Murmushi kawai yaya kabeer ya yi yana mai yi wa Abbu godiya da ya yarda da shi wannan yardar ya sa yake da full confidence akan abin da yake da niyar yi ba tare da ya ji koh da ɗar ba..

Su Abba da umma ma godiya suka yiwa yaya kabeer da sanya mai albarka a yayin yin hakan ne umma ta kasa hakura ta ce mai

"Kabeer ina maka fatar samin nutsatsiya kamilaliyar mace ta gari wacce zata cigaba da ɗora ka akan hanyar alkhairan da kake yi"

Murmushi kawai ya mata ba tare da yace amin ba sai ya juyo gare ni ya kalle ni na wasu lokuta kaɗan next me zan gani sai kawai naga yaya kabeer ya zube a ƙasa yana kallon kwayar idanuna.tun kafin in yunkura ince wani abu sai naga haske ya dallare mu gabaki daya sai na tsinkayo muryar yay kabeer yana min magana

"Its been long da na haɗu da ke na fara ganin ki ne a gidan mu tun kafin ki gama sanin kanki na fada a soyayyar ki ne a lokacin da na fara ganin ki ba tare da nasan son da na kamu da shi a kan ki mai girma bane hakurin ki da hankalin ki su suka daɗa kara miki ƙima da daraja a wuri na kawaicin ki da kunyar ki su suka daɗa zurmani a soyayyar ki nayi rayuwata a wata kasar inda mata ke walagagi ta koh ina amma ban taɓa sha'awar koh da mace ɗaya a cikin su ba na dawo nan ƙasar na tarar da su iri kala kala amma basu taɓa burge ni ba koh daidai da second ɗaya na yi shekaru shida a kasar nan ana nuna min mata amma ban yarda na bude idanuwana na kalle su ba koh da na kwana daya ne farkon dawowa ta kasar nan a kwana na biyu da dawowa ta na gan ki a ranar a lokacin na fara jin wani abu da ban taba ji ba akan kowace mace na so in shashantar da abin amma yanayin yanda nake jin abin a rai na ya rinjaye ni da yawa koh da na zo na fahimci meke dami na na kasa furtawa kowq haka na yi ta jinyar abin har rana mai kamar ta yau da naga ya kamata in sanar da ke saboda mu yi maganin wannan abin da ya saka ni jinyar shekaru kusan shida da haka nake son nemar alfarma a gare ki da fatan zaki yi min wannan alfarmar...

Tsit hall ya dauka ni fargaba sauran jama'a fargaba tsoro ne ya kama ni dan ban san alfarmar me kuma yaya kabeer ke nema daga gare ni ba wanda har yake roko na ba amma koh ma menene wannan alfarmar bana jin zan iya hana shi dan so da kaunar da ya nuna min wani nawa na jiki na ma ba lallai bane ya nuna min bai kyamace ni ba bai nuna min banbanci ba hasali ma janyo ni yayi a jiki ya nuna kaunar shi a gareni akan zanen da nake so yake taya ni son abin da nake so amma ko ma menene zan yi mai wannan alfarmar koh da kuwa hakan na nufin bashi abu mafi soyuwa ne a gare ni

Yaya Aqeeb da ya daɗe da dawowa cikin hall din dan ganin fotar shi bai da amfani so yake ya ga iya gudun ruwar yayan nashi killa ba abin da yake tsammani bans hala ma ya sami ikon isar da sakon da zuciyar shi ke aiken shi tuntuni da haka ya dawo ciki da niyar sanar da ni abin da ke damin shi amma sai me sai kawai ya ga abin da yayan shi ke yi bai gama tsinkewa da lamarin shi ba sai lokacin da yayan nashi yayi wani abin da ya girgiza mu mu duka har da media wato

""Aisha Murad will you be my MTB for ever"??

Ban san lokacin da na zazzaro idanuna waje ba haka sauran jama'a ma suka zuba idanun su suna kallon mu in ban manta ba "Meant to be" yaya kabeer ke nufi wato so yake in zama matar shi kenan wannan tunanin ya sa na dago da sauri baki na na ɓari kamar ya san tunanin da nake yi sai ya tare ni da cewa

"Yes Aisha i mean what you were think will you please be my forever"?

Hawaye ne suka fara tsere akan fuskata dan wannan alfarmar kamar tana kokarin bin ƙarfi na amma fah nayi wa kaina alkawarin yi mai wannan alfarmar koh da kuwa hakan na nufin bashi abu mafi soyuwa ne a rayuwa ta dan haka in har shi bai ji kyashin yi min dawainiya ba toh nima kuwa bazan ki yi mai alfarmar nan ba juyawa  nayi muka haɗa ido da salma ta yi saurin jijiga min kai tana murna alamun in amince juyawa nayi zuwa ga ummi ai da sauri ta jijiga min kai itama Abbu kuwa murmushin manya yamin kawai alamun shima ya amince juyawa nayi na kalle yaya Ib da dariya akan fuskar shi daga min kai Umma kam baki har kunne ta ce min "yes dear" daga haka na maido da kallo na ga yaya Kb wanda yale tsugune tuntuni sai na rasa bakin magana kawai sai ga hawaye a fuskata

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now