********
  Ranar da aka fara shagalin biki which was tuesday a ranar aka yi shuwa arab day ɗin wanda gabadaya jama'an da suka halarci wurin cikin shigar ƴan maiduguri suka fito aka nannaɗa laffaya aka saka kiɗan ƴan shuwa mawaƙan da suka zo ma ƴan maidugurin ne amarya cikin farar laffaya ta fito mai digon ruwan azurfa ta sha kyau dan yarintar ta ya fito fili sosai angon ma cikin farar rigar alfarma da dauri mai kama da rawani ya fito fuskar nan tashi ta sha gyara kawayen amarya biyu kuwa anko suka yi na peach laffaya sun yi kyau ni kuma da falmata da salma hade da babyn salma duk shiga iri ɗaya muka yi creamy laffaya muka saka yayin da babyn aka saka mata doguwar riga iri ɗaya ne sai dai ita doguwar riga aka mata sai daurin wani baby veil da aka mata ta sha ado da dankunne mai duwatsu sai walwal take yi ana ta tambayar ko babyn waye saboda fitowan da cikin falmata yayi ya sa bata taka rawa sosai ba ko ina ya buɗe da kamshin turaruka masu sanyin ƙamshi da daɗi a lokacin wasu ƴanuwan mahaifin yaya ib da bamu san da su ba sai dai Abbu suka zo har Abj domin halartar bikin ba laifi sun nuna mai so da kauna sosai dan sun sha wahala kafin su gano inda yake a nan suka yiwa Abbu godiya da kular masu da ɗa da yayi wani part aka ba su suka tare har a gama bikin sosai suka yiwa Abbu godiya da irin karramawar da suka samu

Rawa na zage na yi ni da salma kun san yanayin kidar shuwa arab mutum bai sanin lokacin da shauƙin rawar kan ɗibe shi a wannan moment din na ma manta da damuwa na saboda ga dangi da ƴan uwa su Ahmad sun zo kuma sun min alheri sun kuma ce  za su zo ɗaurin auren soasi na ji daɗin hakan na yi masu godiya da zasu tafi na haɗa masu package mai dauke da komai da aka raba ranar har hotuna muka yi da su ƙara bani haƙuri suka yi akan abin da khadijah ta min ba komai na ce masu har bakin motar su na raka su na dawo aka cigaba da shagali sai 7:00pm aka rufe taron da ciwon kai amarya ta kwana ranar har ango ya taya ta ciwon kan sai dariya ake masu duk Ya bi ya ishi aunty mama ta bar shi ya kuma ganin amaryar sa amma ta ƙi wai shine ya kwanta shima bai da lafiya

A washegarin ma haka aka yi kamu muka kuma yin ankon sai 6:50pm aka gama muka dawo gida a gajiye muka dawo dan ni ke ta up and down din ganin komai ya ta fi a yadda aka tsara shi kasancewar ni ce na haɗa kamun sai da na sha maganin zazzabi sannan na sami bacci zuwa next morning ɗin zazzaɓin ya sauka dan haka faram faram na yi da kowa ana min ya jiki na ce masu kar su damu jiki da sauƙi duba amarya da kawayen ta na masu sannun ban gajiya daga nan daki na na koma na kwanta kafin a shigo min da breakfast di na na karya na yi wanka kwanciyar na kuma yi sai a lokacin nake tunanin Abdulrahman tun ranar da abin ya faru ban kuma jin ɗuriyar shi ba babu kira babu email ba komai hawaye ne suka silalo min daga idanuna a bazata na yi saurin gogewa na cigaba da tunanin shi yanzu sai ya dauka ko ban da kirki ne ban damu da feelings din shi ba amma ai ni ba zarewa na yi ba da zan amince mai bayan khadijah na son shi kamar ran ta i can't cheat her toh ina ma ya shiga ne wai sai a nan na laluɓi waya ta na duba call log di na na yi scrolling zuwa kan numbern shi last call di na da shi almost one month five days kenan ban san lokacin da wani irin outburst ya riske ni ba sai kuka kamar me wannan wace irin sabo ne zuciya ta tayi da shi da har dan ban ganshi ba nake jin turiri a cikin zuciya na sai na fara maganganu a fili kamar mahaukaciya

"Me yasa ka min haka Abdulrahman me yasa ka bar ni da guilty conscious me yasa ka bar ni a lokacin da na fi buƙatar wamda zan gayawa damuwa ta why did you leave me in this state of desperation Abdulrahman? please come back ina so in baka haƙuri akan abin da na maka am willing to take back my words duka hurtful words din nan zan janye su Mr Abdulsalaam please just come back"!! Sai kuka shar shar ban ankara ba na ji an dafa ni da hanzari na ɗago kai na sai na ga aunty mama ce ta dafe ni saurin share hawaye na nayi sai ta girgiza min kai alamun in bar su su fito haka na cigaba da kukan karshe zama ta yi ta rungumo ni zuwa jikin ta sai kukan nake yi har na fara shiɗewa ta yi saurin kawo min ruwa na kurɓa na ajiye kofin sai sauke ajiyan zuciya nake yi akai akai sai da ta ga na ɗan saita sannan ta fara magana

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now