Toh dama dole taron ya zama babba haka kasancewar dukkan mu mune manyan mata a wun iyayen mu daga ni har su salma da falmata a nan na hangi kannen na mu da kaya iri daya suma wani peach gown suka saka da wani head net aka naɗa musu hawa biyu kalar craem colour yaran sun yi kyau sosai dama ga su fa features din cikakun ƴanmata sai suka yi dal mazan kuwa duk suit suka saka yaya Kb ya saka wata irin dem read suit yaya Aqeeb kuwa ɗan kwalisa naive blue suit ya saka mai daukar ido yaya Ib kuwa royal blue suit ya saka yaya umar ma yau ba'a yi ustazancin ba dan ya haɗe ne cikin silver suit din shi wanda har ma ya so ya fi sauran kyau dan shi bai saba sakawa na dama toh yau da ya saka sai ya fito a ainihin barrister to be din shi

Kallon junan mu muka yi muka ce kamar haɗin baki sun yi anko da mu sai muka yi murmushi abu dai in ya zama na ƴan boko toh a tsare ake yin shi hakan ta kasance dan kuwa bayan an gama shigowa babbar hall din an zazzauna ne aka fara kokarin kiran mu salma ce ta fara shigowa tana murmushi kaɗan kaɗan sai haska ta ake yi da camera har ta isa inda zata zauna ana bin ta da tafi daga nan aka kira falmata itama ta shigo ana ta dallare ta da cameran har ta zauna ni ce ta karshe wanda nima haka aka min hasken camera da tafi suka rakoni har kujera na..

Daga nan aka fara budewa da adduo'i aka gama aka fara gudanar da liyafar a kaidance ga masu abin dariya sun yi ga masu rawa da waka ma duk sun zo sun yi nasu bajintar sun koma daga nan ne aka kira Abba ya bada speech din shi da nuna farin cikin shi akan kammalawar makarantar ƴar ahi wato salma da ƙawayen ta daga nan ne kuma mc ya ce salma ta fito ta taka rawa da Abbu abin dariya sai ta fito kawai ta ce tana alfahari da mahaifin ta da irin hidimomin da ya yi da ita kafin ta ɗora da cewa tana matukar son iyayen ta daga nan wurin ya kaure da tafi suka koma suka zauna bayan an musu hotuna da videos ita da su umma da Abba.

Bayan su falmata aka kira uwar kunya kasa cewa komai tayi sai kawai ta rungume Baban ta da mama da suka fito stage din ta saka musu kuka tana cewa yanda suka faranta mata a lokacin da bata yi tsammani ba itama inshaAllah lokaci na nan zuwa da zata faranta musu suma daga haka aka dauke su hoto har dai suma suka tafi

Abbu aka kira akan ya zo ya bayar da nashi speech din da ya fito sai da ya ma Allah godiya da nuna jin daɗin shi akan nuna mai wannan rana da yayi kafin ya dora da cewa
"Tun da Aisha ta taso ita da kanwar ta basu san wani abu mai suna dadin uwa ba dan tun suna yara mahaifiyar su ta rasu ta bar su maraicin kanwar Aisha wato farida wacce ta ci sunnan umman ta duk ya fi dami na dan Aisha ta san mahaifiyar ta kafin ta rasu ita kuwa farida sai dai a hoto dan tun a lokacin haihuwar ta ta rasu ba tare da ta kalli me ma ta haifa ba..rainon ƴaƴa na biyu ba abu mai sauki bane a gare ni duba da cewa su din mata ne basu da wani na gaba da su da zai koya musu komai daga ni sai ni sai lokacin da yayan su yaron kanin mahaifiyar su ya shigo rayuwar su suka sami abokin wasa tun daga cin su har shansu ni ke musu har ya kai matakin da ya kamata in nemo musu uwa da zata koya musu abubuwan ƴaƴa mata amma sai na ƙi gudun kar in auro matar da zata raba ni da ƴaƴa na koh kuma ta shiga tsakanin mu koh ta cutar min da su haka na hakura na jure na cigaba da kula da su har lokacin da Alhaji Habib da matar sa tare da makocin su Alhaji Amodu da matar sa suka shigo rayuwar mu tare da ƴaƴan su wanda suka dauke mu a matsayin zuri'ar su babu nuna banbanci tsakanin ƴaƴan su da nawa ƴaƴan
A lokacin ne na sami kwanciyar hankali dan daidai gwargwado sun rike min ƴaƴa na sun taimaka min da tarbiyantar su yanda kowace uwa zata yi wa danta sun koyawa ƴaƴa na abubuwan da ni ba zan taba iya koya musu ba matsayin da nake da shi a yau din nan su suka kaini shi da yardar ubangiji gashi a yau har an sanni kuma an taru dan a taya ni murnar kamaluwar makarantar ƴata yar amanata Aisha da haka nake so in ce muku nagode da soyayyar ku gare ni da kulawarku da taimakon ku a gare ni ina alfahari da ku a koda yaushe""

Daga nan ya dakata da jawabin shi bayan jama'a da dama sun share hawayen su wasu kuma idanun su duk yayi jajir aka dau tafi ni da ke zaune ina ta share nawa hawayen na tashi na sakko daga kan step din na iso wun Abbu da sasarfa na rungume shi na sake wani irin kukan tausayi wanda ya daɗa karya ma wasu zuciyoyin su a wurin mun dau lokaci a haka muna abu ɗaya kafin a kara tafa mana na dago kai na ina kallon Abbu na ce

"Abbu abubuwa da yawa ka bar su duk saboda ni da kanwata kaki yin wani auren duk saboda mu kaki jin dadin rayuwar ka duk saboda mu Abbu ni da farida muna mai farincikin yi maka albishir da cewa nan ba da daɗewa ba inshaAllah zamu saka ka yin alfahari da mu zamu saka ka yin farincikin da ka daɗe baka yi irin sa ba muna sonka Abbu fiye da yadda kake zato""..

