"Yanzu shikenan ban da kwanciyar hankali a gidan nan komai magani"?

"Baki da sai kin je gidan mijin ki sai shi ya biye ma shiriritar ki amma a nan baki da shi shi kanshi in an kai ki sai ya saka mana albarka da gyara ki da muka yi shashashar yarinya"cikin ko in kula ta yi maganar kamar ƴar tsana a tsakiyar ƴan gida haka na koma  a gidan mu babu abin da aka fasa a ranar aka yi shuwa arab evening laffaya mai azababen kyau aka yane min jiki da anko muka yi da shi cream colour mai adon duwatsu masu kyau aka rankaɗa min kwaliya sai walwal na ke yi ko ina duwatsu ne a jiki na na ado extensive makeover aka min kamshi kamar kamfanin turaren maiduguri dan bari na ɗakin aunty mama matar nan ta zo ta rinƙa min turin turare ta tabbatar da turirin turaren nan ya biya koina a jiki na tun daga suman da aka kyalkyale shi har ƙafa na ƙamshi ne da aka gama kwaliyar aka buɗe ni da turare ƙarfe huɗu daidai aka fara gudanar da shagalin ranar ba african time tun fitowa ta aka saka slow kiɗa mai daɗi su salma da falmata ne a gefe na sun yi anko bayan mu ƴanuwan mu ne ban hango shi ba har sai da muka iso tsakiyar harabar wurin na hago shi zaune cikin rumfar a kan royal chair sai murmushi yake sakewa kamar wani wawa ya bi ya kafe ni da ido sai na rinƙa aika mai da harara amma bawan Allahn nan murmushi yake ta min kamar bai san me nake yi ba hAr muka karasa Inda ya ke da isar mu kafin in zauna sai yayi wuf ya miƙe ya fara zuba min kuɗi 1k note ya rinƙa zuba min sai da ya juye su duka tuni wurin ya ƙure da hayaniya ana ihu da mai kirari zama na nayi kamar ban san abin da ya yi ba shima ya zauna sai wani kallo na yake ni ni kunya ma ya rinƙa kama ni da irin kallon da yake min dan an cika a wurin mun zama tvn kallo flashes ta ko ina aka fara gudanar da program ɗin in har na ce bai yi kyau ba toh nayi karya dan ranar duk ya fita daban ko dan ango yake shi yasa yayi kyau na daban oho chan cikin rai na ina jin son shi na taso min da kishin shi amma ta wani gefen sai in ga kamar ina aikata rashin adalci ne

"Mrs Abdulsalaam kin yi kyau kamar kar in daina kallon ki ko dai a nan zan kwana yau"? Cikin calm voice yayi maganar wanda na ji maganar har chan cikin jiki na sai na yi shiru muryar shi na echoing a kunne na

"Are you shy of your groom Mrs Abdulsalaam"?? Banza na mai na yi kamar wasu nake kallo har da murmushin ƙarya sai ya juya dan ya ga ko da wa nake murmushin sai ya ga ba kowa juyowa yayi

"Ni kike nunawa attitude cutie"? Numfashi na sauke kawai dan na san magana yake son in yi mai ni ko fushi nake da shi

"Cutie ni ne fah so kike in saka maki kuka a taron nan"? Ƙala ban ce mai ba sai aka fara taka rawa a fili na mayar da hankali na ga masu rawan na yi kamar ban san da shi ba a wurin madaɗin ya kyale ni sai ya cigaba da min surutu da dai na ga bai da niyar yin shiru sai na ba shi amsa

"Humair dan girman Allah ka min shiru saka min ciwon kai kake yi"na ja baki na nayi shiru

Murmushi mai sauti yayi ya ce
"Toh na yi shiru Humairah"tsit muka yi har aka kira mu wai muzo mu taka rawa muka tafi filin kaɗan kaɗan muka taka yanayin daga ni har shi ɗin masu jin nauyin yin abu a gaban mutani ne sai muka yi abin cikin zamananci ana ta fesa mana turare da kudaɗe sosai aka cashe ba mazan ba ba matan ba abu dai yayi albarka around 7pm aka rufe taro lafiya aka sallami jama'a da kyaututtukar taron bai tafi gida ba ya tsaya jira na har na chanza kaya na same shi a jikin mota teasing ɗi na ya shiga yi

"Bar ganin ina kyale ki cutie zan haɗu da ke ne kawai barin ki fah nake yi saboda ban so hankalin ki ya rabu kashi biyu ki yi sha'anin ki cutie lokacin ki ne" hararar shi na yi na ce
"Damuwar ka"dariya ya fashe da shi ya ce

"Majeed zai zo gobe kar ki kuskura ki nuna mai auren nan ba cikin lumana ake yin shi ba dan akwai abin da na ƙulla mai kin ji cutie"? Sai na tsinci kai na da ce mai

"Wai har yanzu ba ka rabu da wannan majanunin ba heartthrob"? Smirk yayi ya ce
"Nahh sai mission ɗin mu ya cika cutie kawai ki bashi duk wani haɗin kan da yake nema dan shi zai haɗa mana dinner ya ce ya ɗau responsibilities ɗin komai na dinner"da mamaki na ce

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now