*_THE MJ RESIDENT_*

  Horn yake dannanwa kamar wani sabon kamun hauka

  Da sauri mai gadin ya farfado daga ƴar karamar baccin da ya fara kusan mintina goma da suka wuce harda yayi ƙoƙarin gani baccin bai dauke shi ba gudun cin mutuncin da zai iya fuskanta daga wurin wannan ɗa marar ɗa'a da mutunta mutani

Sauri yayi ya bude gate din a daidai lokacinda aka yi horn din a karo marar adadi

Tun kafin baba mai gadi ya gama buɗe gate din ya matsa tuni ya danno kan motar da wani irin speed saura kaɗan ya ingiza baba mai gadin ba dan ya matsa ba toh tabbas da gadon asiti ya samu baƙo

A zuciye yayi parking motar ya fito yana dumfarar baba mai gadi wanda a lokacin har ya fara karkarwa domin kuwa zufa ya fara keto mai

Yana zuwa ya fara sauke mai kwandon masifa da bala'i ta inda ya shiga ba ta nan yake fita sai da ya dau lokaci yana zazzaga ma wannan tsohon da zai yi jikan jika da shi kafin ya ɗora da

"Matsiyaci ai bai iya samun wuri ba in ba haka ba har wani bacci kake da lokacin yi a matsayin ka na ƙasƙantacen mai gadin wannan gida iye?ka bani amsa koh dan ku talakawa baku iya samun wuri bane?

Wannan ya zama na farko kuma na ƙarahe da zan dawo gidan nan ina danna horn kana ɓanata min lokaci kafin ka zo ɓude min gate ka fahimce ni ko a'a? "

Abin tausayi wannan tsohon da yake ta faman bashi hakuri yana roƙan shi da ya yafe mai yayi saurin girgiza kai

"Ka ga tsiyar ya zaka jijiga min kai kamar wani zombie ka buɗe baki ka bani amsar abin da na tambaye ka"

Ya karasa faɗa yana daka mai tsawa

"E.. Eh..Ehhhhh na ji ranka ya daɗe"

"Nonsense illiterate coward mtsw"

Ya ja wani irin doguwar tsaki yayi gaba

Shi dai baba mai gadi bai san ma'anar abin da ya gaya mai da harshen nasara ba amma ya san ko ma dai menene abu ne marar kyawun ji duba da yanda ya ja tsaki kafin ya bar wurin

  Baba mai gadi ya koma post din shi ya zauna shiru za tausayi yana jinjina al'amari irin na gidan nan tun da yake bai taɓa aiki ya fuskanci irin wannan matsala da ƙasƙanci irin wannan ba daga ɗan ƙanƙanin yaro da yasan ya yi jika da shi ba

Oh duniya yanzu neman halalin kan ka ya zama hanya da za'a yi amfani da shi a ci mutuncin ka a ƙasƙanta ka ciki har da wadanda basu kai yi maka kallon banza ba amma saboda Allah ya haskaka tauraron su sai su wulaƙanta ka

Allah ya shige mana gaba ya tsirar da mu da mutuncin mu

Yana shiga cikin babbar parlorn ya fara ƙwala kiran ma'aikatan gidan yana faman basu order

"Martha marthaaaaa"
Ta fito da sauri har tana tuntuɓe ta iso gare shi tana haki ta ce

"Ye...yeess sir" har numfashin ta na sama sama

"You disgusting fish where were you that you couldn't answer me on time you made me strain my voice in calling your ugly name? Huhh?

Tana ɓari ta ce mai
"Am so sorry sir i was trying to clean up the restroom i didn't hear you sir pls forgive me"
  Ta ƙarashe tana durƙusar da kanta ƙasa

  "Idiot" ya cigaba da tafiya yana bata order

"" go get my stuffs and call barde to come and clean that car"
"Ok sir"

Ya wuce zuwa sama yana sake kiran wata mai suna Tina yana mai bata dokar ta saka mama hari ta hado mai coffee ta kawo mai

Ya haura zuwa dakin shi da zuwan shi ya tuɓe ya yi cikin toilet din shi da ke cike da kayan more rayuwa ya shige cikin bathtub ya yi kwanciyar shi yana hararo irin farin cikin da mahaifin shi zai yi in har ya ji abin arziƙin da yayi ya murmusa yana ƙara jinjina ma kanshi da alfahari da ilimin shi

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now