"Hmmm dr kenan a wurin ka ne hakan ke nufin risk amma ni a wuri na ba hakan bane saboda na gama lura kana so tausayin ahalin ka yayi overshadowing professional morals din ka shi yasa ni kuma na zare hannuwana a tafiyar ka"

"But Hajiya ina jiye miki matsalar da zai kai ya kawo kin san yanayin abin nan ke kadai na bama wannan labarin"

""A'a dr ka daina kirawo min matsala aimiscun farko na gaya maka yanda za'a yi amma me kayi you put a blind face to what i said har ka doɗe kunnuwar ka akan shawaran da na baka"
"Koh ba'a yi haka ba dr"??

"Jin labarin ka yasa na ce zan taimaka maka because na lura kana an saka ka a ethical delmar amma baka yi duba da hakan ba"

  ""Hajiya walahi ba haka bane ba kuma wai na yi ignoring shawarar ki bane i was hoping that abubuwa zasu lafa bayan na tura musu video clips din nan in yaso sai in yi involving security agents akan maganar but seeing what happened earlier i have to go into a hide ni da family di na"

"Hmm dr kenan toh ka ce ma asibitin me"??

Shiru yayi na dan wasu lokuta kafin ya ce

"I know what to da kar ki damu amma what about the patient? '

"Wannan ba abin damuwa bane i agreed to take the burden all alone ni kuma na san yanda zan yi da ita kar ka damu"

"Toh na gode hajiya zan miki magana duk yanda abin zai kasance"

Da haka muka rabu toh ko bayan kwana biyu that was Friday da ya kira ni sai yake gayamin ai presently yana Singapore tare da familyn shi ashe shima ya riga da yayi visa harda ita patient din akan zasu bar kasar har bayan komai ya lafa in yaso daga chan sai yayi informing security agents da hospital management din akan gaskiyar al'amarin da dalilin shi na yin hakan daga karshe ya sa a yi cigiyar family din patient din

Amma ganin na dauke ta sai kawai ya haɗa kan matarshi da autar shi suka bar ƙasar temporary ba tare da ya sanar da hospital management din ba

Toh a haka yake ce min idan na gama treating din ta ta dawo normal mun samu bayanai akan ta sai mu yi raising maganar zuwa ga hukuma

Muka yi sallama akan zamuna communicating time to time

"Kin ji yanda muka yi da dr"

_Wai wani cakwakiyar sai a ƙasar  wato kawai baka da ƴancin yin rayuwar farinciki idan kayi exposing hidden truth sai dai ka koma kana ɓoye ɓoye kamar kai ne marar gaskiyar saboda kana neman kan ka da lafiya_

  _Allah dai ya sa mu dace_

A cikin zuciya ta nake ayyana wadannan maganganun

"Are u with me"

Firgigit na juyo
"Ina tare da ke ma'am kawai ina tunani ne yanda duniyar ta zama especially a nan ƙasar mu Nigeria shikenan bazaka fadi gaskiya ka kwana lafiya ba sai an nemi salwantar da rayuwar mutum"?

"That is the present resection da muka tsinci kan mu a ciki wanda dole a  ƙara yawan tsaro a ƙasar har da tsatsaurar doka akan duk wanda aka kama da yin wannan act din wato blackmailing da treats to an innocent citizen"

"Haka yake kuma dole media su ƙara daura bambarar yaƙi da ire-iren wadannan mutanen by exposing any single misbehaviour da aka kama mutum nayi ba tare da cewa sai an tsaya samo wasu evidence ba by so doing wasu mutani har da wasu media presenters zasu falga su yi taka tsantsan da wannan da aka kama da misconduct

Da haka ta ce min taso mu haura tana nan na bar ta a zaune ma ba laifi muna samun great improvement

Haurawa muka yi tare da ita zuwa dakin


🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now