"Please don't go".. Da shaking voive na yi maganar sai na ga ko ya tsaya har ya juyo ya tsura min ido waiting for what i will say next shiru na yi dan kunyar shi nake ji a ce ina mace amma ni ce da furta kalmar so ga ɗa namiji kai abin bai yi ba sai wata zuciyae ta ce amma ai shi ya fara furta maki yana son ki ba ke ba dan haka just go ahead and say it in ba haka ba ke gari zai waya duk waɗannan tunane tunanen a rai na nake yin su kuma yana tsaye yana jiran amsar da zan bashi to his greatest surprise sai na furta

"Dawo ka zauna mana ina khadijah ta ke"?

In absolute amusement ya ce

"What"tsorata na yi da reaction ɗin sa sai na matsa baya kaɗan ina kokarin hana kai na zubda hawayen da ke son gangaro min dan ni kadai na san radadin da na ji lokacin da na kira sunan khadijah kafin in gama dawowa daga tunanin nawa na ji karar wurgi da abu a firgice na karasa dawowa duniyar tunanin na gwalalo idanuna waje bottle water da ke wurin yayi jefa da sannan ya juyo a matuƙar hargitse

"Damn it damn it"juyawa yayi ya fara tafiya a zuciye dan ran shi ya kai kololuwar baci

"I love you Abdulrahman"!!! Dif na dauke wuta kamar ba ni na gama furta kalmar ba yanzun nan yayin da shi kuma ya kasa sauke kafar sa kasa daga ɗagawar da yayi da niyar yin wani takun shiru shiru ni ban kuma furta 'a ba shi kuma bai juyo ba chan kusan minti ɗaya kalmar ta kuma kufce min daga baki na

"I love you"a wannan karon muryata na nuna alamun karaya dan a karon farko bai juyo ba yanzu ɗin ma ban saka ran zai juyo ba sai kawai na ƙara furta kalmar

"I Love you Abdulrahman"!! a nan ya juyo ƙaɗan ƙaɗan har ya karasa juyowar gaba ɗaya ya fara min wani irin kallo tun daga ƙasa har sama ni kuma na zuba mai ido ina kallon irin kallon da yake min ƙala ban ce mai ba sai na ga ya juya zai fita kamar in kwala ihu dan azaban da nake ji a rai na i don't know how but i found myself saying

"I said that i love you Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor please don't go".....

Da sauri ya juyo ya karaso gare ni ya ce
  "Kika ce me"?

Ban tsaya bata lokaci ba na ce

"I daid i love you"! Sai ya girgiza kan shi alamun bai yarda ba kallon shi na yi na kuma maimaitawa

"I love you Abdulrahman"..
hannuwan shi biyu a kan kugun shi yana kallo na ya ce

"Ban ji me kike cewa ba Ms Murad sake maimaitawa"

A wannan karon da kuka na furta dan ko na san mamaki ne ya cika shi duba da yadda na nuna mai ƙiyayya a ranar da ya furta min kalmar so ta ya ma zai amince son gaskiya nake mishi

"I said that i Love you mr Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor i love you i love you dearly""!!...

Girgiza kan shi ya shiga yi yana murmushin mamaki ni kuma na tsura mai ido ina kallon shi cikin tausayi da danasanin hali na

"Ƙarya kike yi Aisha ba kya so na bakin da ya furta ƙi ko ya dawo ya furta so toh tabbas yana da manufa amma ba har zuciyar shi ya furta ba dan haka ki sanar da ni dalilin ki na furta min wannan kalma"!?? A zafaffe ya kammala maganar hawayen da na ke boyewa ne suka tona kan su duk abin da min a halin yanzu ba zan ji zafin shi ba saboda ni na janyowa kai na komai

"Stop crying and answer me"!!.. kukan na cigaba da yi har da shesheka na kasa magana saboda karfin kukan ya rinjayi murya ta

"Goddamn it magana nake miki amma kin saka min kuka kamar wacce na daka"??

"Ce maka na yi ina son ka Abdulrahman kuma wallahi har cikin zuciya ta nake faɗa ba wasa nake yi ba dan Allah ka daina ja min rai yin hakan barazana ne ga zuciya ta"Da kuka na ida maganar cikin zaƙuwa da tsawa ya ce

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now