Daga haka sai na kuma rungumar sa sai ga ummi ma ta zo ta rungume mu tana shesheka chan kuwa su salma da falmata suna kukan sukeyi shabe shabe mu kuka jama'an taro kuka aka saka tafi ana ta daukar mu hotuna daga nan ne yaya Ib ya matso kusa sa mu yana cemin yar lukata kin ga kin saka mana Abbun mu kuka koh haka aka ce miki ake yi bakauyiya kawai sai na yi ƴar karamar dariya suma suka yi duka wannan diramar yan jarida na ta aikin daukar mu mc da ke share kwallar shi shima dariyar yaya Ib ya bashi daga haka muka koma mazaunin mu

Ai zaman mu kenan sai muka ji muryar mc na cewa shi bai san wannan ba so yake mu fito gaba dayan mu wato graduant din mu taka rawa ya muka iya haka muka fito muka tsaya aka saka wakar zamani amma sai juyejuye muke yi dan bamu iya tabara a bainar jama'a ba haka dai muka gama muka koma mazaunin mu su hasina da ummi da yanmata biyun nan ne suka chashe rawar su ana ta daukar su..

Shigowa aka yi da cake din da aka mana a nan ne aka ba ma uban taron damar yin jawabin shi wato yaya Kb ya bayyana farincikin shi hade da godiya ma jama'ar da suka halrci taron ya kara yaba ma Abbu da namijin kokarin da yayi wurin tarbiyantar da mu daga karshe ya saka ma rayuwar mu albarka yana mai mana fatan cigaba da karatun mu cikin sa'a.

Hall din ya dau tafi daga nan muka yanka cake din muka sakawa junan mu a baki kafin mu sakawa iyauen mu da yan uwan mu sai yaya Kb da muk cika mai baki da cake din..

Chan wuraren karfe biyar aka fara interview da mu inda aka fara da salma akan me take son karantawa kuma a ina take son yin karatun amsar ta shine

"Ina son in zama human right archivist ne saboda ina sha'awar zamaimai kwato ƴancin ƴan ƙasa ta especially waɗanda ake zalinta ba tare da haƙƙin su ba kuma a nan garin Abuja nake so in yi karatu na dan koh wannan da muka gama ban so ba dan ya nisanta ni da iyaye na saidai saukin da na samu daya shine ina tare da kawaye na kuma aminai na" sai ta ɗan murmusa

Falmata ma ta fadi nata akan cewa
"Ina so in karanci business administration ne a cikin Abuja wato Turkish Universaty"

Ni kuwa nawa amsar banbarakwai ya ma wasu yayin da wasu suke min murna dan cewa na yi
"Art and designing nake son karantawa in da mahaifi na zai yarda a Egypt nake son cigaba da karatu na"

Kallon junan su suka yi falmata da salma irin dama yarinyar nan bata chanza ra'ayin ta ba ashe kallon su na yi na kashe musu ido na yi dariya..

Karfe shida aka fara presenting gifts kowa y ba da nashi muma muka bama junan mu kyautar yaya Ib wasu expensive gold wristwatches ya bamu
Yaya Aqeeb kuwa wasu irin attracting phones ya bamu kirar iPhone da pouches din su murna kamar zamu cinye shi

Yaya umar wasu sets din diamond earings hade da sarkokin su da zobunan su ya bamu a matsayin gifts din mu shima muka mai godiya

Babban yaya wato yaya Kabeer shi ya bamu kyaututukan mu daban daban salma laptop aka bata baka falmata kuwa silver colour aka bata nice aka bani wani abu rufe da wrapping sheet mai tsayi da ban san menene a ciki ba sai da ya zo yace min
"Go on"
Da sauri na bude me zan gani wani irin babban painting ne mai dauke da fuskata a yayin da nake murmushi ban san lokacin da na sake kujan farin ciki ba na bude baki na kenan da zumar yi mai godiya sai ya dakatar da ni yace
"Not yet"

Kawai sai ya fito da wani key ya danna sai muka ji kara gabadayan mu muka juya zuwa ga inda muka ji karar wata irin baby red hilanda muka gani an mata ado da balan balan kala kala sai ya ɗora min key ɗin a hannu na yace
"Happy Birthday Aisha Murad"

In total shock na tsaya ina kallon shi ba ni kadai ba har da yan jaridun da yan uwan mu sunji mamakin irin wannan kyautar..,,,,,,

*_🍒S,Ibraheem🍒_*

#Vote
#Comment

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz