"Yes yes yess yaya kabeer i will be your MTB and your forever inshaAllah"

Ai tuni ya miki ya fara juye juye kamar me neman wani abu sai ya kuma durkusawa kasa ya fiddo da wata yar karamar akwati ya bude min yana mai cewa

"Aisha Murad will you be the wife of Kabeer Habib"?
Da sauri na ce mai
"Yess i will"ni sauri nake ma ya yi ya tashi daga tsugunon da yake dan na fara gajiya da ganin shi a ƙasa amma shi koh a jikin shi

Da sauri ya cire zoben da ke cikin akwatin zai saka min na yi saurin dakatar da shi na mika mai hannu na instead murmushi kawai ya min dan yasan dama hakan ne zata faru sai ya saka min akwatin a hannu na na karba ina mai murmushi nima hall din ya kuma ƙurewa sa tafin jama'a yan jaridu an sami abin bugawa da cewa sai dauka suke ta yi

A harzuke yaya Aqeeb ya bar hall din itama falmata da zafi da radadi ta fita batare da wani ya lura ba

Tasowa yayi ya tsaya yana ta faman yi min godiya da alƙawarurukan kula da ni har karshen rayuwar shi wanda hakan ya saka kowa yi mana kallon sha'awa abokan aikin shi da suka hallari wurin ma sun taya shi murnar samin mace ƴar yarinya a matsayin matar aure har da yi mai tsiyar ashe shiyasa baya kallon kowace irin mace duk kyawunta dama yana da yar beauty da ya ajiye yake musu wayyo..

Haka dai aka karaci liyafar dan labarin mu a baki kowa mun fita mun iso kenan zamu shiga mota muka duba bamu ga falmata ba dubawan duniyan nan mun yi bamu ganta ba dan haka aka koma cikin hall din neman ta an fito ba'a gan ta ba sai gashi ta bullo daga gefen mu tana murmushi da sauri muka nufe ta muna tambayar ta ina ta tafi dariya ta yi ta ce

"Kun ji ku kun shagala da karbar surprises din ku ina zaku lura da cewa bana kusa anyway congratulations and happy birthday to you dear Allah ya bamu aron rai muga ranar bikin ku ke da yayan mu" ta ida maganar ta tana rungume ni sai ta share hawayen ta tana kokarin danne kishin da ke taso mata dan ta san duk yadda zata yi bazata taba samin soyayyar da ta daɗe tana dakon shi ba har abada daga wun yaya kabeer din dan haka kawai sai ta yi kokarin rarashin kanta da ɗorawa kanta dangana da yin alƙawarin taya ƙawar ta aminiyar ta samo soyayyar yayan na su...

Jin ɗigar abu kamar hawaye a kafadana na yi saurin ɗagowa na kalle ta na ce

"falmata me haka na ke gani daga idanun ki kamar ruwa"

Dariya ta yi ta ce min
"Kin ji ki da irin halin taki koh a'a ba ruwa bane pampo ne aka buɗe"

Duk sai muka yi dariya dan maganar ta bamu dariya matuka a gatse ta faɗe shi da haka nima na rungume ta ina mai jin daɗi nace mata thanks sweetheart...

Zan shiga motar kenan yaya kabeer ya ce ai bai san zancen ba sai dai in bishi mu tafi amma nima kememe naki yarda nace sai dai mu shiga tare da su salma ya ya iya da ni haka ya amince muka shiga ni da shi a gaba salma da falmata a baya tun da muka shiga surutu salma ke yi amma falmata daga uhmm sa uhnm bata iya buɗe bakin ta dan ta san tana bude bakin nata kuka ne zai fallasa sirrin ta wanda ita kuwa baza ta so hakan ba ni kuma kunyar yaya kabeer din nake ji shiyasa na kasa ce mai komai sai zuba yake yi ƙarshe ma shi da salma suka koma suna hiran har muka dawo gida yayi dropping din su ni kuma ya ce toh yanzu sun tafi za'a yarda a bi ni mu tafi gidan koh sai an samo yan rakiya?

Rasa abin fada na yi kawai sai na juya fuskata zuwa gefen murfin motar ina kallon hanya abin ya burge shi dan ya lura kunyata a jini take shiyasa ya dage akan lallai sai ni zai aura dan yasan zai sami rayuwa mai dadi da ni a nan gaba..

"Mrs Kabeer kin min shiru should i consider that as a yes"?

Na daga kai na kawai shi kuma ya ja motar muka tafi akan gobe su salma zasu shigo gidan mu a hanya ya rinka ja na da hira tun ina shashare shi har na sake ƙaɗan in ya tambaye ni in dan amsa mai a nan ne yake tambayata a ina nake a islamiya nace mai duk wuri daya muke ni da su falmata muna izhu arba'in da shida yace min wow ashe har mun kusa saukewa kenan na ce muna fata haka dai hirar ta kasance har ya dawo da ni gida inda yaso ya kuma dasa wata hirar nace mai

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now