Karasowa cikin dakin tayi ta nemi wuri ta zauna tana ƙoƙarin kwace kwalbar hannun nashi ya ƙi saki mata sai da ta haɗa da karfin ƙiban ta kafin ya saki dan shima din a ɗan buge yake tana ƙarba ta wurgar da shi a bin din dake dakin..

"Yaya Aqeeb sau nawa zan na gaya maka cewa shan wani abu koh zukar wani abu ba zai taɓa yaye maka damuwar ka da matsalarka ka sai dai ma ya ƙara maka damuwar da zarar ka dawo hayyacin ka ga babbar zunubi da ka aikata ma ubangijin ka haba ni na gaji wallahi Allah yaya gayawa iyayen mu zan yi ni na gaji da wannan halin naka mutum ace ya zamo mashayin karfi da yaji su turawan da kake tare da su ba ka ganin marasa kamun kai ne ke zuwa mashayar ba kana kamilin ka da haddar ka amma kake saɓo toh ni kam na gaji da rufe ma a yau a yanzu zan kai karar ka kowama ya huta"

Banza ya mata sai da ta tashi da niyyar tafiya yayi ƙoƙarin dakatar da ita

"Kid sis kar ki kuskura ki fara dan kamar kin co amanar alƙawarin da kika dauƙar min ne na ɓoye min sirri na"kallon shi tayi kamar zata yi kuka sai ta ce

"Yaya ka ce in ran ka ya ɓaci ne kake kora wannan abin kana so kace min yau liyafar mu ce ta ɓata maka rai har ka kasa hakuri sai da ka dangana da shan barasa"??

"Kid sis tsaya ki ji amma kar ki kai wannan maganar ga iyayen mu"
Ta haɗe fuska ta ce mai lallai sai ya sanar da ita damuwar sa

"Salma am crazy na haukace akan mallakin yaya na yayan nawa ma mafi girma da ƙima a wuri na can you believe this huh"?? 

Da mamaki ta ce yaya Aqeeb me kake nufi da maganar ka ban fahimce ka ba

Hawaye ya share na ƙunci da baƙin ciki ya ce"salma na daɗe ina rainon soyayyar ta a zuciyata na so mu yi *Soyayya mai garɗi* da ita wanda hakan zai kaimu da yin aure mu shimfiɗa rayuwar har abada mai tsafta amma duk ashe mafarki na ne ni kadai ashe wani nake yiwa kiwon ba kaina ba"

Shiru ne ya ratsa wajen dan kuwa salma bata san inda yayan nata ya dosa ba in kuma abin da take zargi ne toh lallai shima ruwar dafa kanshi ya deɓo a hanzarce ta ce mai

"Yaya kana magana a karkace in na harhaɗa maganganun ka duka kana so ka ce min matar yaya kabeer to be kake so kuma babbar aminiyata"??

Da sauri ya tare ta kafin ta dora da wata tambayar ya ce
"Salma pls ko daina kirawo min abar kaunata da sunan matar wani abin na ƙona ni har cikin ƙahon zuciyata bazan iya ba bazan iya cigaba da zama a ƙasar nan ina kallon yaya na na jini yana shimfiɗa rayuwar da na so in shinfiɗa da abar ƙaunata ba ba zan iya ba i have to leave if not ina iya yin abin da kowa ma zai yi dana sani"

A tsorace ta juya ta kalle shi ta ce yaya girman son da kake mata har ya kai matakin da zaka iya aikata mummunar abu??
"Salma in da kin taɓa soyayya koh kuma kin san zafi da raɗaɗin shi zaki taya ni baƙin cikin da nake ciki"

A tsanake ta mai kallon tsaf dan ita dai bata shirya rabuwa da ɗan uwanta ba ba za ma ta iya ganin shi cikin wannan halin ba dan haka ta ce mai

"Amma kana ganin a hakan zata so ka har ma kuyi *soyayya mai garɗin da ita*?kana fah ganin irin gurɓataciyar rayuwar da ka zaɓar ma kan ka wai shine cigaba a hakan zata aure ka kana ganin wata rana bazata san abin da kake yi a cikin duhu bane?kana ganin ni kaina zan bari rayuwar ta ta shiga haɗari ne bayan na san ba zaka iya rike ta yadda ya kamata ba a jin ka ba ta da gata ne ko kuma dan bata da ƴanuwa shikenan sai a cutar da ita??gaskiya yaya ka yi hakuri kawai amma ina ji ina gani Aisha na tsaka da kaunar yaya Kabeer in ce zan hana ta ba sai dai ka san yanda zaka yi dan ba abu mai yiwuwa bane ka ce kana son budurwar ɗan uwanka ba"
Kaiwa nan ta mai shiru tana jiran me zai ce

Kallon mamaki ya mata ya ce salma kina nufin duk kusancin mu da ke har zaki iya zaɓan wani ki bar ni ɗan uwa ya fi ɗan uwa ne?

Sai kuma ya bata tausayi ita kanta ƙarfin hali take yi ya zata yi ta riga ta hango kauna mai zafi tsakanin masoyan dan haka ita baza ta so ace ta silar ta zuciyoyin masoyan ya taɓu ba

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now