Dariya kawai ta mana tana jijiga kafa bata kuma ce mana komai ba har muka iso wun expensive body care din dan ba gyaran suma kawai suke yi ba harta da manicure da pedicure hade da zanen lalle duk suna yi isowar mu ne ya ankarar damu daga surutun da muke yi fitowa muka yi muka kama hanyar shiga ciki

Mun dau kusan awowi uku ana silace mu kafin a mana wani irin extensive makeover wanda ya daɗa fiddo mu sosai a ainihin yanmatan zamani a yayin da ake mana ne nake karanta wani magazine a nan na kara cin karo da same painting din da na taba gani shekaru kusan uku da suka wuce wanda a lokacin ban sami damar karanta sunnan mammalakin painting din ba a yau da nake burin ganin sunnan ne kuma salma ta waufce magazine din ta fara min surutu wai tuntuni ina zaune ina karatun magazine har an gama ban sani ba nayi nayi ta bani in ga sunnan amma ta ki haka na fito ba tare da na san sunnan mammalakin painting din nan ba though ban ji daɗi amma shigar mu wata boutique na sayan kaya yasa na dan ware muka yi shopping din mu muka fito mun isa gida lokacin har shabiyu da rabi na rana ya buga saboda haka da zuwan mu shiryeshirye aka fara yi mana na liyafar da zamu tafi a can transcolt hilton Abuja

Falmata shigar royal blue dinner gown tayi tare da dora champaign gold turban ta saka royal blue set of earrings da wata yar siririyar chain din diamond a wuyan ta wanda mama ne ta bata a matsayin gift din ta ta saka zoben chain din da wani hand bracelet duk champaign gold colour ne sai ta dora champaign gold hill shoe mai igiyoyi wanda gown din nata ya rufe igiyoyin sai ya bada wani irin special attraction dama gown din an zuba mai white stones design sai ta rinka haskawa tana walwal..

Salma silver dinner gown ta saka sai ta saka sea blue earings da wasu irin bangles masu daukan ido kalar sea blue a daya hannun kuma ta saka wata irin silver wrist watch bata saka neckless ba saboda already a cike wuyan ta yake dan ta fi mu ƙiba ga shi nata rigar off shoulder ne ya budu sai ta saka combine silver and sea blue turban aka mata wani irin decoration na stones ta saka silver shoe mai dan tudu ba sosai ba..

Ni kuwa wata irin violet red gown na saka wanda yafi kama da cocktail gown tun daga turban dina har zuwa earings,hand bangle,ring,da takalmina deep black ne earings di na Abbu ne ya bani wanda yake haɗe da bangles da zoben shi turban din nima aka min mixing black and red sai na saka hill shoe black ban saka neckless ba nima dan bai cika burge ni ba..

Dukkan mu da yar pose din mu muka firfito dan kuwa kowacce da inda aka shirya ta ba wu daya aka shiryamu ba har kara mana makeup aka yi a fuskokin mu falmata aka saka mata matte pink lipstick salma aka saka mata matte peach lipstick wanda aka yi lining din shi da brown lip liner ni ma aka saka min red maroon lipstick..

Kowacce a cikin mu sai ta tsaya kallon yar uwarta tana yaba kyawun ta duk ni nafi kwadayin kyawun salma dan yanayin jikin ta sai ya sa kayan ya zauna mata daram a jiki

Fitowa muka yi zuwa falon kasa dan a sashen su salma aka shiryamu tun da muka sauko umma ke kallon mu da murmushi a fuskar ta ta fido wayar ta ta fara daukar mu hotuna bai mata ba ta sa aka kawo mata tablet din ta ta fara video coverage tun daga falon har muka shige motar da zata kaimu wurin saboda a lokacin duk yan gidan sun tafi mu kadai muka rage haka muka tafi umma na ta saka mana albarka har da addua'ar Allah ya kawo miji na gari sai wani nokewa muke yi kamar ba ma cewa komai nan kuwa har rigerigen cewa amin muke yi..

Cike wurin yake da yan uwa da abokan arziki tun daga abokan kasuwancin su Abbu da su Abba har ma da matayen su da ya'yan su wuri yayi albarka kamar wani liyafar wadanda suka gama makarantar jami'a haka aka shirya wurin fannin caterers daban masu bayar da drinks na nan kowane table daya zagaye yake da kujeru shida wadanda suka sha ado chan daga gefe kuma ga wasu rantsatsun kujeru har uku a jere wanda nake da tabbacin namu ne gefe ga wasu family sized table mai dauke da kujeru takwas takwas dayan iyayen mu ne dayan abokan aiki ne na kusa dayan kuma su yaya Kb yaya Ib yaya Umar yaya Aqeeb hasina ummi da wasu yanmata biyu da bamu san su ba..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now