BIYAYYA BAYAN RAI

770 44 0
                                    


BIYAYYA
BAYAN RAI

NAH

UMMU ASMAU(SA'ADTU)

DEDICATED TO NABILAT ZANGO(LEADY)

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 5-10

Asalin labarin

Dr muhammad imam, haifafen garin zaria ne, a cikin sabon garin zaria, mahaifin sa malan musa bature, malamin makaranta ne, dr muhammad su ukku ne wajen mahaifan su, sadiya ce babba sai Aisha, da muhammad imam, mahaifin su malami wata secondry ne a nen zaria, da mahaifiyar su inna fatima, su ukku ne wajen malan bature, inna fatima ta haifi wasu yaran kamin su Aisha suna komawa, a Aisha ne yaranta suka fara tsayawa, malan bature fari ne sosai shiyasa mutane ke kiran sa musa bature, rayuwar iyalin shi gwanin shawa bai rage su da komai duk da zaman sa malamin makaranta.

Inna fatima ma tana sana'onin  ta cikin gida irin na mata, cikin rufi asiri suke rayuwa, sun aurad da Aisha da sadiya bayan sun kare secondry.

Mijin sadiya dan zaria ne, a kaduna yake aiki, a kaduna anka kai Amarya. Mijin Aisha dan zaria a nen zarian yake aiki, auta imam dai ne  a gaban inna yana aji hudu a makarantar secondry, haka rayuwata ta cigaba da tafiya.

Dr imam na ajin karshe secondry, Allah yayi mahaifin su malan bature rasuwa, sun shiga cikin tashin hankali rashin mahaifin su, inna fati tayi kuka, da baya suka yi tawakali, bayan rasuwar mahaifin dr imam yasamu Admission a state universty kaduna da taimakon mijin yayarsa sadiya.

Da taimakon mijin sadiya da Aisha dr imam ya hada first dgree din sa a state university kaduna.

Bayan yayi bautar kasa yasamu aikin karantar wa a wata secondry a zaria, lokacin inna fati shekaru sun ja, su sadiya da Aisha kowa nada yaransa, inna fati ta matsa akan dr imam yayi aure tunda yasamu aikin yi, a samaru zaria ya samu yarinyar da yake so mai suna zainab, zainab yarinyar  ce kyakyawa , ta gama secondry school akayi auren ta da dr imam.

Bayan shekara daya lokacin zainab nada ciki, dr imam ya koma yin masters din sa a ABU zaria, bayan wasu watani zainab ta haifi kyakyawa yarinyar ta, mai kama da mahaifin ta, fara sosai tayi gadon farin kakanta malan bature, anyi suna lfy, yarinya tace sunen Na'ima , lokacin dr imam ya kamala master din sa yasamu lecture  a kaduna polytecnic, Na'ima nada shekara daya, Allah ya yiwa inna fati rasuwa.

Bayan wasu shekaru dr imam ya koma nen ABU Zaria,  yayi phd in sociology, bayan ya kare ya dawo nen ABU da lecturing lokacin yaransa biyar, Naima, ummi fatima, sadiya, fahad da kabir, ummu zainab dr ya saka makaranta har tayi dgree din ta a islamic study, tana karantar wa a FGGC zaria

Rayuwa gidan dr imam, abin koyi ce,  yaran dr imam a shekaru goma suke  sauke qu'rani, sun samu kyakyawa tarbiya a wajen ummu zainab yanda suke kiranta, dr kuma abba,  yaran dr imam a therbow duk suke karatun su.

Kawancen Na'ima da maryam ya farane tun a secondry school,  ajin su daya har suka kamala secondry school, sosai zumunci ya kulu tsakanin umman Naima da mahaifiyar maryam.

Bayan kammalawaarsu suka samu admission atare. Cikin saa suka fara  karatunsu basa kula kowa, maryam tana matukar son Na'ima ita ma tana sonta.

Halinsu yazo daya, duk abinda daya zai zartarwa sai da shawarar daya, mutane da yawa suna son su, yanda suke tafiyar da rayuwarsu. Har suka gama aji daya basa gama aji daya basu bama, kowa fuska domin yayi masu magana ba.

