"Mamana taho kumu tafi gida in kun ci abinci sai mu tafi koh da zuwa karfe biyar ne na yamma

Tsabar rashin hakuri irin nawa sai na tare shi ta hanyar cewa
"Abbu har sai dare yayi kafin mu tafi ni ni nidai"

Na bashi dariya sai yace mamana ai saboda bana son kuyi fashin islamiyar ku ne yau kinga in na kai ku sai in yiwa malamin ku magana koh da 4:30 pm ne sai mu tafi chan gidan nasu koh ya kika gani??

Nikam tsoron zuwa islamiyar nake ji amma na san idan zan fada cewa zai yi saboda zuwa gidan nake karya alhalin ba hali na bane haka dai na yi gumm ban kuma cewa Komai ba har muka kai gida ni da ummi mun gama komai muka kama hanyar zuwa Islamiya a daidai gate din makarantar nafara tsorata amma na yi shiru har dai na shige ajin ina dar dar

Inda Allah ya taimake ni shine yau basu zo ba dama wai sai an kawo su makarantar in ba haka ba ba zuwa suke yi da kansu ba toh da naga basu zo ba sai na sake jiki na nayi bitar karatun da aka min jiya malamin ya kara min

Ana tashin mu sallar la'asar Abbu ya zo daukan mu dama ya ma malamin makarantar bayani da zuwan shi da kawai muka wuce

Da zuwan mu gida na yi sallah na chanza kaya na duk sai doki nake faman yi

Abbu na ta farinciki na fara walwala na sami kawaye
Muka fito muka tafi bakin titi inda muka tsare a taxi ni na gaya ma mai taxin inda zamu tafi ya fadi kudin kafin ya ja mu muka tafi sai federal housing a daidai nan ya sauke mu yace mana mun kai muka firfito Abbu ya biya shi kudin shi

Sai kuma aka bar mu da kame kame saboda wurin dai kusan zan iya cewa shiru yake da kyar muka sami wani yana tafiya a hanya muka tambaye shi gidan da akayi rasuwa jiya sai ya ce mana mu yi tafiya zuwa karshen layin sai mu yi kwana toh akwai gidaje a wurin sai mu duba gida mai lamba 44 a nan aka yi rasuwar

Muka mai godiya muka tafi da kwatancen shi muka iso gidan wanda yake gida ne na masu kudi dan babba ne ga kyau mun bata lokaci sosai kafin a bar mu mu shiga gidan har mun cire ran za'a bar mu mu shiga

Ko da muka shiga sai muka ga fanni biyu mun rasa wanne ne zamu shiga aiko sai ga hasina kanwar salma ta fito daga daya fannin tana hango ummi ta zo tana ta kiran sunan ta wai tazo su tafi kafin su bar wurin sai ga wasu maza sun fito kusan su biyar suma din ta'aziya suka zo yi a nan ne Abbu ya tsaya suka gaisa da su ya musu ta'aziya sai  ya ce musu ai yar shi ce ta ke gaya mai rasuwar da mamaki suka ce wacce a ciki sai ya nuna musu ni yace ai makarantar mu daya da su

  Sai daya a cikin su yake cewa
"Ai jiya da yaran suka dawo basu bar su sun huta ba sai labari suke yi wai sun yi kawa a makaranta jiya sunan ta Aisha Murad"

Abbu ya yi murmushi sai mutumin ya raka bakin shi kuma ya wa Abbu bismillah zuwa ciki muna shiga ya sa aka kira wata mata wacce da ka ganta ka ga falmata domin kamanin nasu har ya baci da ta iso sai mutumin ya ce

"Hajiya ga baki nan mun yi sun zo ta'aziya ne kuma wannan ita ce kawar su yaran nan da suka ce sun yi jiya a makaranta"

Matuka matar ta ji dadi don har take kara godiya kafin ta ce in zo mu shiga suna ciki

Tafiya muka yi su kuma su Abbu suka cigaba da magana a nan Abbu ke sanin cewa shine mahaifin mai rasuwar kuma baban falmata har yake gaya mishi ai shi dan asalin maiduguri ne a wani yanki mai suna Gonin goza kasuwanci ne ya kawo shi nan shine ya samu uban gida mai mutunci da daraja dan adam har ma ya bashi wani matsayi a ma'aikatar shi ya jawo shi ya hada da iyalin shi ya kuma bashi yarda da aminci

Sai yaba mai yake yi ya dora da cewa ai falmata ce yar shi ta biyu akwai babban yayan ta da ke karatu a wani makarantar kwana na sakandire a cikin Abuja sai falmata da kuma kanin ta da Allah ya ma rasuwa a jiya wanda ba zai wuce shekaru uku ba zuwa hudu

Abbu ya dada yi mai ta'aziya shima ya bashi labarin cewa ai shima dan maiduguri ne ya gaya mai komai da ya faru da shi da yanda ya zo nan ya kafa kasuwancin sa

Shima ya mai jajen abin da ya same shi yake tambayar shi toh ina maman su Aishan

Sai da Abbu ya dan yi shiru kafin yace ai ta rasu tun ranar da ta haifi farida wanda wanda wanda sunan ta aka mayar ma yarinyar

Da tausayi baban falmata yake kallon Abbu ya ce Allah ya jikan ta haka dai suke ta tattaunawa akan sha'anin rayuwa

Mu kuwa da muka shige ciki dakin su direct aka kai ni da shiga na kawai sai suka fasa ihu sun ma manta rasuwa aka yi (yarinta kena)

Muka rungume juna suka fara min surutu wai me zan ci a kawo min na ce ba kai suka bata fuska su a dole sun yi fushi sai na ce toh a kawo min koma menene salma ce ta fita ta dawo da abinci a babban tire da cokula wai mu ci haka muka zauna muka ci tare sai annishuwa muke yi sai suka tambaye ni halan me yasa ban zo ba da yan ajin mu suka zo

Amsa na basu da ai tare da Abbu muka zo kuma shi ya hana ni yawo in ba tare muke ba shiyasa ban zo ba dazu sai na ce ai har da ummi muka zo amma sun shiga wani wuri ita da hasina

sai suka ce ai dakin su suka tafi a nan dai muka sha hirar mu salma ke ce min ai su Abban ta sun yi tafiya tare da umman su kenan ragamar gidan a hanun baban falmata yake muka sha hirar mu kamar kar mu rabu sai ga maman falmata ta shigo kira na wai in zo mu tafi

Suka rako ni har falon inda suka gaida Abbu sai ga su husna ma sun fito haka muka rabu akan zamu hadu gobe a makaranta ni har ma na manta da maganar yaran islamiyar mu da nake so in gaya musu har mun yi nisa na dawo na gaya musu ai ko suka ce in Abban su ya dawo zasu ce mishi ya dawo da ni makarantar su su dai iyayen mu na ta jin mamakin shirmen mu da haka muka tafi gida

Pls manage walahi schedule dina na yau is very tight ne hope zaku karbi uzuri na

_*🍒s,ibraheem🍒*_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now