5:45 am na tashi na duba gefe na kunna light da sauri na tashi na watso ruwa na yi alwala na tada sallah ina idarwa na wuce na hada breakfast mai sauki a kitchen din nayi na wanke kayan da nayi amfano da su na fito zuwa falon na kira lambar mutumin d ban san sunan shi ba ringing uku ya daga muka gaisa na mai bayanin yanda muka yi da yaya kabeer ya ce mu hadu a makarantar by 9 godiya na mai na kara kimtsawa na haɗa komai a jaka ta na fito dan dama doguwar riga ce a jiki na peach colour sai na dora karamar hihabi peach na rufe kofar na tare taxi muka tafi school din..

Komai da ya kamata ya kammalu ya kammalu mun ajiye akan gobe zan fara attending classes di na godiya na mai sosai muka tafi straight gida na wuce it was already 2pm so yin komai nayi na kira yaya kabeer na mai bayani daga shi sai na kirawo Abbu na sanar da shi shima sai su salma daga haka na kwanta dan a gajiye nake sosai ban farka ba sai huɗu saura sallah na yi da na idar na yi wanka na shitya cikin simple gown grey colour na yi rolling mayafi shima grey na saka wage shoe na fito na ɗan zaga wuraren da muka wuce ɗazu kafin mu tafi makarantar sai shida da rabi na dawo duk inda na tafi na dau hotuna na turawa yaya kabeer da aminaina..

As early as 6am na shirya na dau karikitai na sai makaranta saboda ina so in san lokutan lectures di na in case zan yi scheduling activities di na bin direction din department din mu na yi na shige hall din ba daɗewa aka fara shigowa har dai aka taru duk fararen fata nake gani ni kadai ce bakar fata sai chan da aka fara introduction ne naji wata ta ce sunan ta Khadijah Alhassaan sai na waiga da sauri na ware idanuna ina duban inda zan hamgo ta chan na tsinkayo muryar ta tana cewa
"From Nigeria"

Ƴar kyakyawa doguwa fara da ita ga iya daukar wanka haka nima na fadi na wa sunan da ƙasar da na fito itama sai ta kai duban ta gare ni kafin mu haɗa idanu ta sakar min murmushi nima na mayar mata lectures mu ka yi a karshe aka ce mana next week zamu fara practicals murna kamar me daman na matsu in ji yaushe zamu fara practicals din nan..

Mun fito kenan sai ga Khadijah ta taho gare ni tana min murmushi nima ina mata sai ta ce min
"Yar kasar mu ya kike a wani gari kike"ni dariya ma tambayar tata ta bani duk a lokaci ɗaya sai na dan dara nace mata

"Daga Abuja nake a wuse zone 2"da sauri ta ce haba da gaske nima ai ƴar Abj ce saidai a zone 4 muke ya aka yi bamu san junan mu ba tun kafin mu zo

Dariya muka yi alokaci daya na ce maybe lokacin haɗuwar mu ce bata yi shi yasa ta gaya min inda take da zama nima na sanar da ita inda gida na ya ke muka yi exchanging contacts din juna akan zamu na jin motsin juna har gobe kafin mu haɗu tafiya muka yi kowacce ta tafi hanyar ta..

   ********************

_Turkish University ABJ_

Motar su salma ce ta shigo falmata ce ke jan motar yayin da salma ke gefen ta tana ta faman kyalkyale fuska dan bata gama ba lokaci ya fara hararar ta sai ta fito kawai da zuwan su parking suka yi suka fito ƴanmatan jami'a joude maroon jallabiya suka saka da rolling din su wage suka saka aka maka black speck mai design  fuskar nan ta sha makeup ana taku dai dai sai kallon su ake yi haka suka daure fuska ana cicin magani sai rigima ake zubawa har department din su falmata salam ta raka ta blowing kisses suka wa juna kafin su rabu ita kuma salma ta wuce tata department din lectures ya musu daɗi sai hudu saura suka fito duk a gajiye suke wannan karon salma ce ta tuka motar suka isa gida dakin su salma suka baje a nan aka kawo musu abinci suka ci suka yi sallah wanka suka yi kowacce da towel a kirji ga net cap suka saita wayar falmata aka danna kira zuwa Egypt ni dake kallon wani painting da aka ba mu a matsayin assignment na ji kira dubawa ta na ga ƴanmatan mu ne sai na dauka da sauri na yi positioning wayar na dauka ganin su babu riga na ce

"Yanmatan jami'a ya lectures din ne wai"

"Babu daɗi sweetheart very stressful mun gaji ya naku lectures din"

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now