Bayan ta mana nasihar ne ta fiddo da pad din ta mikawa salma hannun ta akan ta bata pant din ta ta mika mata itakuma umma ta bude ledan pad din ta cire ta fara sakawa tana mana bayani dalla dalla har ta gama ta mikawa salma pant din akan ta je ta yo wanka sai ta saka tana shiga bayin umma ta kara ja mana kunne ta kuma jadada mana akan dole sai mun kara hakuri da salma dan zamu fuskanci changi daga gareta kafin muma mu kai matakin da ta ke ciki amsawa muka yi muna jimami da haka ta bar mu muna ta maganar abin da falmata

Lokaci na dada ja abubuwa na ta sauyawa a rayuwar mu changi kam daga wun salma mun ganshi har mun saba ko dan kuwa ji take yi kamar ita ce babba da mu ko ma kamar uwar mu ta manta cewa shekarun mu daya dan yanzu muna neman cika shekaru shadaya(11)  cikin abubuwan da suka faru har da cigaban Abbu dan kuwa bayan aikin da ya ke yi da kamfani shagon sa na kasuwa ya hayayyafa ya karu har zuwa shaguna hudu manyan gaske masu zaman shagon Abb na tun asalin wato yahaya da zakir sun rike amana gaskiya a halin yanzu daya daga cikin shagunan Abbu shi ke kula da shi dayan kuma yahaya ga karin masu aiki da aka samu lokaci lokaci in yaya ibrahim ya dawo hutu yakan zauna a shagon Abbu wanda yake cikin wuse zone 2 in kuma ya koma sai isma'il ya cigaba da aikin dan yanzu shekaru sa goma sha shida wanda yayi daidai da shigar sa ajin karshe a makarantar sakandire mu kuma har mun sami makarantar gaba da primary muna matakin ajin farko a wani makaranta mai suna *NEW HORIZON*  da ke garin Minna Niger state makaranta ne na ƴaƴan masu da akwai dan a lokaci nima ba laifi Abbu na ya fara zama hamshakin kanshi toh dama chan Hamshakin ne yanayin rayuwa ne ya maida shi haka

  Yaya aqeeb shi ne da na biyu a ahalin su daga babban yayan su mai suna kabeer wanda yake kasar china yake karantar gynaecology Wato likitan mata

Yana ajin shi na karshe kenan ban san shi ba ban taba ganin shi ba dan ba kasafai muke hirar shi ba ita kanta salma ba wani sanin shi tayi sosai ba sai dai a hoto kokuma in ya zo hutu su hadu a wun cin abinci yadan yi mata wasan da zai yi wanda baya wuce yar lukuta da yake ce mata bayan wannan bata wani san abu mai zurfi game da yayan nata ba

Daga shi sai yaya Aqeeb wanda a yanzu shima yake matakin karshe a makarantar sakandire da ke chan cikin garin Abuja dama dama shi in ya dawo hutu mukan hadu dan har mun saba sosai saboda kallon dan uwa na nake mai shima kuma ba laifi baya duba cewa ni din ba yar gidan su bane yanda yake yi da kannen shi haka nima yake min

Yaya umar yayan falmata kuwa yanzu ne ya ke shiga matakin farko a jami'an Abuja wato University of Abuja wanda ya kasance babu ruwan shi shiru shiru kuma bai cika son hayaniya ba koh da ya kammala secondary school din shi Abba ya so ya tura shi china wai ya hadu da yaya kabeer amma ya ce a'a nan ma Abuja ya ishe shi ya yi karatun shi ya suka iya haka suka bar shi aka samo mai Admission ya fara zuwa sati sati yakan dawo gidan dan ya kasance ne kamar ustazu yanayin shi da rike mutuncin shi ya banbanta da yanayin samari ƴaƴan masu da shi na zamanin nan Law yake karantawa kuma yana da buri babba akan ganin ya cimma kudirin shi a rayuwa(koh menene wannan kudiri oho)

Ummi da hasina kawance ya musu dadi girman jiki kamar hura su ake yi suturu iri kala daban daban su ke sakawa suma yanzu shekarun su shida shida kuma suna aji na biyu a matakin primary basu yarda sun kulla kawance da wata ba daga su sai su ga wani irin jiji da kan da suke fama da shi Abbu yana kokarin shi sosai wurin ganin ya tankwasa ummi amma ina jin kan nan sai hakuri

Abbu a ko da yaushe in Abba ya mai maganar yin aure toh bai cika dawowa gida cikin walwala ba dan shi gudun muguntar mata yake yi ace yayi aure amma wata macen ta yi kokarin shiga tsakanin shi da ƴaƴan shi koh ma ta cutar da su shi kuma bazai dauka ba shiyasa ma baya maganar kara yin wani aure saidai yace mai Alhaji zan duba koh da kuwa baban su falmata ne ya mai tambayar amsar daya ce dai

Ana haka ne muka tsunduma tsundum a karatu babu ji babu gani dan kuwa kowa dan jin kai ne a makarantar dalilin da ya sa bamuyi kawa koh daya ba kenan sai dai yan mutuncin da za'a gaisa sama sama lokaci zuwa lokaci 

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now