Yayin da wani Hafis course mate dinsu ya kamu da soyyyar Na'ima,  duk abokansu sun san irin son da hafis yake ma Na'ima, babban abokinsa Imran shike karfafa mashi guiwa akan yaje ya fada mata sirrin zuciyarsa.

Amman sam yakasa samun kwarin guiwa daga zuciyarsa. Da haka har suka kammala hundred level.

Bayan sun dawo makaranta, Hafis kullun tunanin yake yanda zaima Na'ima magana, watara sun kare lectures, ranar Na'ima dai ce ta shiga makaranta lokacin hafis na tare da Imran, Na'ima tafiya take yi tana jin wani irin rashin zuwan maryam makaranta, ta kira wayarta tace mata bata jin dadi.

Da tunanin zataje ta diba maryam ta isa inda tayi parking motar ta, lokacin da zata shiga univarsity dr ya saya mata karamar honda civic bata dade ta iya, har tana zuwa makaranta da kanta, watarana ita ke zuwa ta dauki maryam ko driven su ya kaita.

Da kyar lmran ya matsawa hafis yaje ya yiwa Na'ima magana, tana cikin kokarin bude mota taji salamar su, tana juyo tana amsa masu, sun gaisa don tana ganin su in zasuyi lectures, imaran yayi karfin halin ce mata abokin na keson magana dake tayi shiru tana sauraren su, Hafis yana
tsaye ya kasa cewa komi,  imran yaga shirun yayi yawa yace Na'ima hafis abokina ya dade yana son ki, ya kasa fada maki.

Na'ima ta dago ta kali imran, tace mashi ta gode, amnan su yi hankuri ita ba soyyaya ya kawo ta ba karatu tazo yi, ta shiga mota ta wuce, hafis jikin shi yayi sanyi, lmaran ke karfafa mishi da yayi hankuri watara zata so shi.

Na'ima kai tsaye gidan su maryam ta wuce da tunanin me hafis din ke nufi, ta isa gidan su maryam dake pz, tayi hon maigadi ya bude ta shiga tayi parking, a kicin tasamu mamar maryam sun gaisa tana tambayar ya jikin maryam, tace da sauki ta shiga tana cikin, nasan zaki zo yau mutuniyar ki bataje makaranta ba,  tayi dariya ta wuce dakin maryam din kwance ta same ta, Na'ima tace na zaci is serious,   maryam tayi dariya tace nadai ji sauki da fever na kwana jiya ban jin dadi, Na'ima tace Allah ya baki lfy ai zaki je makaranta goben ko, maryam tace zanje   naji sauki, Na'ima tace bari inje gida ban ma fada ma umman mu zan zo, hankali ya tashi na zaci sosai ne, maryam ta rako ta har wajen mota suka yi sallama.

Na'ima ta isa gida kusa ukku da rabi na yamma, ta yi parking ta shiga cikin gidan da sallama, ta samu umman su falo kannanta na shirin zuwa islamiya don ka'idan dr ne ko Na'ima dake university in batada evening lectures tana bin kannen ta zuwa islamiya, umma tace yau kin dade nasan biyu kuke gama lectures, tace maryam ce batazo makaranta bata da lfy naje na dibata, ummu tace da saukin jiki nata, zan kira hajiya saudatu mahaifiyar maryam, Na'ima tace da sauki gobe ma tace zata shiga makaranta, ummu tace kiyi sauri ku shirye zuwa islamiya hudu ya kusa.

Bayan sun dawo islamiya duk yaran gidan na tare da dr falo suna kallon news , ka'idan dr ne baa kallon firm ko series gidan sa,   news ne ko history, islam channes sune yaransa ke kallo, da an kare news sun kare homework zasu je  kowa ya kwanta, Na'ima in tana exams zata wuce dakin su tayi karatu.

Da safe  maryam da Na'ima sun hadu school, sam Na'imar ta mance maganar Hafis, sai da suka shiga lecture, bayan sun fito take ba maryam labari, maryam tace to ke me kice masu , tayi dariya tace mi zan ce masu bayan ba soyayya ce gaba na ba.
K

kullun hafis na bibiyan Na'ima tun basa kula shi har suka fara gaisawa, sannu sannu soyyaya mai karfi ya shiga tsakanin su.

Tushen labarin

Muje zuwa

Biyayya bayan rai completedOù les histoires vivent. Découvrez maintenant