"Dr ka cigaba da addua'a Allah zai kawo maka mafita don't loss hope kaji? "

"Nagode hajiya i will think about what we discussed"

Na yi shaking kai na a haka muka rabu

  Bayan fitar shi ne nikuma na aiki daya daga cikin securities  din na ce  ya kirawo min baballe bayan baballe ya zo ne na sa ya kirawo min Anthony

Shi dama Anthony ya kware wurin raha da wasa yana shigowa ya fara "maman mu me zamu samu anshe kana kiran mu"cikin gurbatacciyar hausar sa wanda ya saka kowa darawa daga nan ya karasa shigowa office din yana mai cewa ""yannmatan mama kun ji wei likita zai yi releasing naku gobe koh..suka kara darawa domin sun san tony(anthony) da barkwanci though hausar bata zauna mishi ba

Mun gaisa da ba'a na nuna musu wurin zama suka zazzauna

dukka hadasu nayi na kalle su na wasu lokuta domin ni kaina ban san ta ina zan fara musu bayanin nan ba

  "Baballe nasana jiya ka ga shigowar dr Ladan asibitin nan wuraren karfe 3:00 na rana koh ba haka bane"?

"Eh hajiya na gan shi dan har tambaya na yayi akan ban tafi gida ba har yanzu na ce mai sai anjima kadan saboda Ina jiran wani aike ne da nayi"

Na juya zuwa ga anthony na mai same tambayar da na yi wa baballe shima amsa min yayi da eh shi ya budewa likita gate da zai shigo asibitin

  "Toh ku saurare ni da kyau ku ji abin da zan gaya muku bana son ku min bahaguwar fahimta kuna ji na"??

Suka jijiga kan su

    Tiryan-tiryan na fara musu bayanin abin da likita ya gaya min kafin in dora da ce musu
""Ina so wannan maganar ta zama sirri a tsakanin ni da ku kawai kar ku bari wani ya ji koh da nan gaba wani abu zai taso ku yi kokarin boye wannan sirrin kun dai ji yanda halin rayuwar familyn dr yake ciki koh"?
  Cikin jimami suka girgiza kai tare da yi min alkawarin zasu yi kokarin riƙe wannan amanar at any cost

  Hakan da suka yi ya sa na sami relieve at least i won't carry the whole burden all alone akwai wadanda zasu iya bayar da shaida koh da wani abin zai taso nan gaba wanda bana fatan hakan ya faru

Na sallame su tare da yi musu godiya mai yawa

"Toh koh da aka cigaba da injecting yarinyar nan da allurai iri kala daban daban hankali na baya kwanciya saboda a kullu yaumi kallon ƴar ciki na nake mata ban sani ba koh dan ban da ƴa mace ne shiyasa tausayin ta ya ninku sama da yanda nake ji akan sauran patients di na"..

Haka kullum birkicewar yarinyar nan ke canzawa kuma kullum sai dr Ladan ya dau videon ta ya tura musu
Duk wannan budirin nurses din mu are not aware of it saboda a nasu tunanin wata ce very close to dr Ladan shi yasa yayi abin gaba gaɗi (kun dai san halin wasu unethical nursea marasa passion ma aikin su da..... Hmmm ban karasa ba lolz)

""Until that faithful day that u came a ranar dama nayi niyyar fitar da yarinyar nan ko ma mai zai faru ya dade bai faru ba domin na ga dr is not ready to help this innocent girl kawai shi dai tsoron sa family din sa""

"Kin san me??"
Ta min wannan tambayar na girgiza mata kai na in total shock of labarin da naji

   Ta ce min a lokacin da kika shigo sai da Anthony wato wannan gateman din da ya tsare ki da tambaya
Na yi nodding kai na
  Ta cigaba
"Ya kira ni ya gaya min cewa wata matashiyar yarinyan ta zo wurin patient din da dr Ladan ya kawo kuma shi yayi yayi akan ta wuce amma samm taƙi gashi shi yana tsoron barin ki ki shigo ƙilla kin zo yin harming patient din ne

  Na yi murmushi na ce mai ya ce kin nuna mishi ID din ki yace min eh sai na ce ya bar ki ki shigo shine ya bar ki kika shigo din nan

   "Tana kaiwa nan ta dago kan ta ta kalle ni ta ce toh kin ji iya abin da na sani akan wannan patient nawa mai suna Aisha murad Abdulsalaam""

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now