Yaya ibrahim ya sami admission a university of kano wato Bayero university a inda yake karantar mass communication(aikin jarida) a lokacin da zai tafi kuka sosai ummi ta yi har da ƴar guntuwar zazzabin ta haka dai aka rabasu tana ji tana gani da farko ta saka abin a ran ta amma daga baya sai tazo ta ma manta sha'anin yara saboda shekarun ta tara kuma suma suna aji biyar kenan a makarantar primary kawancen su ita da  husna na nan sai ma abin da ya karu sun zamo kamar wasu ƴan uwan jini kusancin su yasa ake kiran su yan biyun umma koh da kuwa a chan gidan mu ne haka ake kiran su shi Abbu bai ma san irin godiyar da zai yi wa Alhaji Habib mustafa da matar sa Hajiya Amina haɗe da Alhaji Amodu da matarsa dan suna matukar kular mishi da rayuwar ƴar shi da yanda suka mishi kokari a rayuwa har ya kai wannan matakin ba tare da sun mai hassada koh kyashi ba

  Yaya umar ya mayar da hankali sosai a karatun shi yayi kokarin danne abin da ke ran shi dan ya san da karatun nan kadai zai iya aiwatar da abin da yake da niyar yi ba tare da an mai barazana ba bai cika shiga sabgar da ba nashi ba kullum kokarin shi shine ya kai matakin da ya dade yana kwadayin kaiwa a rayuwar shi dan haka neme nemen mata ba nashi bane rashin ji da kin mayar da hankali a karatu duk ba nashi ba ne hutun sati da yake zuwa yi ma ya rage ya mayar duk bayan wata saboda yanayin karatun shi yana buƙatar natsuwa

Akwai wani rana a makaranta ina zaune ina karanta wani magazine da falmata ta zo da shi na ga wani painting da aka rubuta inda aka yi shi a kasa abin ya burge ni harda ma dai painting din kamar zanen kaya ne na mata da na maza kafin a buga din nan

Kura wa magazine din ido na yi kamar na ga aljannah ta ganin na daɗe ya sa falmata matsowa ta wufce magazine din a tsorace na juyo na saka fuskar tausayi ina magana kamar ba zan yi ba na ce

"Haba babbar sister-in-law ya zaki min haka kih kin manta ke din matar yaya na ne to be pls ki ba ni magazine din nan in karanta wallahi da na gama zan dawo miki da shi"sai rokon ta nake kamar uwata.

Zugum tayi tana kallo na kamar taga talabijin kafin ta dora da

"Wai shin in tambaye ki mana Aisho"kasancewar sunan da take kira na da shi kenan a duk lokacin da zata min tsiya

Sai na ce mata ina jin ta

"Aisho wai ba kya jin wani iri ne da rayuwar da kika dorawa kanki akan abin da bai dace da ke ba  matsayin ki ba ƴa mace ace baki da abin yi sai zane zane da karance karancen kayan zane kamar wata namiji ni fah abin nan ya ishe ni kawai zuba miki ido na yi dan ban da yanda zan yi da ke ne in ba haka ba wallahi babu abin da zai saka ni barin ki ki mayar da hankali akan wanan shirmen sai ka ce kina namiji"ta ida maganar tana haki dan abin na ƙular da ita ganin ga ni mace amma sha'awar zane zane ne kawai a gaba na

Abin mamaki madaɗin ta ga nayi fushi koh na masife ta kamar yanda na saba sai ta ga akasin haka sai ma murmushi da na mata na ce

"Toh baaba falmata yanzu faɗa kike min ne koh da nasiha koh shawara kike ba ni"ina mai dage mata gira ɗaya sama
Ai ganin ban masife ta ba sai ta matso kusa da ni da sauri ta ce yawwa yar gari kin ga abin da nake so da ke shine ki duba lamarin nan da kyau ki gani kina kyakyawa maman Abbu guda yayan ummi kuma matar babban yayan mu watarana ai bai kamata ace ki zabi zane zane ba a matsayin ambition din ki bayan kin san wannan kwakwalwar taki zata iya daukar karatun alƙali koh likita koh dan jarida gasu nan da dama amma kice sai wannan aikin mazan ai sai babban yaya ya fasa koh kib fi son haka ne?

Da mamaki na ce hala kin manta da cewa shi babban yayan ne ke supporting di na kuma me halaƙa ta da shi da zaki zauna kina kirawo min shi a matsayin wanda zan zama matar sa watarana??

Sai kuma ta yi shiru tana kokarin daidaita kanta dan ta manta cewa ta so yin suɓul da baka saboda shi kan shi yaya kabeer din bai fito ya faɗa ba kawai ita ce ta hango hakan sai ta yi shiru kafin ta fara magana

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now