Bikin salma da yaya umar saura wata ɗaya yayin da na yaya kabeer da falmata saura watannin shida a wadannan lokutan abubuwa sun gudana kamar kula da falmata da ake yi gudun kar ta rasa rayuwarta dan bayan komai ya lafa aka sanar da iyayen yaya kabeer da su mama abin da ya faru har yasa na bar ƙasar na koma takaici da haushi kam sun ji shi musamman umma dan gani take an cutar da ni ban cancanci haka ba shikenan dan ban da uwa sai a rinƙa kuntata min yaya kabeer bai bin ta kanta yayan ta umar gaisuwar ma sama sama yake amsa mata gashi ya hana salma kula ta amma ita bazata iya ba duk abin da tayi bai sa ta ji ta tsaneta ba dan ta san ba yin kanta bane baba ya bata laifi sosai dan har horo ya mata na hana ta komawa makaranta wai bata da amfani sai da yaya umar ya mai magana akan ya barta kafin ya yarda suka koma tare da salma rashin kulata da ƴan gidan keyi ya daɗa haddasa mata ciwon zuciyar da take fama da shi daga nan ne dr hakeem ya sanar da su in son kashe ta suke yi toh bismilah tun daga lokacin ne aka ɗan sarara da halin ko ohon da ake mata yaya kabeer ma ya fara shiga dubata da jiki wataran har ɗan tsayawa yake yi da ita kafin ya tafi ita a hakan ma ya mata koh da zagin ta zai na yi a wani ɓangare kuma in ta tuno ni sai ta yi kuka dan tun da abin ya faru bamuyi communicating da juna ba but ta san kowa da kaddarar sa matar mutum kuma ƙabarin sa

Yaya Ibrahim tun yana sharewa da batsewa akan kular da ummi ke ba shi yana mata tsawa da korar ta wataran ma har hantarar ta yake yi akan tana ƴar ƙarama da ita amma ta san wani abu wai shi so har dai ya daina ganin ita ɗin itace nashi dan bata guje shi ba tun tana yarinya take son shi ba ta sanar da shi ba ta riƙe sirrin ta har ta iya controlling kanta a lokutan da yake kula falmata kenan she doesn't deserve all these hatred dan ga wacce yake mutuwar so ta ƙi shi ashe wani daban take muradi har ta ke son salwantar da kanta akan shi ga wacce take kaunar shi haka yake dama naka baya taɓa gudun ka duk lalacewar ka ya kuma duba irin hallarcin da mahaifin ta da yar ta suka mai bai kamata ya saka masu da haka ba tun daga nan ya fara saukowa yana sauraron ummi wata rana har fita outing yayi da ita inda ya yi confessing mata soyayyar da yake mata har da alƙawarin zama da ita har ƙatshen rayuwar shi ma'ana auren ta zai yi ranar ummi bata bar ni na huta ba dan murna da farinciki na taya ƴar uwa ta murna dan ita kadai ce gareni wacce zamu iya sharing damuwar mu da farincikin mu tare hasina kuwa ta kasa boye murnar ta har sai da ta je ta sanar da falmata cewa ai yaya Ibrahim auren ummi zai yi nan ba da dadewa ba a lokacin ta ke ƙara tuno da rashin adalcin da ta yiwa ahalin mu

Akan maganar motar da yaya kabeer ya bani kyauta kuwa wanda yaya Ibrahim ya tambaye ni yadda za'a yi da shi nace ya bar min shi kawai ni nasan me zan yi da shi

Bikin falmata ma a bakin salma nake ji dan ita nauyi na take ji duk yadda na so ta share maganar abin ya ci tura nikuma sai na bar ta ina jiran zuwar ranar da zata sake da ni a karo na biyu

During those moments Khadijah happens to be the only close friend of mine ita ce ke kwantar min da hankali tana iya kokarin ta dan ta ga na sake jiki na though akwai lokuta da dama da nakan zauna tunanin kamar na yi wawta barin masoyi na ya kufce min amma in na tuna da ƙaddarar bawa da kuma maganar "matar mutum ƙabarin sa" sai in ji sanyi killa ma yaya kabeer ba alkhairi bane a gare ni adduo'i na rike da kyar da dambe da zuciyata na samu na tunɓuƙe yaya kabeer a zuciya ta da kwakwalwata na yi ƙokarin dasa ƙaunar aminiyata falmata a zuciyata wacce kaunar har ta fi ta da bikun salma ya gabato a inda take sanar da ni wai anjima zata turo min pre wedding pictures din da suka yi ita da yaya umar abin dariya ya bani ustaz yaya umar da pre wedding pics sai ta ce min ai ita ba zata iya da ustazancin nan nashi ba sai da ta juye mai kafin ya amince haka kawai abin lokaci guda ya ce ba zai yi ba shi ustaz dariya sosai ta bani irin wacce na daɗe ban yi irin ta ba ai kuwa muna gama video call din ta turo min hotunan kala kala wani dariya yake bani ganin kamar salmar ce ke yin style din wani kuma kamar bai da niyar haɗa jikin shi da ita wasu sun yi kyau sosai tun ma wadanda suka saka kaya kusan iri ɗaya wato blue colours shi ya saka da babbar riga ita kuma bata saka gyale ba suna tsaye murmushin sa ya fi wadda ta yi da na tambaye ta dalili sai ta ce min wai ai raina mata wayo yayi yace ta kalli mai hoton tana juyawa ya mai signal da ya ɗauka shi yasa murmushin sa ya fi nata abin dariya..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon