyautar ka ban so"kamar wata ƙaramar yarinya na yi maganar sai ya dara ya ce

"Cutie you can't ignore me ni na sani kawai jan aji ne irin ta ki"harara na maka mai na buɗe baki da nufin ba shi amsa sai ga ƴar saƙo wai in zo in ji aunty mama na ce toh

Kallon ƴar saƙon yayi ya kalle ni ya ce
"Wai rowar ki fah ake min ba damar in yi magana da ke ɗazu haka suka saka mana ido yanzu kuma sun aika a kirawo ki nine fah angon ko sun manta ne sun ɗauka sace ki zan yi ne"? kallon rigima na mai ina wani mar mar da ido na ce

"Wa ya sani abu a duhu ƙila nufin ka kenan shi ya sa suka gane suke kafa kafa da ɗiyar su"na ida ina kwafa  dariya ya rinƙa yi kafin yayi wani furuci na ce

"Sai anjima dan ban ga abin dariya ba a nan"fuu nayi gaba ina maganganu ya ma gama raina ni dariya yake ma maganata ko da na shiga ciki ummi da wasu matan da ke zaune a parlor suka rinƙa bi na da kallo har na ji na fara tsarguwa na cigaba da tafiya ta suma suka cigaba da kallo na na juya naga ni suke kallo muna haɗa ido da su suka yi saurin sunkuyar da kai suna magana kamar ba su ke kallo na ba except ummi da ta fashe da dariya haɗe rai na yi na ce

"Zo nan ummi"tashi ta yi ta tako har inda nake

"Gani yaya Aisha"
daɗa harɗe rai na yi

"uban me kika gani kije wa dariya halan"? Ai kamar na zuga ta sai ta tuntsire min da dariya kamar in buge ta

"Yaya Aisha ɗazu fah fuskar ki a murtuke kija rinƙa ƙunƙuni wai ba zaki fita ba yanzu kuma sai da aka aika ɗan saƙo ya kirawo ki awa fah ɗaya da ƴan mintuna kika ɗauka a waje fah shi yasa ake ta bin ki da kallo ana mutsmuts"ta ida tana dariya abin sai ya harzuƙa ni na ja doguwar tsaƙi na cigaba da tafiya ta ina cewa

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now