A haka aka share kwanaki bakwai ana zuwa gaisuwa a nan ne kuma mahaifin mu ya yanke hukuncin zuwa ya dauko yaya Ibrahim daga makaranta saboda saura kwanaki biyu suyi hutun zangon akan in sun dawo nan Abadam sai mu bar garin baki daya

Hakan ta kasance bayan ya dauko shi ya mai bayanin abin da ya faru da kuma barin garin da zamuyi

Makota da abokan arziki su suka ma mahaifin mu addu'oi da fatan alkhairi akan Allah ya bashi sa'a a inda zai zauna

Abubuwan da mahaifin mu ya tsira da shi shine gidajen da ya mallaka wanda ya sayar ya karbi kudadensa ya hada muka bar garin a nufin in mun kai inda zamu je sai ya fara kasuwancin sa tunda shi din dan kasuwa ne bazai iya zama haka nan ba

Bamu tsaya ko ina ba sai wani gari da ake kira da birnin tarayya wato Abuja a wani gari mai suna kubuwa

A ranar mahaifin mu ya fara cigiyar inda zamu zauna aka ce mishi sai dai zuwa gobe

Rasa wurin kwana ya sa dilalin da aka hada shi da shi ya bamu aron wani daki cikin dakunan shi na gida akan mu kwana zuwa gobe

Mahaifin da yaya Ibrahim ne suka mai godiya ya gayawa matan shi a nan suka kawo mana abinci ba laifi sun tarbe mu sosai

Su suka ce ni da ummi mu shigo mu kwana tare da su saboda bai kamata a ce mun hadu duka mu hudu a daki daya ba ga namiji da ya girma sosai

Mahaifin mu ya musu godiya da haka muka kwana bayan sun saka mu mun yi wanka sai tausayin ummi suke yi saboda a shirmen labarin da n basu sun gano cewa bamu da uwa

Washegari ma haka suka mana hidima Kamar dai sun san mu a yayin da mahaifin mu da yaya Ibrahim tare da dillalin suka bar gidan domin zuwa nemo gidan  da zamu zauna

Sun dan sha wahala duba da irin garin da mutanin da ke rayuwa a cikin ta sai da rana ta fado kafin su dawo gida

A nan nake jin wai sun sami gidan ne a wani wuri mai suna federal housing a cikin 2/1 market

Toh a ranar muka bar gidan duk da rokon da sukayi akan mu tsaya har gobe mahaifin mu ya ki ya ce wahalar da suka yi da mu daga jiya zuwa yau ai ko naka iya abin da zai maka kenan  da haka muka rabu dama ba wasu kayayaki muka zo da su ba face kayan sakawar mu

Muka dau taxi zuwa 2/1 market a inda gidan mu yake muka tsaya mahaifin mu ya sallame shi mukuma muka shige ciki a inda muka tarar da wani daki mai kyau wanda yaya Ibrahim ya ce mana mu shiga ciki nan ne namu ni da ummi dakin Alhamdulilah komai mai kyau shima yaya Ibrahim akwai dakin shi daban kafin a shigo falon inda namu yake mahaifin mu kuma nashi a bayan namu yake sai wani dakin da babu komai a ciki

Ashe bayan sun sami gidan sai da suka tsaya suka dan mana sayayya suka saka a gidan kafin su dawo chan gidan

A bakin yaya Ibrahim nake jin komai toh dama mahaifin mu ya saka shi yi mana abinci daidai mu kafin ya sayo mana abin da zamuci shine ya kira ni wai in shigo in koyi yanda ake yin girki gani katuwa amma babu abin da na iya kasancewar shi makarantar kwana yake ni kuma ina yar primary

Sai da muka dau Kwanki hudu kafin abubuwa su yi mana daidai saboda an samo mana makarantar da zamu na zuwa yaya Ibrahim ma an samo mai makarantar da zai tafi ya cigaba da karatun shi dan har ummi an saka ta makarantar itama mahaifin mu ya samu wani karamar shago ya kama haya akan zai fara sayar da abubuwa irin na maza da mata shaddoji da yadi da atamfuna

Ranar da zamu fara zuwa makaranta a ranar ne shima zai fara zuwa kasuwancin sa shi yaya Ibrahim har an kai shi makarantar tun ranar lahadi.

"Mamana.. Mamana"
"Na'ama Abbu ina zuwa"

"Amma dai kin san kun fara makara koh'"
"Abbu ummi nake shiryawa yanzu zan fito"

Shiru ya mana har lokacin da muka fito ni da ummi sanye cikin sabbin kayan makarantar mu wanda yake riga ce iya gwiwa sai doguwar safar da muka saka ya zo mana har gwiwa sai sabbin takalman mu bakake muka kafa hulunan mu na makarantar(Barrett) da abin sunan mu (name tag) goye da jakan mu da lunch box din mu muka fito dama Abbun mu ya saba yi mana girki tun bayan rasuwar ummar mu toh koh a yau din shi ya hada mana abin kari da wanda zamu tafi da shi makaranta

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now