Mukan dawo hutun rabin zango in mun samu(mid time break)toh duk lokacin da muka dawo ba'a rasa abin fada game da yanayin girman mu a wata dawowar ce falmata ta fara al'adar ta (period) ba ma ta gayawa maman ta ba kawai cewa ta yi ta bata kudi tana so ta sayi wani abu yin duniyar nan mama ta yi don ta gaya mata amma ta ki haka kuwa ta hana ta da kukan ta ta tafi sashen su salma ta kai kara inda umma ta kirawo maman falmata tana ce mata

"Haba hajiya yanzu yarinya budurwa da ita tana makarantar manya ba kananan yara ba ta ce ki bata kudi tana bukata amma ki ce sai ta gaya miki me zata yi da shi uhum"

Jin haka sai mama ta ce "hmm umma kece baki lura da halayar ta ba tun da ta tafi makarantar nan ta kara koyon banzan halin miskilanci da rashin son a takura mata wanda a da ba haka bane"

Dariyar manya umma ta yi kafin ta ce "ai ba ita kadai bacw dukkan su ne suka koma haka girman kenan ai da changin wurin zama kuma kin ga yanzu sun fara dogara da kansu ba bu mai saka musu ido sun fara sabawa da rayuwar sirri shi yasa zaki ga bata cika son sanar da ke matsalarta ba yanzu dai shiga ciki ki ce ma salma ta baki kudin sai ki sayi abin da kike son sayan(ita umma ta gane me falmata ke bukata tunda ita ta koyar da su akan ilimin wannan abin)

Da mamaki mama ta ce hajiya ba dai yar yarinyar nan ta fara ganin jinin haila ba kike nufi??

Itama umma da mamakin ta ce "tohh dama matsala ne dan yar shekaru 11 zuwa 12 ta yi haila"??
A tsorace mama ta ce da gaske falmata al'ada take yi"?

Murmushi umma ta yi kafin ta ce "kwarai kuwa Hajiya falmata al'ada take yi ai ba abin mamaki ba ne salma tun suna shekara goma ta fara yanayin jiki daban daban ne kin ga ita Aisha har yanzu bata fara ba ina ganin ita sai ta kai shabiyar kafin ta fara toh ai ba abin mamaki bane koh ba haka ba"

Jijiga kai mama tayi cikin gamsuwa tana mai yiwa umma godiyan abin da ita ta kasa yiwa ƴarta wato koyar da ita tun kafin hakan ta faru da haka suka rabu

Satin mu daya muka koma makaranta a chan salma ke min gulman ai falamata ta fara period da mamaki na kalle ta na ce haba da gaske shine bata gaya min ba sai tace bar munafuka wai ita nan kunya take ji sai muka yi dariya a daidai lokacin da ta shigo dakin ta gan mu ashe ta ji abin da muke fada sai t ce mall dai ya ce mai gulma dan wuta ne in kun fa dama kuyi ta yi munafukai kawai tayi tsaki ta zauna dariya muka saka mata kawai muka share ta

Tun daga nan salma da falmata ke yin monthly period din su yayin da nikuma har lokacin ban fara ba kuma abin bai wani dami na dan har seniors din mu da ke final year wasu basu fara ba ko kadan bai dami na

Wani abu da na fara lura da shi tattare da su falamata da salma shi ne yanzu sun fara maganganu marasa ma'ana da ɗa'a wanda hakan kan dame ni dan kuwa akwai wata isashiyar yarinyar da ke kawo musu litattafan hausa a boye suna karantawa in na musu magana sai su ce ai dan ni ban gama girma bane toh hakan na ɓata min rai sosai sai in fita a harkar su dan ƙashin kansu sai suka fara ragewa ganin kamar nuna banbancin da suke min ya na yawa kuma suna tsoron kar in mun koma gida in faɗa a musu faɗa da kyar suka rabu da wannan litattafan dan sai da na ma yarinyar tass na ce in ta yi wasa toh wallahi sai na kai kararta hukumar makarantar kuma ta san kora ne za'a mata dan dama scholarship ne take amfani da shi daga wun kawayen ta muke ji ai tana jin haka ta fara kama kan ta yawan karatun har yasa abin da ya kaimu makarantar ya fara tangarda a wurin su salma da falmata dan kuwa sun fara wasa performance din su ya fara raguwa koh a test ne makin su baya kaiwa kamar da ganin haka yasa suma suka fara kama kansu sai daga baya suka yi dana sanin abubuwan da sukayi a term din suka bani hakuri muka koma kamar da

Gab da exams din mu na third term ne na fara ganin wani muguwar change change a jiki na dan a lokacin daya nawa girman ya zo muna gama exams din mu ana gobe za'a zo daukan mu na fara ganin nawa period din abin mamaki wai nima na yi girma sai  da nayi kukan murna at least nima za'a fara saka ni a layin manya koh da na gaya ma su salma suma murnar suka yi min falmata ce ke bani pad in saka itakuma salma maganin ciwon cikin da su a lokacin sun manyanta a wannan bangaren

Mun dawo gida hutu kenan muka tarar da gidan a cike gidan mu ga su ummi suna hutu yaya ibrahim ya gama makaranta chan gidan su salma ma yaya kabir ya dawo gaba daya yaya Aqeeb ma ya gama makarantar saura na gaba

Murna kan murna haka muka yi hutun mu wanda kusan rabin shi a gidan mu muka yi a lokacin ne kuma yahaya ya bayyanawa Abbu nufin shi akai na da kuma neman alfarmar idan na gama makaranta zai fara zuwa wuri na Abbu ya ji dadin hakan dan har ya bashi tabbaci amma da sharadin in ban amince ba toh bazai min dole ba yayin da wata shakuwa ta shiga tsakanin falmata da yaya ibrahim shi kuma Aqeeb ya fara min wani gani gani tuntuni na harbo jirgin shi amma na yi kamar ban sani ba

  Fannin yaya Kabir kuwa abin ba'a cewa komai dan kuwa haduwar mu sau biyu amma na rasa dalilin da yasa yake min kallon kuril a duk sanda na je gidan su wannan dalilin ya sa bana son zuwa part din su salma in na tafi sai dai part din su falamata shi kuma wai so na yake yi sosai ashe falmata ta gano hakan itakuma tana nan tana fama da ciwon son da take mishi a cikin zuciyar ta amma ganin bai ma san tana yi ba yasa ta bar ma kanta kuma ta ki gayawa kowa dan duk cikin mu ta fi mu tsananin kunya da kawar da kai a abin da take so amma ta sa a ranta duk hanyar da zata bu dan ta same shi zata bi saidai in har bata yi sa'a ba toh sai ta hakura wannan alkawari ta yi wa kanta itakuwa uwar gayyar salma komai da ke faruwa bata da masaniya a kai abin da ta sani shine akwai shakuwa tsakanin ni da yaya Aqeeb falmata da yaya ibrahim bayan wannan bata san cewa yaya kabeer na mutuwar kaunana ba dan shi kanshi baya nunawa kawai dai jiran lokaci yake yi sai ya fallasa min amma a ganin shi har yanzu ni din yarinyace ban kai matsayin da zai fara min zancen soyayya ba

Ana wata ga wata kulawar da yaya ibrahim ke bawa falmata hakan na konawa ummi rai ba kadan ba dan kuwa hae ya kai matakin da in taga falmata a gidan mu ta rinka jan yaya ibrahim da surutun shirme kenan bayan ba haka take ba miskikancin tsiya ne da ita kamar ɗiyar sarki bai dau hakan a matsayin wani abu ba amma abin da ake cema babba babba ne Abbu ya harbo ta tsab dan duk a cikin mu ya fi bada karfi wurin kula da ita dan ya san nan gaba kaɗan wani irin mummunan zuciyan banza zata yi.......

*_🍒s,ibraheem🍒_*

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now